El-Zaharaddeen Umar">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Layin Dogo Daga Nijeriya Zuwa Nijar: Wace Rawa Hukumar NIS Za Ta Taka?

by El-Zaharaddeen Umar
February 12, 2021
in LABARAI
3 min read
Layin Dogo Daga Nijeriya Zuwa Nijar: Wace Rawa Hukumar NIS Za Ta Taka?
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Tunanin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi na samar da hanyar sufurin jirgin kasa da aka fi sani da layin dogo zai taimaka matuka gayya a fannoni daban-dabn da suka shafi huldar difolimasiya tsakanin kasa da kasa.
Ana sa ran cewa tattalin arziki zai cigaba musamman a yankin arewa, musamman saboda irin matsalolin da aka fuskatan matsalolin tsaro da ‘yan bindiga da boko Haram da suka tarwatsa harkokin daban-daban
Haka tasa dole Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa (NIS) za ta shigo cikin wannan hulda domin ganin komi ya tafi daidai bisa doka da tsarin da gwamnatocin suka amince da shi a hukumance.
Domin ba za a taba tuya a manta da albasa ba, dole ne a ba su mahimmacin na daban saboda su ne za su fi kowa aikin na sa ido shige da fice da duk wani motsa na kasa da kasa a huldar difolomasiya
A cikin wannan makon da muke ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da fara aikin layin dogo da ya taso daga jihar Kano ta ratsa ta jihar Jigawa ta biyo ta danbatta zuwa Daura ta wuce Katsina har zuwa jihar Maradin Jamhuriyar Nijar.
Babu shakka wannan wani cigaba ne da ake fatan kasashen guda biyu za su ci amfaninsu da zaran an kammala, saboda haka masu ruwa da tsari na hukumomin tsaro dole ne su kara himma da kwazo wajan yin aikin su na yau da kullun.
Hukumar NIS a karkashin jagorancin shugabanta, CGI Muhammad Babandede ita ce kan gaban wajan ganin abubuwa na tafiya bisa doka kafin a zo maganar jami’an Kwaston wadanda suke ta’amili da kayayyaki ne kawai.
Irin yadda jama’a ke tuturuwa zuwa cikin Nijeriya ba bisa ka’ida ba, ya sa dole hukumar NIS ta kara bude idonta da zaran an fara wannan aiki, domin shi jirgin ba wai kayayyaki kadai zai rika dauka ba, har da jama’a wadanda ke san bijirewa ka’adar da kasa da kasa suka gindaya a hukumance.
Shugaban hukumar NIS na kasa Muhammed Babandede na daga cikin manya- manyan kusoshin gwamnatin tarayya da suka halarci wannan gagarumin bikin dora harsahin gina wannan hanya ta layin doga da ta taso daga jihar Kano za ta yada zango a jamhuriyar Nijar, a jihar Katsina.
Saboda haka kasancewarsa a wannna wuri bababr alama ce da ke nuni da irin shugabancinsa na wannan hukuma, kuma a shirye yake domin ganin sun hada hannu da sauran jami’an tsaro domin kawo sauyi mai ma’ana da zaran wannan aikin ya kammala.
Shi ne kadai shugaban hukumar tsaro na kasa da ya halarci wannan bikin saboda mahimmacin hukumarsa a cikin wannan al’amari da zarar an kammala aikin a shekarar 2023.
Muhammed Babandede abin ya zame masa guda biyu, bayan kasancewarsa shugaban wannan hukuma kuma har ila yau shi haifafan Jihar Jigawa ne saboda haka haka za a ga aiki sosai.
Ko shakka babu wannan hukumar akwai jan aikin gabanta duk da kasacewar tana bakin kokarinta, saboda haka yanzu wani sabon kalubale danye zo musu, wanda za su kara shirin da sabuwar damara domin tunkarar wannan aikin na musamman.
Tunda wannan cigaba ya zo lallai akwai bukatar gwamnatin tarayya ta sake duba da idanun basira akan wannan hukuma ta NIS ta hanyoyi daban-daban domin kwalliya ta biya kudin sabulu.
Haka kuma akwai tabbacin cewa shugaban wannan hukuma a tsaye yake wajan ganin ya sauke nauyin da ya rataya akan sa musamman abinda ya shafi kan iyakokin Nijeriya da Nijar da kuma wasu sauran kasashe da suke makwabtaka da Nijeriya.
Su kan su ma’aikatan wannan hukuma sun samu shaida wajan yin bakin kokarinsu, to ina ma a ce sun kara samun kwarin gwiwa a wajan gwamnati ta hanyar kara samar musu da na’urorin aiki na zamani da sauran kayan aiki da za su taimaka wa aikin da suke yi ba-dare-ba-rana.
Hatta jama’ar gari suna da tasu gudunmawar da za su ba da musamman taimaka wa wadannan jami’ai na hukumar NIS da bayanan sirri da za su taimaka wa aikinsu a samu nasarar da ake butaka.

SendShareTweetShare
Previous Post

Ya Kamata Gwamnatin Buhari Ta Tallafa Wa Manoman Timatir – Musa Dan Muhammad

Next Post

Babandede Ya Jagoranci Taron Dora Kwangilolin NIS A Sikeli Na Shekarar 2021

RelatedPosts

Alkalin Kotun Koli, Ngwuta, Ya Rasu A Abuja

Alkalin Kotun Koli, Ngwuta, Ya Rasu A Abuja

by El-Zaharaddeen Umar
11 hours ago
0

Daga Sulaiman Ibrahim Mai Shari’a Sylvester Ngwuta, alkalin kotun koli...

Tinubu Ya Bukaci Matasa Su Nisanci Bangar Siyasa

by El-Zaharaddeen Umar
18 hours ago
0

Daga Bello Hamza, Jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya...

E Call

Shirin Kula Da Zirga-zirgar Manyan Motoci Na ‘E-Call’ Zai Kawo Karshen Cunkoso A Tashar Jiragen Ruwan Nijeriya -Hadiza Bala Usman

by El-Zaharaddeen Umar
18 hours ago
0

By Bello Hamza, An tabbatar wa masu hulda da tashoshin...

Next Post
Babandede Ya Jagoranci Taron Dora Kwangilolin NIS A Sikeli Na Shekarar 2021

Babandede Ya Jagoranci Taron Dora Kwangilolin NIS A Sikeli Na Shekarar 2021

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version