Mun yi maraba da ware wa mata kashi 35 cikin 100 na daukar ma’aikata a Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida da suka hada da jami’an tsaron (NSCDC) da Hukumar Kashe Gobara Ta Tarayya, da Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa, da kuma Hukumar Kula da Gyaran Hali ta Kasa.
Wannan ba karamin taimaka wa mata aka yi ba wajen basu gurbin wani kaso na aikin tsaro, saboda da yawa mata suna fama da rashi aiki yi sun gama makaranta babu aikin yi babu aure, sannan kuma babu sana’ar yi sun zama kamar zauna gari banza saboda babu abin da mutum yake yi, wata ma tana son fara sana’a amma babu kudin da za ta yi sana’a.
- Ina Rubutu A Kan Rayuwar Yau Da Kullum Domin Mutane Su Wa’azantu – Fatima Sunusi
- Xi Ya Bukaci Sin Da Faransa Su Hada Hannu Wajen Bude Hanyar Zaman Lafiya Da Ci Gaba Domin Kyautata Rayuwar Bil Adama
Lalle wannan ba karamin taimaka wa mata wadanda ba sa aiki aka yi ba, saboda za su samu abin yi sannan kuma za su samu abin da za su rika rufa wa kansu asiri kila har su taimakawa wani.
Sannan zai rage musu yawace-yawace da shiririta da zaman rashi aikin yi da yawan gulmace-gulmace duk wadannan zai rage dama rashin aikin yi ne yake kawo su. Sannan kuma mata za su ci gaba da samun karfin gwiwar yin karatu saboda sun san idan sun gama za su samu aiki, domin rashin aikin yi ba karamin kashe wa mutum gwiwa yake ba, mutum zai sha wahalar karatu, kudin makaranta, kudin takardun karatu da ‘yan cemi-cemi, sannan kuma mutum ya gama babu aiki wannan bakaramin wahala ake ba.
Mata na fuskanta kalubale wajen daukar su aiki za ku ga mata suna yawon neman aiki amma kuma ba sa samu wasu ma a yi ta musu wasa da hankali, wasu ma idan suka hadu da mutumin banza ya nemi ya bata musu rayuwa sai a ce sai mace ta yarda da shi sannan ya bata aiki, to gaskiya wannan ba karamin kalubale bane a ce sai mace ta rasa mutuncinta sannan a bata aiki, wata kuma tana samun kalubale ne daga wajen mijinta wasu mazajen suna hana mata aiki, ko kuma idan an barta ta yi aikin za su rika samun matsala, wasu kuma dama suke dauke da dauyin kansu, wasu kuma mazajen suna sa musu idon akan abin da suka samu.
Wannan shi ne kalubalen da mata suke fukanta a harkar aiki. Don haka yana da kyau mata mu ci moriyar aikinmu ta hanyar rike aikinmu tsakaninmu da Allah babu cuta babu cutarwa ina ganin idan muka tsarkake zuciyarmu za mu ci moriyar abin bamu kadai ba har da ma wasunmu.
Yana da kyau mata mu kiyaye mutuncimmu sannan kuma mu kama kammu, ki sani ke mace ce a wajen aiki da yawan mazaje abin da ya sa suke hana matansu aiki kenan saboda rashin kamun kai, mata mu yi kokarin kiyaye kanmu sai ki ga an yi kokarin kiyaye hakkin ki a wajen aiki.