Kamfanin LEADERSHIP wallafa jaridar Leadership ta Turanci da Hausa, sun kara karfafa dangantakarsa da kamfanin yada labarai na Kasar Sin (CMG) don fadada aiki tsakanin kamfanonin biyu.
Wannan ci gaban ya samo asali ne lokacin da tawagar CMG karkashin jagorancin babban daraktan cibiyar shirye-shiryen harsunan Asiya da Afirka, An Xiaoyu, ta kai ziyarar aiki hedikwatar kamfanin LEADERSHIP da ke Abuja a ranar Talata.
- Fadan Sudan Ya Hana Kananan Yara Samun Ilimi —UNICEF
- Dokokin Da Buhari Ya Sanya Wa Hannu Kafin Barin Mulki
Sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya da ke da nufin kawo sabbin matakai da za su amfanar da kamfanonin biyu.
Da take maraba da tawagar CMG, shugabar kamfanin LEADERSHIP Group Limited, Misis Zainab Nda-Isaiah, ta ce ziyarar ta yi daidai domin za ta karfafa hadin gwiwar da ke tsakanin manyan kafafen yada labarai biyu da aka fara a shekarar 2018.
Ta kuma kara da cewa, kamfanin LEADERSHIP na da tsari da hangen nesa don bunkasa ayyukansa, ta kuma bukaci kafar ta kasar Sin da ta taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da dangantakar da ke tsakaninsu zuwa wani mataki.
Ta ce, “Idan muka sa wannan hadin gwiwa ya kasance mai amfani ta hanyar cika yarjejeniyar da muka yi, jama’armu za su amfana, ba a iya kanmu kadai ba har jikokinmu.”
Dangantakar dai ta fara ne daga wallafa labaran kasar sin a shafin “Daga Sin,” na LEADERSHIP Hausa wanda daga bisani aka samar masa da shafinna musamman q jaridar Hausa mai suna “Baban Bongo”.
Madam Nda-Isaiah ta kuma yaba wa gwamnatin kasar Sin bisa tsauraran ka’idoji da takunkumin da ta dauka kan yada labaran karya.
Ta bayyana cewa hakan zai magance rashin dacewar da wasu shafukan sada zumunta ke yi, da kuma dakile barazanar da labaran karya ke yi wa al’umma.
“Yana da kyau a samar da ka’idoji kan yada labaran karya don magance munanan illolinsa ga al’umma. Yana da kyau gwamnatin kasar Sin ta dauki nauyi,” in ji ta.
Ta kuma ba da tabbacin cewa LEADERSHIP za ta samu lokaci don kai wa CMG ziyara.
A nasa bangaren, Xiaoyu ya ce kofar CMG a bude take ga duk wani nau’in hadin gwiwa daga kamfanin LEADERSHIP, musamman kan kafafen yada labarai.
Ya kuma bayyana cewa, CMG za ta fadada shirye-shiryensa na horas da ma’aikatan LEADERSHIP don samun ci gaba a fannin aikinsu.