Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar Nasarawa, Yusuf Bello Aliyu, wanda kuma shi ne Mai Tsawatarwa na Ƴan Majalisar Marasa Rinjaye, na tsawon watanni uku bisa wani faifan bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, wanda ake zargin yana ɗauke da kalaman cin mutunci ga Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Dakatarwar ta biyo bayan amincewar majalisar da rahoton Kwamitin Ɗa’a da Ladabtarwa a zaman majalisar na ranar Laraba, ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Ismail Falgore.
Da yake gabatar da rahoton kwamitin, shugaban kwamitin, Garba Shehu Fammer, ya ce kwamitin ya gudanar da bincike kan zargin ne bayan da majalisar ta miƙa masa batun a ranar Litinin, 19 ga Oktoba, 2026, biyo bayan wani ƙuduri da ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar Minjibir, Abdulhamid Abdul, ya gabatar.
Fammer ya bayyana cewa kwamitin ya gayyaci Yusuf Bello Aliyu domin ya ba da bayaninsa kan zargin, sannan ya duba faifan bidiyon a matsayin wani ɓangare na binciken.
Ya ce duk da cewa ɗan majalisar ya musanta yin kalaman cin mutunci ga gwamnan, kwamitin ya gano cewa abin da hujjojin da aka gabatar suka nuna ya saɓa wa ƙa’idojin ɗa’a da mutuncin da ake buƙata daga mambobin majalisar.
Bisa sakamakon binciken, kwamitin ya ba da shawarar dakatar da ɗan majalisar daga shiga dukkan ayyukan majalisar na tsawon watanni uku, daga ranar Laraba, 21 ga Oktoba, 2026.
Haka kuma, kwamitin ya buƙaci ɗan majalisar ya rubuta takardar neman afuwa a hukumance ga majalisar, sannan ya bayyana a zaman majalisa domin karanta takardar neman afuwar.
Baya ga haka, kwamitin ya shawarci majalisar da ta yi la’akari da samar da dokar da za ta tsara yadda ake amfani da kafafen sada zumunta, tare da kare haƙƙoƙi da mutuncin al’ummar Jihar Kano.
Bayan nazari da amincewa da rahoton kwamitin, Kakakin Majalisar, Ismail Falgore, ya sanar da dakatar da Yusuf Bello Aliyu na tsawon watanni uku.
A zaman majalisar na ranar Litinin, ’yan majalisar sun amince da gudanar da bincike kan faifan bidiyon da ake zargin ya nuna Yusuf Bello Aliyu yana riƙe da wani zomo ta kunnuwansa, yayin da yake furta kalaman da aka ɗauka a matsayin rashin girmamawa ga gwamnan jihar.
A lokacin gabatar da ƙudurin neman binciken, Abdulhamid Abdul ya bayyana damuwarsa kan abin da ya ce ya shafi ɗabi’ar da ake sa ran zaɓaɓɓun wakilan jama’a su nuna. Ya kuma buƙaci majalisar ta gudanar da bincike tare da ɗaukar matakin ladabtarwa idan aka tabbatar da zargin.














