Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tabbatar da sunayen mutane shida da gwamnatin jihar ta gabatar domin naɗa su a matsayin sabbin kwamishinoni.
Mutanen sun haɗa da Air Commodore Salisu Yusha’u (mai ritaya), Ibrahim Namadi, Farfesa Sani Lawan, Muktar Ishaq Yakasai, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa da Idris Garba Mustapha.
Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini, ya ce waɗanda aka tantance sun cika dukkanin sharuɗan naɗa su kwamishinoni.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ce za ta sanar da ma’aikatun da za su yi aiki.
Yusha’u ya yi alƙawarin yin aiki tare da jami’an tsaro da al’ummar yankunan domin inganta tsaro da tabbatar da zaman lafiya a jihar.
A nasa ɓangaren, Farfesa Malumfashi ya jaddada muhimmancin bunƙasa ilimin kimiyya da fasaha da kuma harkokin kasuwanci.
Shi kuma tsohon Kwamishinan Lafiya da Muhalli, Aminu Tsanyawa, ya yi alƙawarin tallafa wa ƙoƙarin yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.














