Farfesoshi tagwaye, Hassan Ishaƙ Ibrahim da Hussaini Yusuf Ibrahim tagwaye ne masu kama ɗaya tun daga ƙuruciya har zuwa girman su, sannan rayuwar su ta yi kama da ta juna da abubuwan ban mamaki. Tun daga harkokin karatun su da aikin su da kuma auren su har zuwa matakin karatu suna tafiya da abu iri ɗaya ba tare da rabuwa ba.
Dukkan su Farfesoshi ne a ɓangarorin aikin gona da kuma tattalin arziki da suke aiki a jami’ar gwamnatin tarayya ta FUDMA da ke Jihar Katsina, wakilinmu ya tattauna da su inda suka bayyana labarin rayuwar su daga inda suka fara zuwa inda suke yanzu da kuma irin burin da suke son cimmawa a nan gaba.
Ku gabatar mana da kanku a takaice sannan ku gaya mana yadda kuka tsinci kanku a matsayin tagwaye a layin koyarwa iri ɗaya?
Farfesa Hassan Ishaƙ: Mu dai tagwaye ne masu kama da juna ƴan asalin Jihar Kaduna, dukkan mu Farfesoshi shi ne ɗaya a fannin aikin gona ɗaya a fannin tattalin arziki a jami’ar FUDMA da ke Jihar Katsina. Yadda tafiyar karatun mu ta kasance kusan iri ɗaya shine, mun yi karatu digiri na farko da na biyu tare a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, sannan daga bisani muka yi digiri na biyu a jami’ar Ilorin da ke Jihar Osun. A tsawon shekarun da muka kwashe, mun yi aiki tare a fanni iri ɗaya, ciki harda koyarwa, bincike da gudanar da ayyukan jami’a duk iri ɗaya. Sannan abinda yasa tafiyar mu ta zama ta musamman ba wai a fannin ilimi ba kawai har da yadda muke yin abubuwan rayuwa kusan iri ɗaya a tare kafada da kafada
Farfesa Hussaini Yusuf: Bari in ƙara a kan abinda ɗan uwana ya faɗa, wato rayuwar mu ta kasance a tare tun muna ƙanana, mun tashi tare, mun yi karatu tare, mun yi aure a rana ɗaya, sannan muna da ƴa ƴa yawan su ɗaya, wato mata huɗu namiji ɗaya kowannen mu.
Idan aka koma akan batun karatu kuwa, mun kasance muna tafiya akan turba ɗaya, da suka haɗa da aiki a sashe ɗaya, sannan a rana ɗaya muka fara aiki koyarwa (lecturing) Sannan abinda yasa labarin rayuwar mu ya kasance na musamman shi ne daidaiton da ke akwai a tsakanin rayuwar mu ta ƙashin kai da kuma tafiyar mu ta ilimi, wannan na daga abubuwan birgewa a cikin tarihin rayuwar mu.
Ko zaku iya bayyana irin ayyukan da kuke yi yanzu a jami’a?
Farfesa Hassan Ishaƙ: Yanzu haka ina aiki a matsayin janar manaja kuma kwararai mai bada shawara a jami’ar. Bugu da ƙari akan wannan shine yanzu ina cikin harkokin koyarwa da bincike da kuma ayyuka al’umma wanda ya kasance jigo a ayyukana na koyarwa.
Farfesa Hussaini Yusuf: Ni yanzu ina aiki a matsayin daraktan sashen tabbatar da ingancin ayyuka (Ƙuality Assurance Directorate) na jami’a inda nake aikin tabbatar da ingancin ayyukan ilmi da gudanarwa a faɗin jami’ar. Bayan haka kuma ina gudanar da aikin koyarwa da bincike da sauran ayyukan yau da kullum na wannan jami’a ta FUDMA kuma Ni Farfesa ne.
Bari mu koma baya, akan abinda ya shafi rayuwar ku tun kuna ƙananan a matsayin tagwaye, ta ya ya kuka fahimci cewa kuna da abu na daban a cikin mutane?
Farfesa Hassan Ishaƙ: Wato da farko dai, rayuwa baƙi ɗayan ta tana da sauƙi, muna kallon kanmu kamar kowane ɗa da muka tashi tare, sannan ba mu taɓa sannan ba mu taɓa tunanin muna da wani abu na daban da ya banbanta mu da wasu ba.
Sannan duk dai akan abu ɗaya, mun fara lura da cewa yara suna bin mu duk inda kuma je, sannan suna nuna mu, suna cewa, ga ‘ yan gida ɗaya masu kama da juna ‘ ma’ana dai mutane daga gida ɗaya wanda suke kama ɗaya.To, sai a wannan lokaci muka fara lura cewa mutane suna ganin wani abu tare da mu na daban wanda mu bamu taɓa lura da haka ba.
Daga lokacin da muka shiga makarantar sakandire, daidai lokacin muna a tsakanin shekaru sha biyu, hankalin mu ya fara gaya mana wani abu na daban, sannan muka fara gane cewa mu tagwaye ne. Mun cigaba da lura cewa kasancewar mu tagwaye yana ɗaukar hankali abinda ba mu taɓa kawo a ranmu ba tunda muka ta so
Farfesa Hussaini Yusuf: Gaskiyar magana shine mun taso kamar kowane yaro, mutane ne da muke tare da su, suka fahimtar da mu cewa mu din tagwaye ne. Kamar yadda ɗan uwana ya yi bayani mutane sun cigaba da cewa muna kama da juna, abin birgewa ban taɓa gane haka ba, amma jama’a sun cigaba da nunawa cewa mu ɗin tagwaye ne.
Duk lokacin da muka je wani gari, mutane suna tsayar da mu domin su tabbatar da cewa mu ɗin tagwaye ne, wasu ma cewa suke yi, mu yi masu kyauta saboda mu tagwaye ne. Daga lokaci zuwa lokaci mun fara tabbatar da cewa hankalin al’umma ya karkato akan a matsayin mu na tagwaye.
Ko yau ɗin nan, idan na ga iyaye tare da ƴa ƴan su tagwaye, na kan ji sha’awar sanin su. Sau da yawa na kan tsaya in tambaye su sunayensu da kuma sanin cewa tagwaye ne su. Ban sani ba, ko hakan na faruwa ne saboda ina jin wata alaƙa ta musamman da su kasancewar ni ma tagwaye ne.
Kun taɓa tunanin cewa yanayin rayuwar ku yana ɗaukar hankalin al’umma a kafafen yaɗa labarai?
Farfesa Hassan Ishaƙ: A’a, Ba mu taɓa kawo a ranmu ba cewa muna ɗaukar hankali saboda mu tagwaye ne. Gaskiya ba mu taɓa tunanin cewa mutane za su riƙa gayyatar mu ana tattaunawa da mu kamar haka ba, wannan ita ce hira da mu ta uku, daga cikin mu babu wanda ya taɓa yin shiri akan haka. A shekarun mu na samartaka mun fi san yin rayuwa wanda babu hayaniya.
Sannan kuma duk inda muka je, mutane suna gane mu, a makaranta ɗalibai suna tambaya, wanene Hassan? Wanene Hussaini? Wasu ma suna gardama akan mu idan suka ruɗe. Ba mu taɓa nema mu zama abin ɗaukar hankali ba, amma dai ba za mu iya kaucewa hakan ba, saboda ba mu da ikon da yin haka. Mun yi ƙoƙari so sai wajen yin rayuwa da tsantseni da kaffa-kaffa, amma Allah ta’ala yana da na shi tsarin akan mu.
Me ya yi tasiri a rayuwar ku har kuka yanke shawarar rungumar aikin koyarwa a matsayin sana’arku?
Farfesa Hassan Ishaƙ: Wato sha’awar koyarwa ta fara ne tun ina aji shida a firamare ta Capital da ke Kaduna. Malamina ya kan sani in tsaya bayan an hutun tara, in taimakawa ɗalibai ƴan ajinmu waɗanda ba su fahimci darasin lissafi ba. Saura kuma suna fita su je, su yi wasa, ni kuma in tsaya ina yi masu bayani, wannan ne ya cusa mani san koyarwa tun farko.
Daga baya, ina shekara ta uku a jami’a, an yi wani dogon yajin aikin Malaman jami’a wanda ya kusa kai shekara ɗaya. A daidai wannan lokaci jami’ar Ahmadu Bello Zaria a rufe take, ina gida zaune ba abinda nake yi.
Wata rana sai na ziyarci wata makaranta kusa da mu, na sanar da shugaban makarantar (Head Mastery) cewa ina san ina riƙa koyarwa, inda ta tambaye ni takardun shaida kammala karatu, sai na yi mata bayani da cewa ina aji uku ne a jami’a, amma dai ina shawarar koyarwa. Ta bani damar in koyar, na cigaba da koyarwa har aka gama yajin aikin.
Lokacin da aka bude makarantu, sai kuma ba sa san na tafi, amma dole in tafi domin in kammala karatuna. Ko lokacin da na kammala digiri na ɗaya da biyu na cigaba da koyarwa tunda koyarwa ta riga ta zama wani ɓangare na abinda na ke so, malamin mu na firamare ya riga ya sanya mani san koyarwa.
Ɗan uwanka ne ya rinjaye ka har ka yanke hukuncin rungumar aikin koyarwa?
Farfesa Hussaini Yusuf: Gogewar mu kusan duk ɗaya ce, kafin mu je jami’a na fara koyawa ƴan uwana karatun littafi, daga baya kuma ba ga ya kamata in nemi aikin da na sani ina da muradi.
Ilmin larabci da nake da shi ya taimaka wajen fahimtar yadda ake samar da sautuka da harufa ta hanyar wasula da baƙaƙe, sannan na yi amfani da wannan ilmi wajen koyar da karatun turanci. Haka kuma tun ina makaranta na lura cewa zan iya koyar da karatu cikin sauki fiye da wasu malaman mu, wani lokaci na kan yi tunanin yadda zan koyar da darussa idan na samu kaina a malamin jami’a
Waɗannan ilimimoni sun kasance tare da ni wanda suka gyara mani tunani wajen ɗaukar matakin bin turbar koyarwa. Ina san ina maida koyarwa cikin da jin daɗi ga ɗalibai
Shin tagwaye na iya yin tunani iri ɗaya da ɗaukar mataki da kuma bayyana ra’ayi iri ɗaya?
Farfesa Hussaini Yusuf: Ba kodayaushe ba, da yawan mutane na hasashen tagwaye na tunanin iri ɗaya, amma na gaskiya ba ne, mu samun banbanci, misali, zan iya cewa ina kaunar wakoƙi shi kuma baya kaunar su. Zan iya zaɓar kala shi kuma ya ga bata yi masa ba.
Ko a wajen aikin mu, ana samun wani lokaci da ɗayan mu zai shugabanci ɗaya a lokuta daban-daban, na taɓa zama shugaban sashen yanzu kuma shi ne shugabana.
Muna ƙalubalantar juna a wajen taron jami’a da kuma sauran tauruka, ince kaza, ya ce a’a. Amma duk lokacin da aka tashi taron sai mu koma gida tare a matsayin yan uwa. Sannan kuma babu yadda za a yi wannan saɓanin na aiki ya shafi alaƙar mu ta uwantaka.
Me ya sanya kuka kasance a tare a tsawon rayuwar ku?
Farfesa Hassan Ishaƙ: Allah ya jikan mahaifin mu, ya cancanci yabo da jingina domin tun muna yara ƙanana, ya ƙarfafa cewa mu halarci makaranta ɗaya, mu zauna aji ɗaya, mu zauna a ɗaki ɗaya, sannan mu karanci darasi iri ɗaya.
Bai taɓa nuna karfi akan mu cewa sai mun karanta kaza ba, amma yana karfafa cewa duk abinda muka zaɓa ya zamana iri ɗaya ne. Lokaci guda ɗaya da muka taɓa rabuwa shi ne lokacin da na tafi Dutsinma aiki shi kuma ɗan uwana ya tafi Dutse Jihar Jigawa. Sai dai mahaifinmu bai nutsu da wannan rabuwa ta mu ba, sai ga shi cikin wata biyu mun sake haɗewa da ɗan uwana
A lokacin bautar ƙasa, sai ya a tabbatar da cewa mun yi aikin bautar ƙasa a wuri guda, wato Union Bank a Maiduguri Jihar Barno. Idan muka duba baya, ya gano cewa kasancewar mu tare zai cigaba da ƙara mana karfi.
Kasancewar ku tagwaye ya baku wata dama a fannin ku na koyarwa ko fannin ilmi?
Farfesa Hassan Ishaƙ: Ƙwarai da gaske, misali lokacin da muke yi tafiya zuwa ƙasar Thailand domin yin digirin mu na biyu, a lokacin ba mu da wurin kwana, amma suna lura da cewa mu tagwaye suka ba mu zaki guda
Haka ma lokacin da muke yin rijistar karatun digirin digirgir (PhD) a jami’ar Ilorin an gaggauta yin mana rijista bayan da aka gano mu tagwaye ne,
Farfesa Hussaini Yusuf: Wannan gogewar ta cigaba har yau, mutane har ƙaguwa suke wajen taimakon mu da zaran sun gano cewa mu tagwaye ne. Wasu har tambayar mu suke mu yi masu addu’a su samu tagwaye. Sannan mahaifin mu kodayaushe yana san mu kasance tare, domin a cewar sa hakan zai ƙara buɗe mana kofofi da dama.
Waɗanne irin nasarori kuma samu da wanda kuke ganin tafi kowace mahimmanci a tsawon zaman ku Malamai?
Farfesa Hassan Ishaƙ: Ɗaya daga cikin nasarorin da muka samu shine kammala karatun digiri na biyu da muka yi tare. Mun fara karatun rana ɗaya sannan muka kammala bincike tare da mun kare aikin da muka yi na bincike tare a gaban mai kula da mu mutum ɗaya, daga ƙarshe mun kammala karatun tare. Wannan zai kasance wani abu da muka cimmawa a rayuwar mu ta karatu.
Ta ya ya wannan dangantaka ta ku ta yi tasiri akan iyalan ku da kuma ƴa ƴan ku?
Farfesa Hussaini Yusuf: Dukkan mu, muna da aure, duk da cewa matan mu ba tagwaye nia ne, amma mun aure su ne daga gari ɗaya sannan sun fahimci dangantakar mu.
Wani abin birgewa shi ne, yadda ƴa ƴan mu suka tashi a tare, ɗiya ta da ɗiyar ɗan uwana suna san sanya kaya iri ɗaya su fita wajen taro, kamar taron Sallah, biki da sauran tarurrukan da suka shafi iyali
Misali idan matata zata tana san sayen kayan ɗiya ta, zata yi sauri ta tambayi Nana fa (ɗiyar ɗan uwana) haka ita ma ɗiyar ɗan uwana zata tambayi Jidda fa, suna san sanya kaya iri ɗaya kodayaushe.
Haka suma ƴa ƴan mu maza suna san kasancewa tare, duk lokacin da za su haɗu suna murna sannan su fara wasa tare.
Sannan Ƴa ƴan mu suna zuwa makaranta ɗaya, suna cigaba da haɗuwa da juna akai akai, sannan suna kaiwa juna ziyara a ƙarshen mako. Wani lokaci idan muka samu jinkirin sukan shirya ziyarar da kan su. Har zuwa yau ɗin nan ba su taɓa samun wani gagarumin matsala ba a tsakanin su, suna da fahimtar juna so sai da so sai.
Ya ya dangantakarku ta taso tun kuna ƙananan har kuka girma?
Dangantakarmu dai kodayaushe muna tare da juna. Kuma mun kasance tare ba ma rabuwa tun muna ƙanana, mu yi wasa tare, sannan ba mu taɓa samun wata matsala da ta raba mu ba, har yau ɗin nan muna tare da juna.
Ya aka yi ku biyu kuka kasance malaman a jami’a ɗaya?
Farfesa Hussaini Yusuf: Bayan mun kammala karatun digirin mu na biyu, mun yi aiki da kungiyoyin cigaba da Bankin duniya da na cigaba ƙasashen Afrika a lokacin kuma muna karatun digirin digirgir (PhD)
Ɗaya daga cikin jagororin mu wato Farfesa Shehu Abdurahman ya shawarce mu da mu ajiye wancan aiki mu koma fannin koyarwa. Mun tuntuɓi iyayen mu, waɗanda suka tallafe mu da cewa mu nemi aikin koyarwa sannan mu halarci tattaunawar ɗaukar aiki kuma aka dauke mu aiki a sashe guda.
Farfesa Hassan Ishaƙ: Mun yi aiki na gajeren lokaci a mabambanta jami’o’i amma a shekarar 2014 ta hanyar gayyatar da mataimakin shugaban jami’ar FUDMA mun sake haɗewa da ɗan uwana kuma tun wannan lokacin muke tare har yanzu
Muna aiki tare, kusan shekaru takwas kafin a kafa sabbin jami’o’in gwamnatin tarayya, inda ɗaya daga cikin mu ya samu aiki a jami’ar Dutse ta Jihar Jigawa ɗaya kuma ya samu a jami’ar FUDMA ta Dutsinma da ke Jihar Katsina
Abin birgewa, jim kaɗan bayan ta kammala gabatar da shaidar takardun kama aiki a jamiar Dutse sai mataimakin shugaban jami’ar FUDMA na wancan lokacin, Farfesa Armayau Hamisu Bichi ya lura da cewa ina da ɗan uwa da muke kama ɗaya wanda shi kuma ya karanci tattalin arziki. Ta hanyar wani ɗalibin mu ne aka gayyace mu da mu nemi aiki a Dutsinma
Kodayake ya riga ya kammala gabatar da duk wasu takardu na shaida a jami’ar Dutse domin fara aiki, daga ƙarshe sai gashi ya ajiye aikinsa cikin wata biyu ya dawo Dutsinma a shekarar 2014, kuma tun wannan lokacin muke a sashe ɗaya, muka cigaba da gwagwarmaya inda har muka kai matakin Farfesoshi a watan Oktoba 2018
Daman sana’ar koyarwa ita ce mafarkin ku?
Farfesa Hussaini Yusuf: Eh! Mu daman kodayaushe muna san koyarwa a manyan makarantu musamman inda muka yi karatu, sai dai ba mu samu aiki ba duk da cewa mun nemi aikin a wajen. Daga ƙarshe dai jagoranci da goyon bayan babban malamin mu ne suka buɗe mana kofa a jami’ar Jihar Nassarawa abinda ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tafiyar mu ta ilimi
Wane ƙalubale kuke fuskanta a matsayin ku na tagwaye a wurin aikin ku?
Farfesa Hassan Ishaƙ: Mutane dai suna ruɗewa ne wajen banbance mu inda wani lokaci abin kan zo da rashin fahimta. Wane lokaci sai an yi bayani sannan komi zai dawo lafiya lau.
Farfesa Hussaini Yusuf: Sannan muna ƙoƙarin tabbatar da cewa ba mu yi gasa ba wajen neman muƙami iri ɗaya, dole ɗaya ya janye ya barwa ɗaya bisa yarjejeniya da amincewa
Akwai wasu abubuwan ban dariya da suka taɓa faruwa da ku a matsayin na tagwaye?
Farfesa Hassan Ishaƙ: Akwai wani abokin mu, da ya riƙa tunanin cewa ɗaya daga cikin mu yana canza kaya duk bayan mintuna wanda ya yi tunanin cewa ko ɗayan mu yana da taɓin hankali kafin daga baya ya gano cewa mu tagwaye ne. Mun yi dariya so sai dukkan mu lokacin da ya gano cewa mu ɗin tagwaye ne.
Har yanzu ɗalibai na ruɗewa wajen gane ku?
Farfesa Hussaini Yusuf: Eh! Musamman sabbin ɗalibai, a wasu lokutan dole sai sun koyi yadda za su gane mu.
Farfesa Hassan Ishaƙ: Wasu lokutan sabbin ɗalibai suna gane mu ne ta hanyar lambar motocin mu a makaranta
Ta ya ya kuke taimakawa junanku a wajen aikin ku?
Farfesa Hassan Ishaƙ: Muna haɗa hannu wajen yin bincike da buga takardu da kuma halartar manyan tarurruka. Mun halarci tauruka na ƙasa da ƙasa tare, kuma yanzu haka muna rubuta littafi tare akan tasirin kimiya
Farfesa Hussaini Yusuf: Sannan muna taimakawa juna wajen koyarwa da sauran ayyukan da suka shafi gudanarwa idan buƙatar Hakan ta ta so.
Wacce shawara gare ku ga matasa masu tasowa?
Farfesa Hassan Ishaƙ: Su kasance masu tunani da ladabi da yarda da Allah, sannan ita nasara tana buƙatar juriya da aiki tukuru.
Farfesa Hussaini Yusuf: Kadda matasa su zama masu kariya akan kowane irin ƙalubalen rayuwa. Ga tagwaye kuwa su kasance masu haɗin kai kadda su bari wani ya shiga tsakaninsu har ya raba su.














