Manyan ƴan siyasar da suka dunƙulr a ƙarƙashin ƙungiyar haɗin gwuiwa don tunkarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 ta janye daga shirin kafa sabuwar jam’iyya mai su a ADA, inda ta amince da African Democratic Congress (ADC) a matsayin jam’iyyar da zasu yi takara a zaɓen mai zuwa.
Mai magana da yawun haɗakar, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa wannan mataki ya fito ne bayan taron shugabannin jam’iyyu da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis. Ya ce ƙungiyar ta daina duk wani yunƙuri da ya shafi ADA, ko dai rajista ko akasin haka.
- INEC Ta Amince Da David Mark A Matsayin Shugaban ADC
- Wa’adin Mulki Ɗaya Kacal Za Ka Yi — ADC Ga Tinubu
A taron, shugaban jam’iyyar ADC, David Mark, da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, tare da fitattun ‘yan siyasa irin su Mallam Nasir El-Rufai, da Sanata Aminu Tambuwal, da Rotimi Amaechi sun halarta. Jam’iyyar ADC ta kuma buƙaci mambobinta da ke cikin sauran jam’iyyu, ciki har da Peter Obi (LP), El-Rufai (SDP), da Tambuwal (PDP), da su ajiye muƙamansu su koma cikakkun ƴan ADC.
Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa dukkan ƴan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin ADC sun amince da yin aiki tare, tare da goyon bayan duk wanda ya yi nasara a zaɓen fidda gwanin da za a gudanar. Abdullahi ya ce kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) zai sanar da jadawalin zaɓen fidda gwani a Osun da Ekiti nan ba da jimawa ba, kafin zaɓukan jihohin biyu.
Da wannan sabon tsarin, masana harkokin siyasa na ganin cewa ADC na iya zama babban jam’iyyar adawa a 2027, idan aka tabbatar da haɗin kai tsakanin manyan ƴan siyasa da jam’iyyu daban-daban da suka shiga haɗakar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp