Mamba a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, Dakta Don Pedro Obaseki ya bayyana cewa ministan Abuja kuma tsohon gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya ketare iyaka na kiran a dakatar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Idan za a iya tunawa a wata tattaunawa da aka yi da Wike a gidan talabijin na Channels a shirin siyasa a yau, ya bayyana cewa, “Duba da wuraren da PDP ta yi rashin nasara saboda girman kai da kwadayi da kuma rashin adalci. Idan da PDP ta yi abin da ya kamata ta yi, to da ba wannan maganan ake ba a yanzu.
“Ya kamata a ce an yi adalci, wanda hakan ya sa nake kira da kwamitin gudanar-wa na jam’iyyar ya dakatar da dan takarar shugaban kasa da sauran wasu mutane kamar irin su Aminu Tambuwal domin sake gina jam’iyyar PDP.”
Sai dai da yake mayar da martani a gaban ‘yan jarida a Abuja, Obaseki ya ce jiga-jigan jam’iyya mai mulki ta APC su shirya amsar cin amana daga wurin Wike, inda ya ce PDP ba za ta iya ci gaba da lamuntar duk wani cin kashi daga hannun Wike ba.
Ya ce, “Shi ne mafic in amanan jam’iyyar a tarihin siyasarmu. Ya raba gari da Ro-timi Amaechi da Goodluck Jonathan da Peter Odili da Atiku Abubakar, inda a yan-zu yake tare da Bola Tinubu.
“Wike ya fito fili ya bukaci a dakatar da shugaban jam’iyyarmu na kasa kuma dan takarar shugaban kasa na tutar jam’iyyar, wanda ‘yan Nijeriya suka amshe shi hannu bibiyu kamar yadda INEC ta gabatar da cewa mun lashe jihohi 21, sannan har ya nemi a dakatar da Atiku daga jam’iyyar, lallai Wike ya ketare iya a halin yanzu, ya kamata ya shirya yaki.
“Yana da kudin da zai iya yaki da mu, saboda muna zuwa gare shi kamar runduna. Na tabbata Wike ya karaci fannin shari’a. Na tabbata shi lauya ne kuma ya san cewa duk mai shirin zaman lafiya dole ya shirya wa yaki.
“Nyesom Wike ya tabo tsuliyar dodo, ya jira ya ga abin da zai same shi. Shawarar kawai da zan bayar ita ce, wadanda suka hada baki da shi suka ci amana wajen yi wa APC aiki, su jira karshensu.”