Lantarki Ya Kashe Wani Lokacin Da Yake Satar Waya A Kano

Daga Sulaiman Ibrahim,

Wani mutum da ba a tantance ko wane ne ba ya gamu da ajalinsa yayin da yake kokarin satar wayoyin taransfoma a kauyen Lambu da ke karamar hukumar Tofa a Kano.

Daily trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 1 na daren Laraba.

Wani mazaunin kauyen mai suna Naziru Lambu ya bayyana cewa, mutumin da wutar lantarkin ta kama, ya yi nasarar cire wasu wayoyin da ke cikin taransfoma din, ya ajiye su a kusa da taransfomar.

Ya ce mazauna kusa da wurin sun shaida cewa sun ji karar wutar lantarki a cikin dare sannan kuma suka ji kururuwar mutumin kafin ya mutu.

Ya kara da cewa jami’an hukumar tsaro ta NSCDC da wakilan kamfanin samar da wutar lantarki ta Kano (KEDCO) sun isa garin domin duba lamarin.

Exit mobile version