‘Yan kungiyar Zabarmawan Nijeriya a karkashin jagorancin Sarkin Zabarmawan Nijeriya, Alhaji Ibrahim Mahmud Tsamiya, sun nesanta kansu daga shugabancin wani mutum mai suna Alhaji Aliyu Abubakar wanda Mai Martaba Sarkin Sasha Alhaji Haruna Mai Yasin, Sardaunan Yamma ya nada a fadarsa dake Ibadan a ranar 9 ga watan Yulin 2023.
kungiyar ta ce sam ba su amince ba da wannan nadin. Domin ba za su amince da shugabancin wanda ba Zabarmawa ne suka amince da shi ba. A don haka sun ce nadin da aka yi wa Alhaji Aliyu Abubakar ba su san da shi ba, kuma shugabansu a Nijeriya shi ne Alhaji Ibrahim Mahmud Tsamiya kuma gare shi suka yi mubaya’arsu.
Zabarmawan na Nijeriya sun bayyana hakan ne a taron da suka kira a ranar Asabar 15 ga watan nan da ake ciki a Fadar Sarkin Zabarmawan Ikeja da ke Shodipe Agege domin tattaunawa a kan nadin Sarkin Zabarmawa na jihohin kudu goma sha bakwai da Sarkin Sasa ya nada kuma suke nesanta kansu ga shi.
Zabarmawan sun nuna rashin amincewarsu a kan wannan nadin, inda suka tabbatar da cewa ba za su bari wasu su raba kawukansu ba.
Dakta Lawal Sani Kasgada, Sakataren kasa na kungiyar Zabarmawa zallah ta Nijeriya ya ce sun kira taron ne domin jaddada mubaya’arsu ga jagorancinsa na Sarkin Zabarmawan Nijeriya; “Wadanda Zabarmawa zallah suka zaba ya shugabance su a matsayin Sarkin Zabarmawan Nijeriya. Duk Zabarmawan da ke Nijeriya suna mubaya’a ga shi. A bayan haka kuma muna kara nesantar da kanmu a kan duk wani Basarake da za a ce a nan Kudu wani Bahaushe ya nada. Duk Basarake ko Bazarmane Bahaushe ya nada da sunan Zabarmawa mu ba za mu aminta ba, ba ma tare da shi”, ya jaddada.
Lawal ya ci gaba da cewa Zabarmawa yare ne masu ‘yanci, inda ya ce; “a don haka Bazamarme ne zai nada mana Bazamarme. Duk wani wanda yake son sarauta a jihohin Kudu, to ya zo fadar mai girma Sarkin Zabarmawan Nijeriya a nada shi. Idan kuma ya bar wannan ya je wurin wani Sarki wanda ba Bazamarme ba, wannan yanayi ne a karon kansa. Duk wani wanda ya yi hulda da shi a matsayin Basaraken Zabarmawa da ke kudu, to ya yi wannan ne a gaban kansa.
Zabarmawa ba su da alaka da wannan, ba su da alaka da shi. Kuma ba su amince da shi ba, a don haka mubaya’armu yana ga Sarkin Zabarmawan Nijeriya da duk kuma wanda shi ya nada idan dai a Kudancin Nijeriya ne; wato jihohi goma sha bakwai na jihohin Nijeriya.
“Kuma wannan maganar da nake yi ina yin shi ne a madadin dukkanin Zabarmawan da ke Nijeriya da Sarakunan kudun Zabarmawa wadanda ke Nijeriya tun daga Fatakwal da ke jihar Ribas har zuwa Legas, Ogun, Osun, Imo, Ondo, Kuros Ribas, Bayelsa, duk dai jihohin nan guda goma sha bakwai”, ya nusasshe.
Ya yi kira ga Zabarmawan Nijeriya da su wanzar da zaman lafiya. Kuma ka da su dauki doka a hannu, inda ya aara da cewa; “A don haka kuma bayan haka muna kira ga Zabarmawa da su zauna lafiya, duk Zabarmawa daya ne. A hada kai, ka da a dauki doka a hannu. Zaman lafiya shi ne abu ingantacce. Abin da zaman lafiya bai kawo ba, tashin hankali ba zai kawo shi ba.
Musamman wannan kasa ta mu da take cikin rigingimun barazanar tsaro. Mu ba hukumomin tsaro damar su, mu ba su goyon baya. Ka da kowa ya dauki doka a hannunsa. Bazamarme dan uwan Bazamarme ne. Bazamarme dan uwan Nijeriya ne gaba daya a matsayinmu na al’umma daya, kasa daya, wanda aka raba ba”.
Alhaji Yahaya, dan majalisar Sarkin Zabarmawan Ikorodu, ya nemi a zauna lafiya tare da yin biyyaya ga masarautar Zabarmawa da aka sani, wato karkashin jagorancin Sarkin Zabarmawan Nijeriya wato Alhaji Ibrahim Tsamiya. Taron ya samu halartar dimbin jama’a da suka hada da Sarakunan gargajiya, ‘yan kasuwa da matasa.