Kungiyar Feyenoord ta kwashi kwallo 4 a gida a hannun Manchester City a wasan farko na rukuni na shida a gasar cin kofin Zakarun Turai da suka yi a ranar Laraba.
Manchester City ta ci kwallayen ta hannun John Stones wanda ya ci biyu sai Sergio Aguero da kuma Gabriel Jesus da kowanne ya ci daidai.
Shakhtar Donetsk wacce ke rukuni da Manchester City doke Napoli ta yi da ci 2-0, kuma Taison da kuma Facundo Ferreyra ne suka ci maata kwallayen.
City za ta karbi bakuncin Shakhtar Donetsk a ranar 26 ga watan Satumba, a kuma ranar ce Feyenoord Rotterdam za ta ziyarci Napoli.