Babban Malami mai wa’azi na kungiyar, Nasrullah -il fatih (NASFAT), Imam Abdul-Azeez Onike, ya shawarci shugabannin siyasa da na Addini da su guji yin kalaman kiyayya, a maimakon hakan, su rungumi junansu.
Onike ya bayar da wannan shawarar ce cikin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na kasa ya yi da shi ranar Juma’a a Legas, a dab da bukin ranar yin hakuri da juna da samar da zaman lafiya ta 16 ga watan Nuwamba.
Tun a shekarar 2018 ne wani shahararren malami, Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan, da ke kasar hadaddiyar Daular Larabawa, ya kaddamar da wannan ranar.
Ranar Duniyar ta nuna hakuri da juna wacce UNESCO ta shelanta gabatarwa a duk shekara tun daga shekarar 1995 domin wayar da kan al’ummu a kan hadarin da ke tattare da rashin hakuri da juna. Ana gabatar da ita ne a duk ranar 16 ga watan Nuwamba, na kowace shekara.
Taken ranar shi ne: “Prospering from Pluralism: Embracing Dibersity through Innobation and Collaboration.”
A cewar Onike, rashin hakuri da yin kalaman batunci ba za su amfanar da komai ba, sai dai ma su yi hannun riga da koyarwar Addini.
Ya kuma bukaci mabiya manyan Addinan kasar nan biyu da su kasance masu neman wata mafitar da kuma fahimta mai kyau a duk lokacin da suka yi karo da wani malamin da yake yin wa’azin haifar da rashin hakuri da rashin zaman lafiya.
Onike ya ce, manufar Addinin Musulunci shi ne daukaka abin da zai amfani al’umma da kawar da abin da zai cutar da al’umma.
Ya ce an gina Shari’ar Musulunci ne a kan basira da jin dadin bayin Allah a cikin rayuwar su da kuma bayan mutuwar su.
“Baki-dayan Shari’a adalci ne, tausayi, amfanarwa da kuma basira.
“Duk wani abin da ya saba wa adalci ya zama zalunci, ya saba wa tausayi ya zama mugunta, ya saba wa amfanarwa ya zama barna, ko ya saba wa basira ya zama wawici, sam wannan abin ba a cikin Shari’a ne yake ba, ko da kuwa an yi kokarin shigar da shi ta hanyar tawili.
Ya bukaci ‘yan Nijeriya da su rika tuna sakon da ke cikin ranar ta 16 ga watan na Nuwamba.
An kebe wannan ranar ce domin kara fahimtar juna da girmama juna a tsakankanin al’umma mabambanta fahimta.
“Akwai bukatar yin hakuri da juna a kowane fanni na rayuwa, saboda hakan yana taka mahimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya, kauna da soyayya a cikin al’umma.
“Ya kamata a gane a sarari cewa, girmama juna da yin hakuri da juna ba yana nufin na bar fahimta ta ne ba na komo naka,” in ji shi.