Dan majalisar dattawa mai wakiltar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya ce makiyan tsohon shugaba Goodluck Jonathan ne kadai za su zuga shi ya tsaya takarar shugabancin kasa a 2027.
Oshiomhole ya bayyana hakan ne yayin wata firan siyasa na gidan talabijin Channels.
- Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa
- Yadda Za A Magance Yawaitar Malaman Da Ba Su Cancanta Ba A Nijeriya – TRCN
Ya ce neman sake zabensa a shekarar 2027 na iya lalata martaban tsohon shugaban kasa, wanda cikin sauki jam’iyyar APC mai mulki za ta samu nasara a kansa.
“Ta yaya Jonathan zai zama barazana? Mun doke shi a baya lokacin da PDP take kan mulki.
“Idan mutum yana ganin cewa PDP ita ce kololuwar jam’iyya a Nijeriya, kuma ya sha kaye a lokacin da yake ganiyarsa, ina ganin sai makiyinsa ne kawai zai tilasta masa ya kara tsayawa takara a zaben 2027,” in ji shi.
Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa ya ce a yanzu haka Jonathan ya kasance dan siyasa mai daraja, yana mai cewa komawa fagen siyasa na iya rage masa kima da kuma zubar masa da darajar da yake da shi a idon duniya.
Ya jaddada cewa Jonathan ya samu damar nuna cewa mulki bai tsole masa ido ba, domin haka ne ya samu daraja a cikin harkokin siyasar Nijeriya, sake dawowa takara zai zubar masa da daraja.
Oshiomhole ya jaddada cewa, “Da zan iya ba shi shawara, zan cewa, ka ci gaba da rike matsayin. Ka yi mulki har na tsawon shekaru takwas, ba lallai ba ne ka sake yin mulki na shekara tara.”