Kwamishinan Lafiya A Jihar Yobe Ya Tabbatar Da Rahoton Mutane 10 Sun Kamu Da Cutar Sankarau

Kwamishinan ma’aikatar lafiya a Jihar Yobe Alh Bello Kawuwa ya tabbatar da cewar an samu mutane 10 da ke dauke da cutar nan ta sankarau a cikin Jihar kuma, 3 daga cikinsu tunin sun riga mu gidan gaskiya.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne a ya yin da ya ke kaddamar gangamin allurar rigakafin cututtukan nan na kyanda da sankarau dake yaduwa a cikin al’umma musamman a lokacin zafi da aka gudanar a garin Damaturu.

Ya kara da cewar, gwamnatin Jihar da hadin gwiwar hukumar samr da harkokin kiwon lafiza a matakin farko ta kasa (PHC).

Kwamishinan ya ci gaba da cewar, wannan rigaki da ake kokarin akai za a gudanar da shi ne a cibiyoyin kiwon lafiyar da aka tanada, ana kuma kyautata zaton za a yiwa yara kimanin 771,778 rigakafin.

Ya kara da cewar wannan aiki na rigakafin za a gudanar da shi ne bangare biyu na farko tunin aka fara gudanar da shi daga ranar 7 ga watan nan na Fabararu 2018 aka kare shi a ranar lahdi 11 ga wata a kananan hukumomi 8 sai kashi na biyu a gudanar da shi daga ranar 14 ga watan na Fabarairu zuwa 18 ga watan.

Don haka ne kwamishinan ya nemi iyaye da su bada ‘ya’yansu don yi musu wannan rigakafi,

don hakkin mu ne mu iyaye da muga mun samarwa da yaran mu yanayin lafiya mai nagarta.

 

Exit mobile version