Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce wasu kungiyoyin kasa da kasa ne ke daukar nauyin ayyukan Boko Haram a kasar nan.
Buhari ya yi wannan jawabi ne a lokacin wata liyafar cin abincin shugaban kasa da gwamnatin Jihar Kano ta shirya masa yayin ziyarar aiki ta yini daya.
- Shugaban NIS Ya Sake Gargadin Marasa Gaskiya A Kan Harkokin Fasfo
- Sin Na Fatan Amurka Za Ta Shawo Kan Amfani Da Karfin Tuwo Da Jami’an Tsaro Ke Yi Kan Fararen Hula
“Lokacin da muka hau mulki a shekarar 2015, Boko Haram sun mamaye kananan hukumomi 13 cikin 17 na Jihar Borno, hudu ne kawai ke hannun gwamnati a lokacin.
“Sun zo ne domin hana mu ci gaba.
“Amma mun yi nasarar nunawa ‘yan Nijeriya da sauran kasashen duniya cewa muna da albarkatun kasa da yawa a yankin tafkin Chadi,” in ji shi.
“Dole ne mu dage da addu’a kuma mu gode wa Allah, za mu yi yakin kwato kasarmu daga kungiyoyin kasa da kasa da ke kokarin ruguza Nijeriya.
“Mun yi sa’a sosai cewa wannan gwamnati ta yi abin da ya dace karkashin Gwamna Zulum na Jihar Borno, wanda ya yi matukar aiki.
“Na yi matukar farin ciki da ‘yan Nijeriya suka nuna min goyon baya. Sun gane cewar ina tare da su.
“Ina so ku tuna cewa tsakanin shekarar 1999 zuwa 2019, NNPC tana hako ganga biliyan 2.1 a rana a kan farashin dala 100 kan kowacce ganga.”
A cewarsa Nijeriya tana samun dala 100 kan kowace ganga kuma tana hako ganga miliyan 2.1 a kowace rana.
“Farashin man fetur a yau ya ragu da kusan dala 37 a kowace ganga wanda ake samar da ganga miliyan 1.5 kacal amma duk da haka mun samar da ababen more rayuwa da dama.”
“Na yi gwamna, na yi minista kuma na kasance Shugaban kasa, na yi yakin basasa.
“Dole ne mu gode wa Allah da abin da muke da shi a kasar nan a yau,” in ji shugaba Buhari.
Tun da farko Gwamna Abdullahi Ganduje ya yaba wa shugaba Buhari bisa yadda yake martaba Jihar Kano.