Rundunar ‘yan sandar jihar Edo ta samu nasarar cafke mutum bakwai bisa zargin su da buga kudin jabu na Nijeriya. Wadanda ake zargi dai sun hada da mata guda biyu sai maza guda biyar, an dai cafke su ne a gurare daban-daban a garin Benin ciki har da kan titin Sakponba da kuma New Benin. Da yake gabatar da wadanda ake zargi a shalkwan ‘yan sanda, kwamishinan ‘yan sanda Mista Johnson Kokumo ya bayyana cewa, an samu sama da naira miliyan 12.8 daga hannun wadanda ake zargi. Kokumo ya kara da cewa, rundunar za ta binciki wani ma’aikacin banki wanda aka aikata wannan laifi tare da shi. Ya bayyana sunayensu kamar haka; Franklin Izukwu, Bright Mugbeyoghe, Obi Aled, Elbis Iyomana, Osazee Osagede, Bictoria Igbinos da kuma Deborah Uwa. Kwamishinan ya kuma bayyana umurnin da shugansu ya baiwa rundunar ‘yan sanda a kan masu buga kudin jabun Nijeriya, kamar dai yadda yake a cikin sashi na 20 da kuma na 21 na dokar babban bankin Nijeriya mai lamba ta 7 ta shekarar 2007, ta samar da cewa duk wanda aka kama yana buga kudin jabu to za a daure shi a gidan koso na tsawon watanni shida da kuma tarar kudi naira 50,000 ko kuma fiye da haka.
“Domin cika wannan umurni dai, a ranar 8 ga watan Nuwamba ta shekarar 2018, rundunar ‘yan sandar jihar Edo tare da jami’an tsaro na farin kaya da kuma hadin gwaiwar babban bankin Nijeriya reshen Benin sun hada kai domin hukunta wannan masu buga kudin jabu.“Wadannan masu buga kudin jabu suna aikata wannan laifine kafin asirinsu ya tonu,” inji shi.
Daya daga cikin wadanda ake zargi mai suna Izukwu ya bayya wa manema labarai cewa, ya kai tsawan shekara biyar a cikin wannan haramtacciyar kasuwanci. A ciwarsa, takardar naira 200 da kuma na 100 ya saye su ne a wasu bankuna da ke Legas da Abuja, sannan aka nannade su kamar jarida aka kawo su Benin, yayin da sauran kudin takardan ya saye su ne a Benin. Wanda ake zargin mai shekaru 25 ya kara da cewa,“a wasu lokuta, kudin suna zuwa ne dunkule. Ba ma amsarsu sai da rakiyar ‘yan sanda. Ana shirya su ne a cikin kwali kamar jarida.”
Kokumo ya bayyana cewa, za a mika wadanda ake zargi zuwa kotu idan an kammala bincike. Sannan kuma ya gargadi wadanda ke aikata haramtacciyar kasuwanci a kan su dai na aikata laifin.