ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

by Ibrahim Bala
2 months ago
Zawarawa

Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta’ala Wa Barakatuhu. Jama’a barkanmu da sake kasancewa tare da wannan fili mai albarka,

wanda yake zaƙulo muku batutuwan da suke ci mana tuwo a ƙwarya, musamman a wannan zamani da muke ciki.

A daidai wannan lokaci, zan yi magana ne a kan aure, idan muka yi duba za mu ga cewa; a Arewacin Nijeriya ne aka fi samun mace-macen aure, amma kusan na ce mutanenmu hankalinsu bai kawo kai ba, mene ne ya sa?

ADVERTISEMENT

Mene ne kuma dalili?

Magana ta gaskiya matsala ɗaya ce zuwa biyu ko uku, na farko akwai laifin iyaye, na biyu akwai laifin samari da suke zuwa su yi auren, na uku kuma akwai laifin amaryar wacce ita ce take zaman auren.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Bari na fara da maganar farko, dalilin da ya sa na ce laifin iyaye ne shi ne; duk mutumin da ya zo zai auri ƴarka, idan kana da ƴa ta isa aure, ya kamata ka zaunar da shi ka tambaye shi; mene ne ma auren, kuma me yasa yake son ya auri ƴar taka? Da yawan samarin da suke yin aure, ba su san ma mene ne auren ba.

Alal haƙiƙanin gaskiya, sha’awa ce kawai take tunzura su; a tunanin samari jima’i kawai shi ne aure, wannan shi yake kawo mace-macen aure ka ga namiji ya saki mace cikin sauƙi. Domin idan don sha’awa ka yi, da zarar ka gusar da sha’awarka za ka ji to, ai ba ka da kuma wata buƙata a wajenta.

Don haka, yana da kyau ka tambayi wanda ya zo neman auren ƴarka cewa; mene ne ma auren? a nan za ka gane ko yana da addini ko kuma ba shi da shi, ya san mene ne ma auren ko bai sani ba, shin ya san aure sunnah ce ta Ma’aiki ko ma bai sani ba?

Ba fa jima’i ne kawai aure ba, wani sha’awa ce, ruɗu ne kawai tana da kyau, ta iya kwalliya da dai sauransu, shikenan da an yi auren kuma ya ga ta zo ta yi wanka ta yi kaza, ya ga ta tashi daga barci, ya zo ya same ta ba wanka, sai ya ga kamar ba waccan ba ce, to ya kamata ya san ma mene ne auren tukunna.

Ba laifi ba ne, kuma ba abin kunya ba ne, ka sanar da shi kai da shi, domin burinka idan ya auri ƴarka su zauna har abadan da’iman mutu-ka-raba, ba kawai a yi rawar ƙafa ba. Ah! kawai shikkenan yarinyar nan duk ƙannenta sun yi aure ga wani ya fito kawai sai a ce turo iyayenka, saboda me, waye shi, mene ne matakin iliminsa, me ya sani, me ya sani dangane da auren?

Sannan ku zaunar da ƴarku, ku sanar da ita mene ne aure, da kike ta rawar ƙafa za ki auri wane, me ya sa kike sonsa? Don haka, ga abin da addini ya shara’anta, ga abin da ya kamata ki yi idan kina son ki zauna lafiya, ga kuma yadda ya kamata ki yi.

Neman kai kake da ƴarka? lokacin da ka yi aure ka haife ta har ta yi laulayi aka goya ta, ta tashi ta fara rarrafe, ka raine ta, makaranta safe, rana da kuma dare, ka kai ta ka ɗauko ta, duk ba ka yi neman kai da ita ba sai da aka zo ɗan taƙi na ƴan shekaru kawai da wani yake so, kake son ya aure ta sai ka yi ta gaggawa?

Duk mace a duniya Allah ya rubuta mata mijinta, amma dolenmu sai mun tsaya mun miƙa wa Allah lamarinmu, ba lallai sai maikuɗi za ki aura ki zauna lafiya ba, Hajiya ki nemi mai rufin asiri, wanda za ku zauna lafiya ya rufa miki asiri ya ga mutuncin iyayenki, ya kare ki, ya kare mutuncinki, ya kuma kare addininki.

Sannan su ma na dawo kan su samarin masu yin aure, sha’awa ce take sa wa da yawa muke yin aure, ko kuma tana burge ni, ko abokina ya auri wata kyakkyawa fara ƙal ni ma ƙal zan aura a ce shege wane ya auri wance, “Kai! ka ga matar wane?”, wa ya aike ka Alaji duk ga abin da Annabin tsira ya karanto ka kalli wannan suffofin shin tana daga ciki?

Amma ba ma bi, muna ɗauka ne kawai mai kyau ce, ta iya wanka, ta iya girki, “kai! ka ga idan ta yi wanka, ai idan na auri wannan ai na kece a cikin abokanai”, wa ya faɗa maka? ba wannan ba ne Alaji.

Alaji ka yi aure kai kwanciyar hankali, ka bi abin da addini ya ce da abin da ma’aiki (SAW) ya faɗa, ga irin tsarin duk ya zayyano mana siffofi.

Idan za ka auri mace, kar ka yi mata ƙarya, ku yi gaskiya da gaskiya, kuma ka sanar da ita ga irin zaman da kake so ku yi tun kuna waje, yadda idan ta shiga ma ba za ta ga ka yi mata ƙarya ba, Alaji wallahi idan ka yi ƙarya ma ba za ka ga daidai a gidanka ba, ka yi iya bakin ikonka kar ka kwaikwayi rayuwar wani ka yi iya irin taka wacce ba ta kaucewa al’ada da addininmu na musulunci ba.

Idan muna so a rage zawarawa da mace-macen aure, to kafin auren sai mu riƙa kiyayewa da sanin me ya kamata mu yi.

Wassalamu Alaikum.

Zawarawa
Ibrahim Bala
+ postsBio
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    A Duba Halin Da Masu Buƙata Ta Musamman Ke Ciki
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    Matsalar Ƙwacen Waya: Ina Mafita?
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    Falalar Goman Farko Na Zul-hajji 
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    Bukatar Kulawa Da Marayu Da Masu Karamin Karfi

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Jam’iyyar PDP Ce Za Ta Dawo Da Kwanciyar Hankali A Nijeriya – Hajiya Khadija

Jam'iyyar PDP Ce Za Ta Dawo Da Kwanciyar Hankali A Nijeriya - Hajiya Khadija

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.