Rundunar ’yansandan Jihar Katsina ta tabbatar da kashe fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, tare da abokinsa, Adamu Abubakar, a Ƙaramar Hukumar Dutsin-Ma ta jihar.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:30 na daren ranar Litinin, 26 ga watan Oktoba, 2026, a ƙofar gidan malamin da ke garin Dutsin-Ma, inda wasu mutane biyu ɗauke da makamai a kan babur suka buɗe musu wuta.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ’yansandan jihar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar, ya ce mutanen biyu sun samu raunukan harbin bindiga da suka yi sanadin mutuwarsu.
Sanarwar ta ce bayan samun labarin harin, jami’in ’yansanda na yankin Dutsin-Ma ya jagoranci tawagar jami’an tsaro zuwa wajen da lamarin ya faru.
An garzaya da waɗanda aka harba zuwa asibiti domin samun kulawar gaggawa, amma likita ya tabbatar da rasuwarsu.
’Yansanda sun fara bincike
Rundunar ’yansandan ta ce Kwamishinan ’Yansandan Jihar Katsina, CP Ali Umar Fage, ya bayar da umarnin tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin domin gano waɗanda suka kai harin da kuma kama su.
Ta ƙara da cewa an fara bincike domin gano yadda lamarin ya faru da kuma waɗanda ke da hannu a kisan.
Kwamishinan ’yansandan ya kuma miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, mabiyansu da al’ummar Dutsin-Ma bisa wannan babban rashi.
Ya tabbatar wa mazauna yankin cewa rundunar za ta ci gaba da ƙoƙarin ganin an kama waɗanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kotu.
Har yanzu ba a san waɗanda suka kashe su ba
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ’yansandan ba ta sanar da kama wani mutum da ake zargi da hannu a kisan ba.
Haka kuma, ba ta bayyana dalilin da ya sa aka kashe malamin da abokinsa ba.
Rahotanni sun nuna cewa Sheikh Masussuka ya kasance fitaccen malamin addinin Musulunci a yankin, wanda koyarwarsa ta sha haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin Musulmi.














