Ruɗani kan badaƙalar kafa hukumar bogi ta haɓaka zuba jari daga ƙasashen waje na ci gaba da zama abin cece- kuce musamman yadda rikita-rikitar ta muzanta gwamnati tare da kwance mata zane a kasuwa.
Taƙaddamar zargin kafa hukumar ta ƙara tsananta ne a kwanan nan a yayin da Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi wasu jami’an hukumomin gwamnati da baiwa Prince Adeniyi Adeyemi damar gudanar da ayyukan hukumar da ta ce ba ta taɓa wanzuwa ba.
Ya zuwa yanzu hankalin al’umma ya karkata ga Fadar Shugaban Ƙasa a yayin da Shugaba Bola Tinubu ya umarci Hukumar Yaƙi da Rashawa ta ICPC da ta gudanar da cikakken bincike kan badaƙalar assasa hukumar ta bogi wadda ya tabbatar da cewar gwamnatii ba ta san da wanzuwar ta ta ba.
Tinubu ya tabbatar da cewar babu wata doka da ta bayar da damar kafa hukumar wanda a kan hakan ya kuma umurci hukumar ICPC da ta kammala bincike cikin kwanaki 30 tare da miƙa masa cikakken rahoto kan sakamakon binciken.
A cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Talata ya jaddada cewa gwamnatin Nijeriya ba ta taɓa kafa hukumar PFIPC ba, kuma hukumar ba ta da wani tanadi a kowace doka, umarnin Shugaban Ƙasa, amincewar ɓangaren zartarwa, ko kuma wata halastacciyar hanyar gwamnati da ta tabbatar da wanzuwarta.
Tinubu ya kuma bayar da umarnin cewa duk wanda bincike ya tabbatar yana da hannu a lamarin a hukunta shi bisa tanade-tanaden dokokin ƙasa ba tare da nunawa kowa ko wace irin alfarma ba.
A kan wannan shugaban ya buƙaci hukumar ICPC da ta binciki zargin ƙirƙira da amfani da jabun takardun naɗin muƙami da yadda aka yi amfani takardar iƙirarin naɗin muƙami daga Shugaban Ƙasa wajen neman ko samun amincewar hukumomi da goyon bayan harkokin diflomasiyya, ciki har da sauƙaƙa samun biza.
Sanarwar ta ce binciken zai kuma duba rawar da duk wani jami’in gwamnati, mutum mai zaman kansa, cibiyoyin kuɗi, mai shiga tsakani ko wata hukuma ko ƙungiya da ake zargin ta taimaka ko ta shiga cikin gudanar da waɗannan ayyukan da ake zargi.
LEADERSHIP Hausa ta ruwaito yadda shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya nesanta kansa da hukumar PFIPC tare da bayyana cewar babu wata hukuma mai wannan sunan wanda a kan hakan jami’an ƴan sanda suka kama Adeyemi a Nuwamba 2025 tare da tsare shi tsawon kwanaki 21.
Haka kuma ya bayyana wanda ke iƙirarin kasancewa shugaban hukumar, Prince Adeyemi a matsayin mayaudari, wanda hakan ne ya haifar da taƙaddamar da ta girgiza manyan matakan aikin gwamnati a Nijeriya.
Rundunar Ƴansanda ta gudanar da bincike kan Adeyemi tare da gurfanar da shi a kotun tarayya da ke Abuja, inda yake fuskantar tuhume-tuhume takwas da suka haɗa da buga jabun takardu da kuma satar suna. Idan aka same shi da laifi, zai fuskanci hukuncin ɗaurin shekaru 21 kan kowanne daga cikin tuhume-tuhume bakwai ba tare da zaɓin tara ba, har zuwa shekaru uku ko kuma biyan tara kan ɗaya daga cikin sauran tuhume-tuhumen.
Haka ma Gwamnatin Tarayya ta sanya Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila da wasu mutum goma cikin jerin shaidun da za ta gabatar a shari’ar
Sai dai Adeyemi ya ci- gaba da jaddada cewa ba shi da laifi, tare da zargin Femi Gbajabiamila da yaɗa ƙarya a iƙirarin cewar hukumarsa ta bogi ce tare da alwashin kare kansa a gaban kotu a ranar 27 ga Yuli.
Tuni jam’iyyun adawa a Nijeriya suka yi Allah- wadai da faruwar lamarin wanda suka bayyana a matsayin abin kunya da tozarci kamar kuma yadda ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar adawa ta ADC Atiku Abubakar da ƙungiyar Kwankwasiyya da ƙungiyoyin farar suka buƙaci gwamnati ta yi cikakken bayanin yadda aka assasa hukumar tare da ware mata kuɗi a kasafin kuɗi.
Hayagagar da ta dabaibaye badaƙalar ta ƙara ɗaukar sabon salo a ranar Litinin a yayin da Rundunar Ƴan Sanda ta kama mahaifin Adeyemi a daidai lokacin da ake ci- gaba da binciken hukumar da ake zargin ta bogi ce.
Fitaccen lauya mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana (SAN) da wasu shaidun gani da ido sun tabbatar da kama mahaifin Adeyemi da wani aminin iyalansa a gidansa a ranar Litinin yana cewar babu hujjar kama mahaifin Adeyemi domin wanda ake zargi ya yi alƙawalin gabatar da kan sa a kotu.
Tun da farko badaƙalar ta fito sarari ne a yayin da Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana ɓullar hukumar bogi a ƙarƙashin jagorancin Adeyemi wadda ake zargin ba ta taɓa wanzuwa ba, amma aka ware mata naira biliyan 1.3 a cikin Kasafin Kuɗin shekarar 2026 da buɗe mata ofis a sakatariyar gwamnatin tarayya, ɗaukar ma’aikata da buɗe asusun ajiya a babban bankin ƙasa.
A sanarwar da Kakakin Shugaba Tinubu Bayo Onanuga ya fitar ya bayyana cewar PFIPC, hukuma ce ta bogi da gwamnati ba ta san da ita ba wadda Adeyemi ke damfarar ofisoshin jakadanci na ƙasashen waje da cibiyoyin kuɗi don haka ta umurci hukumar yaƙi da cin hanci ta ICPC da ta gudanar da bincike mai zaman kansa kan lamarin.
Yayin da Fadar Shugaban Ƙasa ke nanata cewa majalisar ba ta taɓa wanzuwa ba, masu sukar lamarin na cewa rahotannin da ke nuna cewar an warewa hukumar kuɗi a kasafin kuɗi sun haifar da tambayoyi masu muhimmanci da ke buƙatar bincike mai zaman kan sa domin fayyace gaskiya.
Bugu da ƙari a wata sanarwa da ya fitar a makon nan, babban mataimaki na musamman ga Shugaban Ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Temitope Ajayi, ya ce ya zama wajibi masu bincike daga Hukumar tsaron farin kaya ta DSS da Rundunar Ƴan Sanda da Hukumar Yaƙi da cin hanci ta EFCC su gano tare da gurfanar da jami’an gwamnati da ake zargin sun taimakawa Adeyemi wajen aiwatar da aika- aikar.
A cewar Ajayi, babu shakka akwai sa hannun ƴan cikin gida waɗanda suka taimakawa Adeyemi wajen ƙirƙirar takardun naɗin mukami na bogi da aka jinginawa Shugaban Ƙasa, buɗewa da gudanar da asusun banki guda 34 da sunayen hukumomin gwamnati da babu su, karɓar baƙuncin jakadun ƙasashen waje, har ma da buɗe asusu a Babban Bankin Ƙasa yayin da yake gabatar da kansa a matsayin shugaban hukumar.
Ajayi ya ce “Abin da babu tababa a kai shi ne cewa wasu da suka sa hannu daga cikin jami’an gwamnati ne suka baiwa Adeniyi damar kaiwa wannan matsayi. Wannan shi ne ainihin abin da masu bincike daga DSS, ƴan sanda da EFCC ya zama wajibi su bankaɗo. Dole ne a tarwatsa wannan ƙungiyar ta masu aikata laifuka da ke cikin hukumomin da abin ya shafa, sannan a kama tare da gurfanar da duk wanda bincike ya tabbatar yana da hannu a lamarin.”
Ajayi ya kuma bayyana Adeyemi a matsayin “Ƙwararren ɗan damfara wanda ya fahimci yadda jama’a ke kallon batun cin hanci da rashawa, ya kuma yi amfani da hakan wajen jefa sunan Gbajabiamila cikin taƙaddamar domin kare kansa daga ɗaukar alhakin laifukan da ake zarginsa da aikatawa.”
A cewarsa duk da cewa masu sharhi da dama sun soki gazawar hukumomin da lamarin ya shafa da baiwa zargin damfarar damar ci-gaba na tsawon lokaci, sun yi watsi da gaskiyar cewa tsarin gwamnatin ne dai daga bisani ya gano waɗannan kura-kurai da kuma abubuwan da ba su dace ba tare da takawa aika- aikar.
A ranar 11 ga Yuni 2026 ne dai Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila ya fitar da sanarwar musanta hukumar tare da sanar da ofisoshin jakadancin ƙasashen waje, cibiyoyin kuɗi da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa cewa PFIPC ba ta da wata sahihin matsayi a hukumance, kuma ba a taɓa naɗa kowane irin muƙami a ƙarƙashin ta ba.
Da yake bayani kan badaƙalar, Atiku Abubakar ya zargi Shugaba Tinubu da cewa ko dai yana da hannu a cikin abin da ya bayyana a matsayin babban kuskure da ake zargi sun dabaibaye taƙaddamar hukumar ta bogi, ko kuma bai san abin da ke faruwa a gwamnatinsa ba.
A cikin wata sanarwa da kakakinsa Phrank Shaibu ya fitar a wannan makon, Atiku ya ce yunƙurin da Fadar Shugaban Ƙasa ke yi na kare Femi Gbajabiamila daga zarge-zargen da suka shafi taƙaddamar PFIPC ya ƙara haifar da shakku a tsakanin jama’a maimakon kwantar da shi.
A cewarsa “Dabarun siyasa da Fadar Shugaban Ƙasa ke amfani da su domin wanke Gbajabiamila daga yawaitar zarge-zargen da suka dabaibaye badaƙalar hukumar bogi sun ƙara jefa gwamnatin Tinubu cikin abin kunya da kuma ƙara haifar da shakku a idanun jama’a.”
Wazirin Adamawa ya kuma yi nuni da zarge-zargen da Adeyemi ya yi, inda ake cewa ya yi iƙirarin cewa Gbajabiamila ya buƙaci a ba shi biliyoyin naira domin sauƙaƙa masa samun muƙamin shugaban hukumar, a cewar zargin, an buƙaci a fara biyan naira miliyan 400, sannan da kuma kusan rabin kuɗin tallafin fara aiki na PFIPC da ya kai naira biliyan 27.4, wato kimanin naira biliyan 12.5.
Atiku ya ce “Fadar Shugaban Ƙasa ba za ta iya kawar da waɗannan zarge-zarge da sanarwar manema labarai ko hujjojin siyasa kawai ba, alhali bayanan da ke fitowa na ƙara nuna wata al’ada mai tayar da hankali ta rashin hukunta masu laifi.”
Ya ce badaƙalar na ɗaukar wani salo da ya bayyana a matsayin wanda ya fi tayar da hankali fiye da badaƙalar kuɗaɗen fansho ta Abdurrashid Maina yana cewar hukumomin tsaro sun ɗauki matakin gaggawa a shari’ar da ta shafi Maina, saɓanin yadda gwamnati ke tafiyar da zarge- zargen badaƙalar PFIPC.
Atiku ya kuma buƙaci Majalisar Tarayya da ta ta yi bayani kan yadda tanade-tanaden kasafin kuɗi suka tsallake tantancewar majalisar dokoki. Ya ce an kafa Majalisar ne domin kare dukiyar al’umma ba domin a bar kura-kurai bayyanannu su wuce ba tare da an bincike su ba.
Haka ma ƙungiyar Kwankwasiyya ta bayyana cewa taƙaddamar ta wuce batun ayyukan mutum guda kaɗai, ta ce lamari ne daya shafi yadda gwamati ke gudanar da harkokin ta bakiɗaya.
A cikin wata sanarwa da kakakin Kwankwasiyya, Habibu Sale Mohammed ya sanyawa hannu, ƙungiyar ta ce nacewar da Fadar Shugaban Ƙasa ke yi cewa hukumar ba ta taɓa wanzuwa ba, ba ta amsa muhimman tambayoyin da suka taso daga rahotannin da ke nuna cewa an ware sama da naira biliyan 1 ga wata hukuma mai irin wannan suna ko makamancin ta a cikin Kasafin Kuɗin 2026 ba.
“Idan har wannan hukumar ba ta taɓa wanzuwa ba, ta yaya sunanta ya samu shiga cikin kasafin kuɗin ƙasa? Wa ya gabatar da buƙatar ware mata kuɗi, kuma wa ya amince da hakan? Waɗanne ofisoshin gwamnati ne suka sarrafa takardun da suka shafi ware kuɗin? Shin an fitar ko an ƙudiri aniyar fitar da kuɗin gwamnati a ƙarƙashin wannan tsari? Idan kuma a na zargin an yi jabun takardun hukumar, ta yaya aka bari a na amfani da su na tsawon lokaci ba tare da an gano hakan ba?”
Ƙungiyar ta bayyana cewa waɗannan tambayoyi ba na batun siyasa ba ne, illa batutuwan da suka shafi haƙƙin jama’a a kan gwamnati. A cewar ta yadda gwamnatin Tinubu za ta nuna ƙudurinta na gaskiya, riƙon amana da bunƙasa cibiyoyin gwamnati, zai dogara ne da shirinta na bayar da cikakken bayani kan lamarin.
Sai dai matsayar da Fadar Shugaban Ƙasa ta ɗauka na ci-gaba da fuskantar suka daga sassa daban-daban kamar daga irin fitaccen lauya mai rajin kare haƙƙiin ɗan Adam, Femi Falana wanda ya riga ya bayyana cewa Fadar Shugaban Ƙasa ba ta da hurumi a kundin tsarin mulki na wanke kan ta ko kuɓutar da kowa daga zargin da ke da alaƙa da badaƙalar.
Falana ya buƙaci Hukumar ICPC da ta gudanar da bincike mai zaman kansa kan Femi Gbajabiamila da kuma Adeniyi Adeyemi domin bankaɗo gaskiyar lamari tare da bayyanawa duniya.
Haka ma lauyan ya buƙaci a yi cikakken bayani kan yadda ake zargin an ware biliyoyin naira a kasafin kuɗi domin hukumar da a yanzu gwamnati ke cewa ba ta taɓa wanzuwa ba, da kuma yadda aka bar ta tana gudanar da ayyuka a cikin hukumomin gwamnati na tsawon lokaci ba tare da an dakatar da ita ba.














