A makon da ya gabata, mun fara kawo muku tattaunawa da marubuciya RUKAYYA IBRAHIM LAWAN, inda ta bayyana wa masu karatu irin kalubalen da ta fuskanta bayan fara rubutunta. To a wannan makon ma ta zayyano wasu abubuwan ciki har da magana mai daci da aka taba fada mata. Ga karashen tattaunawar tare da wakiliyarmu PRINCESS FATIMA ZARAH MAZADU kamar haka:
Wane labari ne ya fi baki wahala wajen rubutawa?
Zuwa yanzu dai wata Duniya ne ya fi ba ni wahala wurin rubuta shi kasancewar shi labarin gasa ne, gasar da take da dokoki da ka’idoji. Abin da ya sa ya fi ba ni wahala shi ne bincike, da zaben kalmomi. Kusan kowacce gaba ta labarin bincike ne ya gina ta ga shi rubutu ne da aka kirkire shi a dan takaitaccen lokaci.
Shin kin taba buga littafi?
Eh, na buga guda biyu Gidan Duhu da Wata Duniya. Ina saka ran buga wasu a gaba idan mai duka ya ara mini dama. Da a kwai gajerun labaraina da aka buga a littafan hadaka. Misali; ina da gajeren labari mai taken KASATA a Littafin Dukan Ruwa Ba ya hana Gwarje Amo na hadakar (daliban makarantar Hausa 2021) sai gajeren labari mai taken Wutar Kaiƙayi a littafin Daukar Jinka na hadakar (marubutan da labaransu suka yi zarra a gasar Dangiwa literary 2022).
Wane irin nasarori ki ka samu game da rubutu?
Nasarori kam sai dai na ce Alhamdulillah. Nasarar farko da na samu ita ce haduwa da mutanen da ko a mafarki ban yi zaton layin kaddarata zai sada ni fuska da fuska da su ba.
Sai nasarori bangaren gasa. A shekarar 2020 na yi nasar zuwa ta uku a gasar da kunyar jarumai writers ta saka. A 2021 na yi nasarar samun kai wa zagaye biyun karshe na gasar Majalisar marubuta. Duk dai a wannan shekarar labarina ya yi nasarar shiga cikin jerin labarai 25 da BBC suka fara fitarwa na gasar Hikayata. Na san wasu za su iya kallon hakan a ba nasara ba, amma a wurina nasara ce babba zuwa wannan matakin a shekarar farko da na jarraba shiga gasar. Sai shekarar 2022 na yi nasar karbar shaidar girmama daga hannun mai girma gwamnan jihar Katsina a taron gasar Dangiwa literary ta wannan shekarar.
Har ila yau a shekarar 2022 din na samu takardar girmamawa a zagayen kusa da karshe na gasar Aliyu Muhammad research Library (Gusau Institute). Ban fasa gwadawa ba, a shekarar 2023 na yi nasarar lashe kambun girmama (award) na 2 a gasar ta Gusau Institute. Duka dai a 2023 na samu certificate na shida (6th p) a gasar Hazaka writers Association. Wadannan kadan kenan daga cikin nasarorin dana samu silar rubutu.
Ya batun kalubale, shin akwai ko babu?
Akwai kalubalai da na fuskanta ga mutane lokacin da na fara rubutu, amma wanda ya fi tsaya mini a rai shi ne wanda aka ce mini duk marubuta ‘yanwuta ne. Sai kuma masu kallon marubuta a matsayin marasa aikin yi. A bangaren masu karatu kuwa kalubalen bai wuce wanda ke addabar ‘online writers’ ba wato karancin sharhi.
Ya kika dauki rubutu a wajenki?
Nishadi, hanyar isar da sako cikin sauki.
Mene ne burinki na gaba game da rubutu?
Burina na gaba bai wuce in zama sananniyar marubuciya wacce duniya za ta yi alfahari da irin rubuce-rubucena ko bayan shudewa ta ba.
Ko akwai wanda ya taba bata miki rai ko faranta miki game da rubutu?
Uhm! Idan ma akwai wanda ya bata mini rai game da rubutuna to na manta, amma su na yabo ba na mantawa. Nakan yi mamaki sosai kuma na ji farinciki a duk lokacin da na ga manyan marubuta suna yaba rubutuna da kuma masu yi mini kallon allon kwaikwayonsu a fagen rubutu. Yadda rubutuna ke yawan samun yabo a ta bangarorin da ban yi tsammani ba. Da kuma yadda rubutu ya yi silar haduwata da manyan mutane (sarki, gwamna, matsimakiyar gwamna, da ma wasu cikin masu rike da mukaman gwamnati) har yanzu ji nake kamar a mafarki ne hakan ta faru.
Bayan rubutu kina wata sana’ar ne?
Eh, bayan rubutu ina taba sana’ar gashe-gashe, sayar da kayan sanyi a cikin gida, ina taba aikin jaridar online. A takaice dai ni komai da ruwanki ce in dai zan iya abin.
Ta ya ki ke iya hada ayyukanki da kuma rubutunki?
Sana’a, rubutu, karatu kowanne yana da nasa lokacin, in dai ka yi wa kanka tsari mai kyau. Don haka wannan bai taba zame mini damuwa ba.
Kamar wane irin lokaci ki ka fi jin dadin yin rubutu?
Da dare, lokacin da sawu ya dauke nutsuwa ta sauko mini.
Me za ki ce da masu karanta labaranki?
Abin da zan ce musu shi ne sannun su da jimirin bibiyar rubutukana, Allah ya saka musu da alkhairi ya bar kauna. Ina matukar godiya da alfaharin kasancewar su tare da ni.
Gaida mutum biyar.
Sai dai mutum biyar sun yi karanci a gaisuwata don ko wadanda suka cancanci gaisuwar suna da tarin yawa, amma dai wadanda ba su ji sunan su ba su yi min afuwa duk kuna raina. Ina gaisuwa da fatan alkhairi zuwa ga; Yusuf Yahya Gumel, Bilkisu Muhammad Garkuwa, Jibril Adamu J. Rano, Maryama H, Fatima Sunusi Rabi’u.