Bankin masana’antu, BOI ya bai wa kungiyar matsakaitan masu masana’antu ta kasa NASSI, bashin Naira biliyan 75.
Ya bai wa kungiyar bashi ne, domin ta tallafa wa ‘ya’yan kungiyar a kan sana’oinsu da suke gudanarwa.
- Sarki Sanusi II Zai Naɗa Babban Ɗansa A Matsayin Ciroman Kano
- An Watsa Shirin Bidiyo Zagaye Na 3 Mai Taken “Bayanan Magabata Da Xi Jinping Yake So” A Rasha
An wanzar da rabbata hannun bayar da bashin ne, ta hanyar sanya hannu a tsakanin shugaban kungiyar na kasa Dakta Solomon Daniel Bonfa da kuma manajin darakta na bankin na masana’antu, Dakta Olasupo Olusi.
A jawabinsa a kan shirin Ma’ajiyin kungiyar na kasa Dakta Abubakar Tanko Bala, ya bayyana cewa, an tsari bashi ne, zuwa kashi uku.
A cewarsa, manyan masu gudanar da masana’antu, za su samu bashin Naira biliyan 75, inda kuma kanannan masu matsakaitan sana’oi, suma za su samu irin yawan wannan adadin kudin.
Ya kara da cewa, wadanda ke a kan tsarin kasuwanci na Nano, za su samu bashin Naira biliyan 50.
Bala ya kuma gode wa kokarin da mankin na BOI ke ci gaba da yi, wajen kara tabbatar da wanzar da bayar da bashin.
Ya bayyana cewa, kungiyar na kuma ci gaba da gamgamin fadakar da kai ga masu gudanar da kanannan sana’oi a daukacin fadin kasar nan, musamman a kan yadda za su ci gaba da gudanar da ayyukansu na kasuwanci don su san mahimmancin bashin da aka ba su.
Ya kara da cewa, wannan shirin, ya nuna a zahiri, na jajircewar gwamnatin shugaban kasa mahimmancin Bola Ahmed Tinubu, na yunkurin magance kalubalen da tattalin arzkin Nijeriya ke fuskanta da kuma tallafawa ‘yan kasuwa, don su tsaya a kan kafafunsu.
Ya bukaci ‘ya’yan kungiyar da ke a fadin kasar, da su shiga cikin shirin domin su amafana su kuma bayar da ta su gudunmawar, waen kara habaka tattalin arzkin kasar.
Bala ya bayyana yakininsa na cewa, wadanda suka amfana da bashin, za su yi amfani da shi yadda ya dace da kuma mai do da bashin, musamman domin a ci gaba da gudanar da shirin har zuwa na dogon zango.