Ammar Muhammad" />

Lalong Ya Zama Sabon Shugaban Gwamnonin Arewa

Rahotannin da suke shigowa LEADERSHIP A YAU ya nuna cewa; gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya zama sabon shugaban kungiyar gwamnonin Arewa. Gwamnan jihar Borno, Kassim Shettima kafin zaben wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin arewan, shi ne ya bayyana haka a karshen zaman da suka gudanar a garin Kaduna.

Kassim Shettima  ya ce suna da imanin cewa Gwamna Lalong yana da kwarewar da zai kawo wa yankin ci gaba. Kuma suna fatan zai dora daga inda tsoffin shugabannin gwamnonin Arewan suka tsaya.

Ya ci gaba da cewa; zabar gwamnan Lalong a matsayin sabon shugaban yana da nasaba da zaman lafiyar da ya kawo wa mutanen jiharsa.

A karshe ya jinjinawa membobin kungiyar ta su da suka zabi Lalong a matsayin sabon shugaban gwamnonin Arewan, inda ya shawarce da su ba shi dukkanin gudummawar da za su iya wajen ganin ya samu nasara.

Exit mobile version