ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yansandan Jihohi Za Su Bai Wa Gwamnoni Cikakken Iko Wajen Yaƙi Da Matsalar Tsaro — Gwamna Dauda

by Sulaiman
2 months ago
Yansanda

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa kafa rundunar ‘yan sandan jihohi zai taimaka matuƙa wajen magance matsalar rashin tsaro a Nijeriya, domin hakan zai bai wa gwamnoni cikakken iko da ya dace da su matsayin su na manyan jagororin harkar tsaron jihohin su.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake matsayin ɗaya daga cikin masu tattaunawa a taron Arise News Town Hall Summit mai taken “Gina Matsaya Kan ‘Yan Sandan Jihohi da Tsaron Ƙasa”, wanda aka gudanar a ThisDay Dome da ke Abuja.

A cikin wata sanarwa da Sulaiman Bala Idris, Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfaraya fitar a ranar 9 ga Yuli, 2026, Dauda Lawal ya ce, ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka sa rashin tsaro ya daɗe yana addabar jihohi shi ne kasancewar tsarin bayar da umarni da jagorancin jami’an tsaro ba ya ƙarƙashin gwamnoni, duk da cewa ana kiransu manyan jami’an tsaron jihohinsu.

ADVERTISEMENT
Yansanda

Ya ce, idan aka bai wa gwamnatocin jihohi alhakin kare rayuka da dukiyoyin jama’a a yankunansu, hakan zai ƙarfafa rundunar ‘yan sanda ta fuskar kayan aiki da kuma yawan jami’an da za su iya yaƙi da miyagun laifuka.”Ana kiranmu manyan jami’an tsaron jihohi, amma tsarin bayar da umarni da jagorancin jami’an tsaro ba ya ƙarƙashin gwamnoni.

“Na yi farin ciki da ci gaban da aka samu kan batun kafa ‘yan sandan jihohi, domin hakan zai ba mu damar sauke nauyin da ke kanmu, tare da bai wa al’umma damar riƙa ɗora mana alhakin halin tsaro a jihohinmu.”

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

Gwamnan ya ƙara da cewa, yana da cikakken yaƙinin cewa da zarar an kafa rundunar ‘yan sandan jihohi, za ta taimaka sosai wajen shawo kan yawancin matsalolin tsaro, tare da bai wa gwamnoni damar zama manyan jami’an tsaro na haƙiƙa a jihohinsu.

Da yake mayar da martani kan fargabar cewa gwamnoni za su iya amfani da rundunar wajen musguna wa ‘yan adawa, Dauda Lawal ya ce kusan dukkan jihohin ƙasar nan na da wasu hukumomi ko rundunonin tsaro na cikin gida, amma ba a yi amfani da su wajen danne ‘yan adawa ba.

Yansanda

Sai dai Gwamnan ya buƙaci Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta samar da ƙa’idoji da kariya da za su hana duk wani amfani da rundunar ba bisa ƙa’ida ba.

“Ina goyon bayan kafa ‘yan sandan jihohi. Na fahimci damuwar da wasu ke da ita game da yiwuwar cin zarafi, amma idan aka samar da ingantattun dokoki da tsare-tsare, za a kawar da wannan fargaba.”

An shirya taron ne domin cimma matsaya kan batun kafa ‘yan sandan jihohi da kuma sauye-sauyen da suka shafi tsaron ƙasa, yayin da matsalar rashin tsaro ke ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan batutuwan da suka fi daukar hankalin ‘yan Nijeriya.

Taron ya haɗa manyan jami’an tsaro, gwamnoni, ‘yan majalisu, ƙungiyoyin fararen hula, ƙwararrun masu tsara manufofi, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna hanyoyin ƙarfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin ƙasar.

Yansanda
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang
  • Sulaiman
    Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris
  • Sulaiman
    Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu
  • Sulaiman
    Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

MASU ALAKA

Yansanda
Labarai

Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

September 11, 2026
Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya
Labarai

Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

September 11, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu
Labarai

Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang

September 11, 2026
Next Post
Alkaluman Farashin Kayayyakin Masarufi Na Kasar Sin Sun Karu Da Kaso 1 A Watan Yuni

Alkaluman Farashin Kayayyakin Masarufi Na Kasar Sin Sun Karu Da Kaso 1 A Watan Yuni

LABARAI MASU NASABA

Yansanda

Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

September 11, 2026
Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

September 11, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang

September 11, 2026
Yansanda

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026
Yansanda

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris

September 11, 2026
Yansanda

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA

Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.