Connect with us

MANYAN LABARAI

Majalisar Dattawan APC A Zamfara Sun Ci Alwashin Sasanta ‘Yan Takara

Published

on

Majalisar Datawan jam’iyar APC ta jihar Zamfara, karkashin jagorancin Makaman Kauran Namoda, Alhaji Lawali Kaura, ya dau sun dau alwasun sasanta ‘yan ta kara dan ganin jam’iyar ta zamo tsintsiya madaurin ki daya.

Shugaban ya bayyana haka ne jim kadan bayan kaddamar da su da Gwamna Abdul’aziz Yari a fadar Gidan Gwamnati jihar Zamfara da ke Gusau.

Alhaji Lawali Makama.ya bayyana cewa, a matsayinsu na dattawa da a ka zabo su su jagoranci wannan majalisar, kuma kowacce karamar hukumar na da wakilai a ciki, za su yi iyaka kokarinsu na ganin sun hada kan jam’iyar APC ta zamo tsintsiya madaurin ki daya kuma yanzu haka za su fara ne da sasanta ‘yan takarar da su ka turje ,kuma suna da kyakkyawan zato ‘yan takarar zasu basu hadin kai.

Makaman Kauran ya kuma tabbatar wa alumar jihar Zamfara zasuyi Iya kokarin su wajan gain samarwa jam’iyar mafita da alumar jihar Zamfara. dan haka ya naimi hadinkan ‘yan jam’iyar ta APC.

Shima anasa jawabin Gwamna Abdul’aziz Yari, Abubakar ya bayyana cewa’ Wannan Majalisa ta Datawa bin umarnin uwar jam’iyar APC na kasa ne ta tanaimi a Samar da su kuma run a ranar zaben shugabani na jiha da ya gudana aka gabatar da su sai yau Allah ya bada ikon kaddamar da su .

Gwamna Yari ya kuma bayyana cewa ‘Wadannan Kwamitin Datawane na jihar Zamfara masu mutunci dan haka aikin su ba kan jam’iya kadai zai takaitaba harda ,kawo habyoyin cigaban alumar jihar ta Zamfara. Dan haka muna fatan za’abasu hadin kai wajan Samar wa jihar Zamfara mafita
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: