Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umarci tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da ya kare kansa kan zargin sa da yin kutse domin sauraron tattaunawa a wayar mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro, Nuhu Ribadu.
A ranar Litinin, Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta yi watsi da buƙatar El-Rufai na a sallame shi, inda ta ce masu gabatar da ƙara sun gabatar da isassun hujjojin da suka sa ya zama dole ya kare kansa.
Shari’ar ta samo asali ne daga wata hira da El-Rufai ya yi a gidan talabijin na Arise TV a watan Fabrairun 2026.
Ya ce shi da wasu sun yi kutse a wayar Ribadu kuma sun saurari tattaunawar da Ribadu ya yi.
Kotun ta ɗage shari’ar zuwa ranar 25 ga Nuwamban 2026, domin El-Rufai ya gabatar da kare kansa.














