ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, November 13, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Masu Sayar Da Abinci Da Tsada, A Ji Tsoron Allah

by Ibrahim Bala and Sulaiman
10 months ago
Abinci

Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta’ala Wa Barakatuhu.

Jama’a barkanmu da kasancewa tare da wannan fili mai albarka, filin da yake zakulo batutuwan da suke ci mana tuwo a kwarya.

A wannan gabar zan yi wani dan tsokaci ko nace tuni ko kuma jan hankali, musamman game da masu siyar da kayan abinci na cikin lunguna ko na shaguna.

ADVERTISEMENT

Idan muka yi duba da ‘yan watannin nan cikin lokutan nan, za mu ga cewa kayan abinci suna yin sauki kuma suna karyewa, sai dai wani hanzari ba gudu ba masu dafa abinci su siyar suna siyar wa da tsada ba tare da sun kara mudu ba, ma’ana; ba sa yin aunin daidai yadda ya kamata.

Ya ilahil’alamina yaushe rayuwa za ta yi daidai, abu na farko dai tauye mudu haramun ne, domin Manzon Allah (SAW) a hadisansa ingantattu ya yi magana sosai akan irin azabar da wadannan mutanen za su sha a ranar gobe alkiyama.

LABARAI MASU NASABA

A Duba Halin Da Masu Buƙata Ta Musamman Ke Ciki

Falalar Goman Farko Na Zul-hajji 

Ya kamata masu auna mudu su rika aunawa daidai misali, kuma ha’inci ne idan ka tauye mudu ko ka rage yadda ake auna mudu, ranar gobe alkiyama za ka biya, kuma za ka fuskanci hukuncin ubangiji.

Haka mutanen da suke siyo danyan abinci a saukake, sai su siyar da shi da tsada su zuga masa kudi ko da kuwa ya sakko dan kawai su ci riba, wannan ba riba bace ribau ce, kuma shi ma haramun ne. Ya kamata mu ji tsoron Allah, tsadar abinci ma musifa ne.

Akwai masu shaguna na lungu da sako wasu wuraren ba sa saukaka wannan al’amarin ko kadan, ya kamata dai mu duba. Idan ka tausaya sai Allah kai ma ya tausaya maka, ba sai kayi tsada za ka yi kudi ba, ba a yin arziki a haka, idan ka tausaya sai Allah ya  kalli zuciyarka.

Ina kara jan hankalin mutane musamman masu aikata hakan, da masu sha’awar yin hakan, dan Allah a tausaya a wannan bangare na siyan abinci, idan ka samu a sauki kai ma sai ka siyarwa al’umma a saukake su samu sauki, idan farashi ne ya dagu kai ma sai ka daga.

Amma sai a ga kayan abinci ya sakko, masu dafa abincin siyarwa awon bai ragu ba kuma bai karu ba, sun kara masa kudi, ai ya kamata ace tunda abinci ya sakko suma a wajensu abun yayi sauki. Da yawa wuraren da ake siyar da abinci haka suke, sun kara kudin kuma sun ki kara awon da suke na abincin, wannan zalumci ne, kuma babu kyau, rashin tausayi ne.

Idan ka tausaya Allah zai tausaya maka, ba kullum ka rika zagin shuwagabanni ba, abinci ya sakko kai ba za ka sakko da naka ba. Jama’a duk sai mun ji tsoron Allah, mu kyautata sai mu ga daidai, Allah ya sa mu dace.

Abinci
Ibrahim Bala
+ posts Bio
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    A Duba Halin Da Masu Buƙata Ta Musamman Ke Ciki
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    Matsalar Ƙwacen Waya: Ina Mafita?
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    Falalar Goman Farko Na Zul-hajji 
Abinci
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Da Amurka Na Wanzar Da Tuntuba Da Nufin Ragewa Juna Harajin Fito Da Bunkasa Cinikayya Da Zuba Jari
  • Sulaiman
    Yawan Mutane Shi Ne Kasuwa…
  • Sulaiman
    Gwamnan Zamfara Ya Yi Ta’aziyyar Kwamishinan Kasuwanci, Tasiu Shinkafi
  • Sulaiman
    Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Yi Tattaunawa Mai Alfanu Ta Wayar Tarho Da Rubio Kan Alakar Sin Da Amurka

MASU ALAKA

A Duba Halin Da Masu Buƙata Ta Musamman Ke Ciki
Marurun Zuciya

A Duba Halin Da Masu Buƙata Ta Musamman Ke Ciki

June 20, 2026
Laifukan Intanet: Kotun Abuja Ta Karɓi Rahoton DSS, Ta Ba Da Belin Wani Ɗan Gwagwarmaya
Marurun Zuciya

Falalar Goman Farko Na Zul-hajji 

May 23, 2026
marayu
Marurun Zuciya

Bukatar Kulawa Da Marayu Da Masu Karamin Karfi

May 17, 2026
Next Post
AFCON 2025: Hukumar CAF Ta Sauya Alƙalin Da Zai Jagoranci Wasan Nijeriya Da Algeria

AFCON 2025: Hukumar CAF Ta Sauya Alƙalin Da Zai Jagoranci Wasan Nijeriya Da Algeria

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Tuntuba Da Nufin Ragewa Juna Harajin Fito Da Bunkasa Cinikayya Da Zuba Jari

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Tuntuba Da Nufin Ragewa Juna Harajin Fito Da Bunkasa Cinikayya Da Zuba Jari

November 12, 2026
Ƙungiya Ta Fara Horas Da Mata Kan Yadda Ake Kaɗa Ingantacciyar Ƙuri’a Domin Kauce Wa  Lalacewarta

Ƙungiya Ta Fara Horas Da Mata Kan Yadda Ake Kaɗa Ingantacciyar Ƙuri’a Domin Kauce Wa Lalacewarta

November 12, 2026
Yawan Mutane Shi Ne Kasuwa…

Yawan Mutane Shi Ne Kasuwa…

November 12, 2026
Shehu ABG Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gwamna A Kaduna

Shehu ABG Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gwamna A Kaduna

November 12, 2026
Gwamnan Zamfara Ya Yi Ta’aziyyar Kwamishinan Kasuwanci, Tasiu Shinkafi

Gwamnan Zamfara Ya Yi Ta’aziyyar Kwamishinan Kasuwanci, Tasiu Shinkafi

November 12, 2026
Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Yi Tattaunawa Mai Alfanu Ta Wayar Tarho Da Rubio Kan Alakar Sin Da Amurka

Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Yi Tattaunawa Mai Alfanu Ta Wayar Tarho Da Rubio Kan Alakar Sin Da Amurka

November 12, 2026
Duniya Ta Fahimci “Damarmakin Sin Na 2.0” Daga Bikin CIIE

Duniya Ta Fahimci “Damarmakin Sin Na 2.0” Daga Bikin CIIE

November 12, 2026
Kasar Sin Ta Bayyana Goyon Baya Ga Shirin Gargadin Wuri Ga Kowa Na MDD

Kasar Sin Ta Bayyana Goyon Baya Ga Shirin Gargadin Wuri Ga Kowa Na MDD

November 12, 2026
Sojoji Sun Kashe Ɗan Ta’adda, Sun Kama Uba Da Ɗansa A Katsina Da Sakkwato

Sojoji Sun Kashe Ɗan Ta’adda, Sun Kama Uba Da Ɗansa A Katsina Da Sakkwato

November 12, 2026
Mataimakin Shugaban Kasar Sin Ya Halarci Babban Taron Shugabannin Kasashe Kan Sauyin Yanayi COP31 Da Ake Gudanarwa a Antalya

Mataimakin Shugaban Kasar Sin Ya Halarci Babban Taron Shugabannin Kasashe Kan Sauyin Yanayi COP31 Da Ake Gudanarwa a Antalya

November 12, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.