Daga Rabiu Ali Indabawa
Kungiyar matasan Arewa, ‘Arewa Youth Consultatibe Forum’ ta bayyana ra’ayinta kan tsare Sanata Ali Ndume na JIhar Borno. Babbar Kotun Tarayya a Abuja ranar Litinin, 23 ga Nuwamba, ta ba da umarnin tsare Ndume bayan kasa gabatar da Abdulrasheed Maina – Kungiyar matasan Arewan ta ce ta yi mamakin yadda kotun ta bar Sanata Abaribe ya tafi bayan ya kasa gabatar da shugaban IPOB, Nnamdi Kanu a gaban kotu, Kungiyar tuntuba ta matasan Arewa (AYCF), ce ta yi Allah wadai da tsare sanatan mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, bisa yadda ya kasa gabatar da tsohon Shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina. Maina ya gudu daga beli akan almundahanar kudi Naira biliyan 2 kamar yadda kafofin yada labarai suka ruwaito.
Legit.ng ta ruwaito kungiyar ta ba da wata sanarwa ta bakin shugaban ta, Yerima Shettima, wanda ya ce kungiyar ta ce tsare Ndume saboda guduwar Maina daga beli, a matsayin rashin adalci. AYCF ta ce duk da bata karyata ko Maina ya aikata laifin da ake zargi ko a’a ba, ta ce bai kamata a saki Abaribe wanda ya tsayawa dan tawaye Nnamdi Kanu yana yawo a matsayin mai yanci ba.
Sanarwar ta ce: “Ba mu gane dalilin da ya sa, Sanata Abaribe, wanda ya tsayawa shugaban Biafra wanda aka bayyana al’amuran a matsayin ayyukan ta’addanci (kuma har yanzu suna gudana) kuma an gaza hukunta shi ba.