Connect with us

WASANNI

Luke Shaw Ba Zai Buga Wasan Manchester United Na Gaba Ba

Published

on

Rahotanni sun bayyana cewa dan wasan baya na Manchester United Luke Shaw ba zai buga wasan da kungiyar zata buga na gaba ba saboda raunin daya samu akansa sakamakon wata haduwa da sukayi da dan wasan Sipaniya Carbajal.

Dan wasan yasamu buguwa a tsakiyar kansa ne bayan wata arangama da dan wasan baya na Real Madrid da yake wakiltar Sipaniya a wasan da kasashen Ingila da Sipaniya suka fafata a ranar Asabar a filin wasa na Wembley dake birnin Landan.

Shaw yasamu matasalar ne bayan andawo daga hutun rabin lokaci a lokacin da kasar Ingila tasha kashi daci 2-1 kuma likitocin tawagar ta Ingila suka daukeshi sukayi waje dashi tare da na’rar taimakawa numfashi a  hancinsa.

“Ban taba ganin irin wannan tsautsayin ba mai hatsarin gaske sai dai kamar yadda likitoci suka bayyana duk da haka abin yazo da sauki kuma tun a ranar ya farfado yafara Magana da abokansa da kuma iyalansa” in ji kociyan Ingila Gareth Southgate

Ya ci gaba da cewa “Mun turashi yakoma kungiyarsa ta Manchester United domin ya ci gaba da karbar magani amma dole ba zai fara wasa ba sai bayan sati daya kamar yadda dokar duk wanda yasamu irin matsalar sa take”

Hakan yana nufin dan wasan ba zai buga wasan da kungiyar zata buga da Watford ba a karshen sati da kuma wasan da zata fafata na cin kofin zakarun turai da kungiyar Young Boys a ranar Laraba a satin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: