ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, July 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi

by Ra'ayinmu
39 seconds ago
Discarded tyres being processed at the Freee Recycle factory. 2 April 2024. Ibadan, Nigeria. Photo by Zaniel Dada, bird story agency.

Discarded tyres being processed at the Freee Recycle factory. 2 April 2024. Ibadan, Nigeria. Photo by Zaniel Dada, bird story agency.

Ana ci gaba da tabka zazzafar muhara, matakin ƙasa, kan shirin Gwamnatin Tarayya, na yunƙurin daƙile barin yin amfani da Robobin da ke haifar da gurɓatar muhalli, a ɗaukacin faɗin ƙasar.

Masu yin muhawarar na ganin ta yaya za a iya fayyace, batun kare mhulali da kuma batun ƙara bunƙasar, tattalin arzikin ƙasar.

Batun da yafi jan hankali ga muharar shi ne, yunƙurin Gwamnatin, na shirin wanzar da cikakun dokokin kare muhalli na ƙasa wato dai daƙile yadda ake zubar da Robobin na   2026, tare da kuma shin, ina batun nauyin da aka ɗorawa Hukumar Kula da Muhalli ta Ƙasa wato NESREA.

ADVERTISEMENT

Misali, an dai ɗorawa NESREA nauyin haramta sarrafa Robobin da kaurinsu ƙasa da kaso 80, a cikin ɗari, wanda take wannan umarnin, zai iya sanya wa, a ƙaƙabawa duk masana’antar da aikata haka, haraji.

A ɗaukacin faɗin duniya dai, Gwamnatocin su, tuni suka ɗauki matakan da suka dace, na daƙile yaɗuwar irin waɗannan Robobin da ke janyo gurɓatar yanayi, musamman duba da yadda Robobin, ke shafar kiwon lafiyar alumma da haifar da ɗumamar yanayi.

LABARAI MASU NASABA

Kisan Gillar Marabar Jos: Bai Kamata Jinin Malama Ummulkhairi Ya Tafi A Banza Ba

Buƙatar Mayar Da Hankali Wajen Kawo Ƙarshen Ciwon Sikila A Nijeriya

Kazalika, Robobin na kuma toshe magudanan Ruwa, wanda hakan, ke janyo aukuwar ambaliyar Ruwa da gurɓata Ruwan da haifar da illa ga gonakai da kuma shafar rayukan dabbobin, da ke rayuwa a cikin Tekuna.

Tsarin na haramtawa da dakatar da yin amfani da irin wannan Robobin, na ci gaba da karɓuwa, musamman, domin ɗaukar matakan kula da yadda za a rage yaɗuwar Robobin a cikin alumma.

Sai dai, za a iya cewa, wannan batun a ƙasar nan, za a iya cewa, yana da matuƙar wuya, a iya wanzar da hakan, musamman, duba da cewa, Nijeriya a matsayin ƙasa mai tasowa, na ci gaba da fuskantar matsin tattalin arziki, rashin aikin a tsakanin wasu ƴan ƙasar, ƙalubalen da wasu masana’antun ƙasar, ke ci gaba da fuskanta, tare da rashin, ingantatun kayan aiki, inda saboda irin waɗannan matsalolin da muka zayyano, yunƙurin na harmta sarrfa Robobin, tamkar abu da za a iya cewa, zai yi wuya.

Misali, tuni dai ƙungiyar kula da masana’antu ta ƙasa  MAN, ta fara mayar da martini, kan wannan tsarin na Gwamnatin, tare da yin gargaɗin cewa, dakatar da masana’atun da ke sarrafa Robobin a ƙasar, zai haifarwa da masana’antun, illa da kuma haifar da wawan giɓi, ga fannin tattalin arziki.

Ƙungiyar ta yi nuni da cewa, kamata yayi a daƙile yadda Robobin ke haifar da gurɓatar yanayi, musamman ta hanyar inganta yadda ake tattara Robobin da ake watsarwa a ƙasar, ko sake mai-maita da kuma samar da kyakawan tsarin na tara su, amma ba wai kawai, a harmata sarrafa su ba, duba da cewa, yin hakan, zai shafi sana’ar da kuma sauran ma’aikatan da aki, a irin waɗannan, masana’atun, masu sarrafa Robobin.

Darakta Janar na MAN Segun Ajayi-Kadir, ya yi nuni da cewa, tuni Gwamnatin ta samar da tsarin haɗaka na ƙasa a tsakaninta da Ma’akatar Kare Muhalli ta Tarayya, wato NPAP tun a 2024 na daƙile yaɗuwar Robobin.

Sai dai, ya ce, amma Gwamnatin, ta gaza wanzar da manyan  shawarwarin, da ke a cikin tsarin na  NPAP.

A saboda wannan gazawar da kuma yunƙurin na Gwamnatin, na bijiro da batun wani sabon tsarin, tamkar ƙara mai-maita, ƴar gidan jiya ne.

Bugu da ƙari, ƙungiyar ta buga misali da tsarin na haramta sarrafa Robobin da ƙasashe kamar irinsu, Kenya, Ɓangladesh, Afirka ta Kudu da kuma Indiya, inda mahukuntan ƙasar, suka fuskanci, kakkausar suka, kan matakin.

Duk da ƙara ƙarfafa wayar da kai, da waɗannan ƙasashen suka yi, na ɗaukar matakin haramtawar da samar da ƙarin wasu tsare-tsare kan batun, bayan wanzar da makin, hakan ya haifar garƙame, masana’antun da ke a ƙasashen da sarrafa Robobin wanda hakan, ya janyo rasa aikin yi, inda kuma duk da hakan, wasu masana’antun, suka ci gaba da sarrafa Robobin, ta ɓarauniyar hanya.

Ƙasashe kamar irinsu Jamus, Koriya ta Kudu da kuma Netherlands, mai makon su haramtawa masana’atun da ke sarrafa irin waɗannan Robobin, sun cimma nasara, kan samar da tsarin daƙile yaɗuwar Robobin tare da zuba jari na shirye-shiryen kula da yadda ake kula da yaɗuwar Robobin.

A saboda haka, ta MAN buƙaci Gwamnatin, da ta dakatar da wannan yunƙurin na ta, na haramtawa kamfanonin sarrafa irin waɗannan Robobin, har zai idan, ta samar da wasu cikakkun, ƙa’idoji.

A gefe ɗaya, Hukumar ta NESREA, ta jadda cewa, tsarin da Gwamnatin ke shirin yi, an masa mumunar fahimta, inda ta ce, manufar tsarin, ba wai bias nufin janyo koma baya ga masana’antun da ke sarrafa irin waɗannan Robobin ba ne, amma nufin shi ne, domin Gwamnati ta saita yadda masana’antun ke sarrafa Robobin, inda za su kai mataki irin na duniya, musamman domin  kula da daƙile yaɗuwarsu, barkatar bayan an yi amfani da su.

A ɓangaren da Gwamnati da kuma masana’antun duk suna da haƙƙi, wanda hakan ya nuna cewa, tabbas, ya zama wajbi, a Nijeriya a ɗauki matakan daƙile yaɗuwar Robobin barkatai, musamman duba da yadda suke haifar da gurɓatar muhalli.

Sai dai, ya kamata a yi tunani mai zurfi, wajen ɗaukar tsauraran matakai irin na matakin duniya, na haramta sarrafa Robobin, duba da yanayin matsin tattalin azrki a ƙasar.

Haka zalika,  bai wai kawai batun rage dogaro da yin amfani da Robobin ne batun ba,  amma ƙalubalen shi ne, a yaya ne, za a iya ciimma nasarar daƙile yaɗuwar Robobin, ba tare da an shiga haƙƙin masana’antun da ke sarrafa su ba.

A namu ra;ayin ya zama wajbi, a yi duba da kyakywar basirar da ta dace, kafin Gwamnatin ta zanzar da tsarin na haramtawar.

Muna bayar da shawara, da a rungumi yin amfani da tsari na zamani, musamman wajen zuba jari, kan yadda ake juya irin waɗannan Robobin, da aka gama yin amfani da su, mai makon kawai, a rinƙa watsar da su, barkatai, a cikin allumma wanda hakan, ke haifar da guraɓar muhalli da shafar lafiyar jama’a.

Akwai kuma buƙatar Gwamnatin ta bazama wajen yin gamgamin wayar da kai, kan illolin da ke tattare da watsar da irin waɗannan Robobin.

Babban abinda ake son cimma buri shi ne, samar ingantacciyar tsafta a ƙasar, amma ba tare da durƙusar da tattalin arzikin ƙasar da kuma shafar yuwar ƴan Nijeriya ba.

Ra'ayinmu
+ postsBio
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Kisan Gillar Marabar Jos: Bai Kamata Jinin Malama Ummulkhairi Ya Tafi A Banza Ba
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Shin Nijeriya Ta Shirya Tunkarar Dawowar Annobar Ebola?
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Buƙatar Samar Da Alƙibla Ta Musamman Ga Gidajen Gyaran Hali Na Ƙasar Nan
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Ce-ce-ku-ce Kan Batun Biyan Bashin Naira Tiriliyan 3.3 Na Kuɗin Lantarki

MASU ALAKA

Kisan Gillar Marabar Jos: Bai Kamata Jinin Malama Ummulkhairi Ya Tafi A Banza Ba
Ra'ayinmu

Kisan Gillar Marabar Jos: Bai Kamata Jinin Malama Ummulkhairi Ya Tafi A Banza Ba

July 3, 2026
sikila
Ra'ayinmu

Buƙatar Mayar Da Hankali Wajen Kawo Ƙarshen Ciwon Sikila A Nijeriya

June 26, 2026
Shin Nijeriya Ta Shirya Tunkarar Dawowar Annobar Ebola?
Ra'ayinmu

Shin Nijeriya Ta Shirya Tunkarar Dawowar Annobar Ebola?

May 29, 2026

LABARAI MASU NASABA

Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi

Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi

July 10, 2026
Asusun IMF Ya Rage Hasashen Bunkasar Tattalin Arzikin Duniya, Ya Kuma Kara Na Sin

Asusun IMF Ya Rage Hasashen Bunkasar Tattalin Arzikin Duniya, Ya Kuma Kara Na Sin

July 9, 2026
Alkaluman Farashin Kayayyakin Masarufi Na Kasar Sin Sun Karu Da Kaso 1 A Watan Yuni

Alkaluman Farashin Kayayyakin Masarufi Na Kasar Sin Sun Karu Da Kaso 1 A Watan Yuni

July 9, 2026
‘Yansandan Jihohi Za Su Bai Wa Gwamnoni Cikakken Iko Wajen Yaƙi Da Matsalar Tsaro — Gwamna Dauda

‘Yansandan Jihohi Za Su Bai Wa Gwamnoni Cikakken Iko Wajen Yaƙi Da Matsalar Tsaro — Gwamna Dauda

July 9, 2026
Taron Intanet Na Sin Karo Na 25 Ya Bayyana Yadda Ake Amfani Da Fasahar AI A Rayuwar Yau Da Kullum

Taron Intanet Na Sin Karo Na 25 Ya Bayyana Yadda Ake Amfani Da Fasahar AI A Rayuwar Yau Da Kullum

July 9, 2026
Tunanin Xi Jinping kan JKS: Hikimar Mulki Ta Farfado Da Kasa Da Kuma Tasirinta A Duniya

Tunanin Xi Jinping kan JKS: Hikimar Mulki Ta Farfado Da Kasa Da Kuma Tasirinta A Duniya

July 9, 2026
Rashin Tsaro: Tinubu Ya Gana Da Shugabannin Hukumomin Tsaro

Rashin Tsaro: Tinubu Ya Gana Da Shugabannin Hukumomin Tsaro

July 9, 2026
Motoci Masu Aiki Da Lantarki Kirar Kasar Sin Na Kara Samun Tagomashi A Kasuwannin Duniya

Motoci Masu Aiki Da Lantarki Kirar Kasar Sin Na Kara Samun Tagomashi A Kasuwannin Duniya

July 9, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Ɗaga Albashin Sojoji Daga Naira 49,000 Zuwa Naira 100,000 – Ministan Tsaro

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗaga Albashin Sojoji Daga Naira 49,000 Zuwa Naira 100,000 – Ministan Tsaro

July 9, 2026
An Gabatar Da Shirin Fadar Potala Ta Kafar CMG

An Gabatar Da Shirin Fadar Potala Ta Kafar CMG

July 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.