Gabanin bikin rantsar da zababben shugaban kasar Nijeriya, Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu, babbar hukumar Birtaniya a Abuja ta bayar da jadawalin wata tawaga da za ta halarci bikin.
Shugaban sashen yada labarai na hukumar kolin Birtaniya da ke Abuja, Dean Hurlock ne ya bayyana hakan a ranar Laraba.
- Mun Yi Iya Kokarinmu Wajen Shugabancin Nijeriya —Buhari
- LEADERSHIP Da CMG Sun Karfafa Dangantakar Aiki A Tsakaninsu
Ya ce, “Tawagar ta Birtaniya za ta kasance karkashin jagorancin Firaminista Andrew Mitchell MP, Karamin Ministan Ci Gaban Afirka a Ofishin Harkokin Waje, tare da Wakilin Fira Ministan Harkokin Kasuwanci a Nijeriya sa kuma Wakili na Musamman kan Ilimin ‘Yara Mata, Helen Grant (OBE, MP) da Babban Kwamishinan Birtaniya a Nijeriya, Dokta Richard Montgomery, CMG.”
A halin da ake ciki kuma, haifaffen Nijeriya Enoh Ebong na cikin tawagar Amurka da za ta halarci bikin rantsar da zababben shugaban kasa Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.
Ebong na cikin tawagar wakilai tara da shugaban Amurka Joe Biden ya sanar a ranar Litinin.
Wata sanarwa da ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja ya fitar a ranar Talata, ta ce tawagar za ta kasance karkashin Sakatariyar Gidaje da Raya Birane ta Amurka, Marcia L. Fudge.
Sauran mambobin tawagar Amurka zuwa Nijeriya sun hada da: David Greene, mai kula da ofishin jakadancin Amurka a Abuja; Sydney Kamlager-Dove.
Wakili daga California; Marisa Lago, ma’aikatar kasuwanci ta Amurka, ma’aikatar kasuwanci ta kasa da kasa, da kuma Michael E. Langley, kwamandan rundunar Amurka a Afrika.
Sauran sun hada da Mary Catherine Phee, Mataimakiyar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka kan Harkokin Afirka; Judd Devermont, mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin tsaro na kasa kuma babban darakta mai kula da harkokin Afirka, da Monde Muyangwa, mataimakiyar mai kula da harkokin Afirka a hukumar raya kasashe ta Amurka (USAID).
Kwanan nan Ebong ta jagoranci tawagar binciken Amurka zuwa Nkjeriya da Ruwanda domin inganta harkokin kasuwanci da zuba jari a kasashen.
Enoh Ebong, wadda ita ce mataimakin daraktar hukumar kasuwanci da raya kasa ta Amurka, ta samu rakiyar sakatariyar kasuwanci ta Amurka, Penny Pritzker, da mambobin kwamitin ba da shawara na shugaban kasa kan harkokin kasuwanci a Afirka.
Da yake tsokaci kan aikin, Ebong ta ce an tsara aikin ne domin musayar bayanai da kuma gano damammaki na inganta huldar kasuwanci tsakanin Amurka da Afirka.
Ta ce, “An nemi na shiga cikin wannan tafiya a matsayina na mataimakiyar daraktan ciniki na Amurka da
Hukumar Raya Kasa, wacce ke hada kai da kamfanonin Amurka don tsara hanyoyin magance kalubalen ci gaba a Nijeriya, Rwanda da ma duniya baki daya.
“Muhimmin abu ne na abin da muke yi. A cikin muhimman matakai na farko na ci gaban aikin samar da ababen more rayuwa, muna gina hadin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki na Afirka da kamfanonin Amurka wadanda ke gano abubuwan da suka dace don tabbatuwar aikin.”
Ta bayyana cewa, a lokacin da ta fara zuwa USTDA, a kwanan baya gwamnatin Nijeriya ta fara bude bangaren sadarwa.
Tun daga wannan lokacin, ta ce Amurka na hada kamfanonin sadarwa na Nijeriya da kwararrun Amurka wadanda za su taimaka musu wajen sabunta ababen more rayuwa.
“A halin yanzu muna taimaka wa Kamfanin Main One Cable na Nijeriya don shirin tsawaita hanyar sadarwa ta ‘fiber optic’ karkashin teku mai nisan mil 300 daga Legas zuwa Fatakwal, ta hanyar aikinsu tare da wani kamfani na Amurka, HIP Consult, Inc. (Washington, DC).
Aikin zai kara yawan mutane da kasuwancin da ke da damar yin amfani da sadarwa a duk yankin.
“Saboda wannan samfurin ya tabbatar da nasara sosai, muna amfani da shi ne don taimaka wa abokan huldar mu na Nijeriya su bunkasa bangaren wutar lantarkinsu. Muna aiki don kawo makamashi ga karin ‘yan Nijeriya. Misali daya shi ne, USTDA tana kimanta karfin fasaha da kudi na gina tashar wutar lantarki mai karfin megawatt 275.”
A cewarta, aikin zai kara karfi da kuma inganta samar da wutar lantarki ga abokan huldar zama da na kasuwanci a fadin Jihar Legas.”
“Wannan yunkurin babban misali ne na yadda Amurka da Afirka ke aiki tare don kara samar da wutar lantarki a karkashin shirin Shugaba Obama na ‘Power Africa’.
“Ta hanyar hada kai a kan ayyuka irin wannan, muna taimakawa wajen tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya da yawa sun samu damar samun makamashi. Kuma muna taimakawa wajen karfafa dangantakar tattalin arziki tsakanin Nijeriya da Amurka,” in ji ta.
Da ta ke magana a kan asalinta l, Ebong ta ce, “A matsayina na ’yar Nijeriya kuma ’yar kasar Amurka mai alfahari, na fara ganin yadda abubuwan da mahaifina ya yi a baya suka tsara rayuwata. Yunkurinsa na ci gaban Nijeriya ya sa na shiga cikin kokarin gwamnatin Amurka na bunkasa ci gaba ta hanyar amfani da kwarewa da albarkatun kamfanoni masu zaman kansu na Amurka.
“Ina matukar godiya da wannan damar na komawa kasar da aka haife ni da kuma shiga cikin masu ruwa da tsaki na Amurka da na Afirka wajen musayar ra’ayoyi don karfafa hadin gwiwarmu. Na san mahaifina zai yarda cewa, ta hanyar karfafa dangantakar kasuwanci da ci gaba a yau, muna taimakawa wajen tabbatar da kwanciyar hankali da wadata a gobe.”
A halin da ake ciki kuma, bayan bin sahun kasashen Amurka da Birtaniya, a jiya, kasar Kanada ta bayyana ta hannun babbar hukumarta cewa kasar za ta wakilci kasar a wajen bikin rantsar da Tinubu.
A nata bangaren, babbar hukumar Indiya da ke Abuja ta shaida wa wakilinmu a Abuja a jiya cewa, kasar za ta samu wakilcin tawaga.
Jami’in yada labarai na tawagar, Vipul Mesariya, ya shaida wa LEADERSHIP cewa, Delhi na iya tura wata tawaga karkashin jagorancin minista.
Hukumomin kasar Sin da ke ofishin jakadanci da ke Abuja sun kuma tabbatar da cewa, akwai yiyuwar wata tawagar gwamnatin kasar Sin za ta halarci taron, domin nuna goyon baya ga Nijeriya, da karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Jami’in kula da harkokin siyasa da yada labarai, Gu Jing, ya shaida wa wakilinmu cewa, tabbas kasar za ta aiko da wakili, amma har yanzu babu tabbas.
Wata majiya daga Saliyo ta shaida wa wakilinmu a jiya cewa, akwai yiwuwar shugaban kasar Julius Mada Bio, ya jagoranci wata tawaga zuwa rantsar da Tinubu.
Ofishin jakadancin Turkiyya ya kuma shaida wa LEADERSHIP cewa har yanzu ana kan hada tawagar da za a aiko Nijeriya.
Wata majiya a ofishin jakadancin da ba ta bayyana sunanta ba, ta ce mai yiwuwa a sanar da tawagar kafin karshen mako.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
Ya doke abokan hamayyarsa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar LP, inda ya lashe kujerar da Nijeriya mafi girma.
Sai dai kuma, Atiku da Peter Obi ne ke kalubalantar nasarar da Tinubu ya samu a kotun sauraren kararrakin zabe, inda suka yi zargin cewa hukumar zaben ta yi magudin zabe ne domin fifita tsohon gwamnan ja Jihar Legas.
Har ila yau, sun yi zargin cewa Tinubu na da alaka da harkar safarar miyagun kwayoyi a Amurka.