Umar A Hunkuyi" />

Kungiyar Masu Sayar Da Kaji Ta Gagarumin Taro Na Kasa A Kaduna

A ranar Talata ce hadaddiyar kungiyar masu siyar da kaji ta kasa ta gudanar da babban taron ta na kasa a garin Kaduna.

Taron, wanda kusan za a iya cewa shi ne irinsa na uku, amma ya kasance taro na farko da ya hada kusan dukkanin ‘ya’yan kungiyar daga jihohin Nijeriya.

Kamar yadda babban Shugaban kungiyar na kasa Alhaji Tajudden Aliyu, ya yi bayani a wajen taron, a wannan karon an gudanar da taron ne domin kara dankon zumunta da kuma hada kan ‘ya’yan kungiyar yadda ya kamata, ta yadda a kowane lokaci za su rika yin Magana da murya guda kamar sauran takwarorin su watau kungiyoyin masu sauran sana’o’i.

Alhaji Tajudeen, ya kuma bayyana dalilin zabar Kaduna a matsayin wajen da kungiyar za ta gabatar da wannan babban taron nata da cewa; sun zabi Kaduna ce a bisa kasancewar Kaduna cibiya a kasar nan. sannan kuma har ila yau sun zabi zuwa garin na Kaduna ne a bisa irin jajircewar da shugabannin kungiyar da ke Jihar Kaduna su ka yi na ganin bunkasar kungiyar tasu.

Alhaji Tajudeen Aliyu, wanda ya bayyana cewa shi mutumin Ilorin ne, kuma daga can Ilorin din ne ya zo domin halartar taron, ya bayyana matukar farin cikin sa a kan yadda ya ga ‘ya’yan kungiyar sun halarto taron kusan daga dukkanin sassa da kuma Jihohin kasar nan, wanda a cewar sa, wannan babban abin farin ciki ne da kuma jin dadi ganin yadda a yau masu siyar da kaji sun dinke a matsayin ‘yan’uwan juna masu sha’awar yin tafiya a tare.

Ya kuma bayyana cewa daman kokarin hada kan masu siyar da Kaji na kasa shi ne babban manufar kafa kungiyar wanda kuma ya ce a bisa ga dukkanin alamu sun sami nasarar hakan kamar yadda taron na su ya nuna.

Ya kuma bayyana cewa, duk da cewa har ya zuwa yanzun kungiyar ta su ba ta taba samun wani taimako daga gwamnati ba, amma ya yi tilawar yadda a can baya a shekarar 2006 wata kungiya mai kama da wannan ta so kafuwa, amma rashin samun wani tallafi daga wajen gwamnati musamman a lokacin da aka sami wata annoba ta ciwon Kajin ya sanya hakan bai yi nasara ba, wanda a dalilin hakan ma yawancin masu siyar da Kaji suka yi asarar da har ya zuwa yau din nan ba su farfado ba. “A wancan lokacin masu kiwon Kajin ne kadai aka tallafawa ta hanyar biyansu diyyar asarar da suka yi. Amma mu masu siyar da Kaji wadanda a lokacin da zaran mai kiwon Kaji ya hangi alamar cutar a gonar Kajin sa, sai ka ga ya zo ya kira mu da sunan zai siyar ma na da Kaji, wanda mu ba mu san da wata cuta a tare da Kajin nan na shi ba, mun dauka tsakani da Allah ne yake son ya siyar mana da Kajin kamar yadda aka saba. Sai bayan mun je mun saye Kajin na shi ne mun kawo su wajenmu, sai cutar ta bayyana wanda a karshe mu yi asarar dukkanin Kajin nan, Jarinmu ya tafi kuma babu mai taimaka mana. Amma a yanzun da kafuwar wannan kungiya tamu, muna sa ran hakan ba zai sake faruwa ba domin mu ma za mu iya yin Magana da murya guda kowa ya ji.

Shi ma Shugaban kungiyar na babban birnin tarayya Abuja, Alhaji Danladi Hashimu, wanda kuma shi ne Ma’ajin kungiyar na kasa, ya nuna matukar godiyarsa ga Allah Ta’ala ne a kan yadda ya ga ‘ya’yan kungiyar sun halarto taron daga dukkanin sassan kasar nan, da kuma yadda ya ga suna mu’amala da junan su a matsayin ‘yan’uwan juna ba tare da nuna wani bambanci na kabilanci, Addini ko bangaranci ba. Sannan ya nuna farin cikinsa da a kan yadda masu masaukin baki, watau shugabannin kungiyar na Kaduna suka shirya taron tare kuma da irin hidima da tarban da suka yi wa dukkanin ‘ya’yan kungiyar na kasa, wanda a cewarsa, “Ba mu taba ganin inda aka yi mana irin wannan tarban ba. mun gode, mun gode Allah Ya bar zumunci,” a cewar Danladi Hasimu.

Alhaji Yakubu mai Kaji Sabon Garin Zariya, wanda shi ne shugaban kungiyar na Zariya, a shawarar da ya bayar cikin jawabinsa, ya nemi shugabannin kungiyar ne da su ci gaba da jajircewa a kan aikin su, sannan ya nemi da ilahirin ‘ya’yan kungiyar da su guji yin zargin junansu, su kuma rika kyautata wa shugabanninsu zato. Ya kuma yaba da salon da shugabannin kungiyar na kasa suke tafiyar da lamurran kungiyar a bisa hadin kai da tuntubar juna. Shi kuwa mataimakinsa, Alhaji Bala Usman mai Kaji, nuna jin dadinsa ne ya yi da yadda a yau sana’ar sayar da Kaji ta habaka har ta sami mukami sabanin yadda ake ma kyamatar mai siyar da Kaji din a can baya. Sannan ya yi kira musamman ga matasa masu tasowa a sana’ar ta siyar da Kaji da su yi kokari su hada kansu, su kuma kasance tare da wannan kungiyar a duk inda suke.

Ita kuwa shugabar shirye-shirye na kungiyar, Okeduwon Odukwe, wacce ta fito daga Jihar Ogun, ta bayyana fatan ta ne na ganin ‘ya’yan kungiyar sun ci albarkacin kungiyar na su, sabanin abin da ya faru a can baya, inda wasu suka rika cin moriyar wata kungiya da sunan masu siyar da Kaji alhalin su na bogi ne.

Shi kuwa mai masaukin baki, watau shugaban kungiyar na Jihar Kaduna, wanda kuma har ila yau shi ne mataimakin shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Husaini Adamu Yakun, ya bayyana matukar jin dadinsa ne a bisa samun nasarar taron da kuma yadda ya ga wakilan kungiyar da suka sami halartar taron suna ta farin ciki da junan su, wanda ya ce daman hakan shi ne babban makasudin shirya taron domin ganin an samu yaukakar zumunta da hadin kai a tsakanin dukkanin masu siyar da Kaji a cikin kasar nan.

“Wannan kungiya an kafa ta ne domin taimakon kai da kai, da tsarkake sana’ar daga batagari.” Ya kuma bayyana cewa wannan shi ne taro na farko na shugabannin kungiyar da aka gudanar da shi tun bayan kafuwarta watanni hudu da suka gabata. Ya kuma bayyana cewa taron na su ya sami halartar wakilan kungiyar daga Jihohi 25 na kasar nan. sannan sai ya yi kira ga gwamnatoci a dukkanin matakai da su tallafi kungiyar na su, wacce ya ce wakilan kungiyar suna da dimbin yawa a kowane sashe na kasar nan. ya nemi gwamnatin da ta taimaka masu ta yadda za su zamanantar da sana’ar na su. Sannan ya nemi da idan har gwamnati ta tashi taimaka masu da ta tabbatar da ahalin abin ne aka taimaka ma su, ba wadanda za su ci da gumin wasu ba.

A karshe ya yi fatan Allah Ya mayar da kowa gida lafiya.

Exit mobile version