Sojojin rundunar Operation Fansan Yamma sun ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Sakaba ta Jihar Kebbi.
Waɗanda aka ceto su ne Aisha Aminu, mai shekaru 46, Sumayya Aminu, mai shekaru 27, da Nana Abbas, mai shekaru 15.
ADVERTISEMENT
An ceto su ne a ranar 24 ga watan Oktoba, 2026.
An gano biyu daga cikinsu a ƙauyen Makuku, yayin da aka ceto ɗayar a ƙauyen Dankolo.
Daga bisani, an miƙa mutanen hannun Dagacin Dirindaji, Usman Muhammad, ta hannun shugaban ƙaramar hukumar Sakaba.
Rundunar sojin ta ce an kammala aikin ba tare da wata matsala ba, tare da jaddada aniyarta ta kare rayuka da dukiyoyin al’umma.













