Connect with us

LABARAI

Kyawawan al’adun Sallah Suka Sa Kano Ke Karbar Baki Daga Kasashen –‘Yandakan Karaye

Published

on

Ibrahim Mu’azu ‘Yandakan Karaye shi ne babban Saktaren Hukumar Raya al’adu da adana tarihi ta jihar Kano, Hukumar da ke sahun gaba wajen shirya bukukuwan al’adu wanda suka hada da kade-kade da raye-raye da kuma adana kayan tarihi, ‘Yandakan na Karaye ya bayyana irin rawar da Hukumar ke taka wa a lokutan bukukuwan Sallah da ma sauran tarukan da ake baje kolin al’adu iri daban-daban.  A tattaunawarsa da wakilinmu na Kano ABDULLAHI MUHAMMAD SHEKA, ALHAJI IBRAHIM KARAYE ya bayanna yadda

Gwamna Ganduje ke tayar da komadar gidan adana kayan tarihi da kuma raya al’adunmu. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance.

Ko za ka gabatarwa da mai karatu kanka?

Sunana Ibrahim Mu’azu ‘Yandakan Karaye, kuma ni ne babban sakatare mai kula da wannan Gida na adana tarihi da raya al’adun garagajiya na jihar Kano.

 

Shin ko ya ka samu wannan Hukuma zuwanka a matsayin babban Sakatare?

Kamar yadda aka sani an kafa wannan Hukuma a ckin shekara ta 1973 a matsayin hukumar al’adu wanda kuma aka sake sabunta ta wadda gwamnatin Mulkin soja ta yi a shekara ta 1987, inda ta zama hukuma raya al’adu, adana tarihi da kuma fadada harkokin bincike mallakin jihar Kano, akwai gidan kayan tarihi na Gwamnatin tarayya Gidan Makama. Ayyukan hukumar ya hadar da bangaren adana hotunan mashahuran mutane tun tsawon wani zamani, wannan kuma sun hada da Malamai da attajirai da sarakuna.

Sai kuma wani sashi da ke karkashin wannan Hukuma wanda shi kuma

amfaninsa  shi ne adana kayan tarihin da suka shafi rubuce rubuce, wannan kuma ya hada da dakunan Karatu, akwai litattafan da aka bai wa jihar Kano kyauta da kuma litattafan da muka gada iyaye da kakanni, inda za ka samu cikakkun bayanan Turawa kan kowacce gunduma irinsu kasar Rano wanda a lokacin Dawakin Kudu ke karkashinta, wadannan da sauransu na cikin irin tagomashin da wanna Hukumar ta samu tun lokacin da aka kafa Hukumar, akwai batun kade-kade da raye-raye da saura fannonin dishadantarwa duk suna karkashin kulawar wannan Hukuma.  Sannan daga cikin ayyukan wannan Hukuma akwai hada kai da kowacce Hukuma domin gudanar da wani shiri ko aikin wayar da kai da fadakarwa. Saboda haka a wannan Hukuma yanzu haka muna da cikakkun bayanai kan abubuwa da suka shafi jihar Kano da ma Arewacin Nijeriya.

 

Kasancewar yadda ake gudanar da bukukuwan sallah a Kano,  Masarautar Kano ne ke zama wurin kashe kwarkatar ido musamman ga bakinmu daga kasashen waje, wane tanaji wannan hukuma ke yi na bikin Sallar?

Ina tabbatarwa da Jama’a cewa, ba wai wannan Hukuma ba Gwamnatin Kano takan dauki wannan biki da muhimmacin gaske sai dai kawai mu kara yiwa Gwamna Ganduje godiya, domin tabbatar da nasarar wannan biki Gwamna Ganduje tuni kan kafa  kwamiti mai karfin gaske wanda za a dora wa alhakin gudanar da shirye-shirye da kuma tsare-tsaren da aka tabbatar zai haifar da kyakkyawar nasara .

Cikin abubuwan da aka saba gudanarwa akwai haye-haye da kuma sauran al’adun gargajiya, wanda suka hada da raye-raye  da langa da Kokawa da dambe, shadi da sauransu, dukkansu wannan kwamiti na nan na dubu yadda za a inganta su tare da hadin gwiwa da wasu kungiyoyi masu kishin ci gaban al’adunmu, saboda haka muke bai wa ire-iren wadanan kungiyoyi dama domin suma su nuna irin tasu kwarewar, yanzu haka akwai wata kungiya mai suna KUCHKA wadda kungiya ce da ta yi shura wajen gudanar da abubuwan raya al’adu, yanzu haka sun nemi amincewarmu domin gudanar da wasan langa, wanda kuma ga duk wanda ke son bayar da irin wannan gudummawa sai an nemi izinin wannan Hukuma. Yanzu haka Masarautar Kano ta sanar da wannan Hukuma domin duba yadda za a gudanar da wannan wasan Langa.

 

Wadanne kalubale  wanann Hukuma ke fuskanta?

Gaskiya  ne shi duk abin  a ka sani musamman wanda ake gudanar da shi aduk shekara dole a samu wasu kalubale wanda a lokuta da dama sai an runtse ido domin shawo kan wani kalubalen, amma dai mu a wannan Hukuma muna kara yi wa Allah godiya tare da jinjinawa Gwamna Ganduje saboda irin gudummawa da yake bai wa wannan Hukuma.

Abin da ya sa muke kara kaimi wajen tabbatar da ganin cewa al’amarin harkokin raya al’adu domin kowa ya san kasuwar man fetur gaf take da zuwa karshe, don haka dole abubuwan da ake ganin za su maye gurbinsa wajen samarwa jihohi kudaden shiga su ne ire-iren wadannan al’adun namu na gargajiya, wanda idan aka inganta ta su, ko shakka babu za su ci gaba da zama wuraren yawon bude ido ga baki daga kasashen waje, hakan zai haifar da samun karin masu sha’awar zuba jari a cikin kasarmu.

 

A kwankin baya an ji wannan Hukuma a wata makwabciyar kasar nan Nijar inda kuka je domin gudanar da wasu abubuwa, shin ko me aka je yi a Nijar?

Gaskiya ne mun je har shelkwatar kasar Nijar Niyame bisa gayyata da wata kungiyar al’adun gargajiya  ta yiwa mai Giram Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje domin karrama shi, Allah bai sa ya samu zuwa ba saboda wasu ayyukan da suka sha gabansa,  don haka ya tura mu a matsayin wakilansa muka tafi da yaranmu masu raye-rayen gargajiya suka je kuma suka taka rawar gani abubawa na bajinta wanda suka kawata.

 

Zuwa yanzu da Gwamnatin Ganduje ta cika shekara uku da doriya, ko me za ku iya bugun kirji da shi wanda Gwamnatin Ganduje ta yi wa Hukumar raya al’adu?

Abubawan da Gwamna Ganduje ya yi wa wannan Hukuma suna da yawa amma dai ko daga yadda ka kalli cikin ofis din nan za ka aminta da cewa mun yi dacen Gwamna, domin ada idan ka shigo wannan ofsi din sai ka rantse teburin sarkin fawa ne, amma yanzu dubi yadda aka sake fasalin ofishin, dubi sashin wannan Hukuma dake kan titin Saikkwato Rd. dubi cikin gidan Dan Hausa yadda aka sake fasalinsa, kuma ana ma kan aikin ne a halin yanzu.

Bayan haka kuma yanzu Gwamna ya amince da gina katafaren dakin gudanar da bukukuwa irin na zamani wanda za’a gina acikin wannan Hukuma, haka duk wuraren da aka saba gayyatar wannan hukuma musamman wuraren tarukan al’adu irin Canibal, NAFEST, APAC duk Gwamna Ganduje na bamu

cikakken goyon baya domin halarta, muna zuwa kuma muna samun gagarumar Nasara, akwai lokacin da ba’a bamu kudaden tafiya ba, amma mu kaje kuma mu kazo na uku a fadin Najeriya, wannan ya baiwa Gwamna mamaki kwarai da gaske. Ma’akatan gidan nan suna da jajircewa kwarai da gaske ba don kudin suke aikin ba kishin cigaban al’adun ne a gabansu.

 

Mene sakonka na karshe?

Alhamdulillahi da farko dai dole mu kara gode wa Gwamna bisa irin gudunmawar da yake bai wa wannan Hukuma ta raya al’adu, kuma ina kira ga al’ummar Kano cewa ga lokacin zabe na kara gabato wa, saboda haka akwai bukatar Kanawa su kara jajircewa wajen sake zabar Gwamna Ganduje da Shugaban kasa Muhamamdu Buhari

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: