ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Falalar Goman Farko Na Zul-hajji 

by Ibrahim Bala
4 months ago

Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta’ala Wa Barakatuhu. Jama’a barkanmu da wannan lokaci, barkanmu da sake kasancewa a wannan fili mai albarka. A wannan mako zan yi magana a kan falalar goman ƙarshe na Zulhajji.

Hadisi ne daga Ibn Abbas (RA) ya ce, “Annabi (s.a.w) ya ce, ranar ɗaya ga watan Zulhajji ita ce rana da Allah (SWT) ya gafartawa Annabi Adam  (AS). Wanda ya azumci wannan rana Allah (SWT) zai gafarta masa kowane irin zunubi ne tsakaninsa da shi, domin Allah shi ne me yafe zunubi ba kowa ba.

Rana ta biyu ga Zulhajji ita ce ranar da Allah (SWT) ya karɓi addu’ar Yunusa (AS) ya fitar da shi daga cikin kifin da ya haɗiye shi. Wanda ya azumci wannan ranar yana da lada kwatankwacin wanda ya raya shekara da ibada. Haƙiƙa Allah (SWT) yanata kaho mana ranaku da lokuta da za mu yi abubuwa da zai kankare zunuban da muke yawan aikatawa.

ADVERTISEMENT

Rana ta uku malamai suka ce ga Zulhajji, rana ce da Allah (SWT) ya karɓi addu’ar Annabi Zakariyya (AS) ya bashi haihuwa, duk wanda ya azumci wannan rana Allah ubangiji (SWT) zai karɓi addu’o’insa.

Rana ta huɗu ga Zulhajji ita ce, ranar da aka haifi Annabi Isah (AS), duk wanda ya azumci wannan rana Allah zai kare shi daga talauci da kuma musiba. Wannan musubu da suke yawan faruwa ka rasa ta kai ta ƙafa, ta ko’ina to, ire-iren waɗannan abubuwa sai ka ga Allah ya tsallakar da kai ko da musulmi za ta shafarwa.

LABARAI MASU NASABA

A Duba Halin Da Masu Buƙata Ta Musamman Ke Ciki

Bukatar Kulawa Da Marayu Da Masu Karamin Karfi

Rana ta biyar ga Zulhajji ita ce ranar da aka haifi Annabi Musa (AS), duk wanda ya azumci wannan rana Allah (SWT) zai kare shi daga munafurci ko azabar kabari.

Rana ta shida ga Zulhajji ita ce ranar da Allah (SWT) ya yi buɗin alkhairi ga Annabi (SAW) fiyayyen halitta, wanda ya azumci wannan rana Allah zai dube shi da rahma kuma ba zai azabtar da shi ba. Allah gafurul rahim.

Rana ta bakwai ga Zulhajji ita ce ranar da Allah (SWT) zai sa a rufe ƙofofin wuta ba za a buɗe su ba, har sai waɗannan kwanaki goma sun wuce. Duk wanda ya azumci wannan rana Allah zai rufe masa ƙofofi talati na tsananin ratuwarsa, ya buɗe masa ƙofofi talatin na sauƙi. Kai! Allah ya sa mu dace.

Rana ta takwas ga Zulhajji ita ce, ranar da Allah (SWT), ranar da ake cewa ranar tarayya. Duk wanda ya azumci wannan rana babu wanda ya san adadinsa sai Allah.

Rana ta tara kuma ga Zulhajji ita ce, ranar hawan arfa, Allah yana gafartawa dukkan alhazan dake gurin arfa, wanda kuma ba ya gurin aikin idan ya azumci wannan rana Allah yana gafarta masa zunubansa na shekarar da ta gabata da kuma shekrar da take tafe.

Ranar goma ga wata kuma ita ce, ranar layya, ga wanda Allah ya horewa abin da zai yi layya, idan ya yanka dabbarsa ɗigon jini na farko da zai fara ɗiga a ƙasa zai zama gafara gare shi da iyalansa. An so wanda zai yi layya da wanda ba zai yi ba ya kama bakinsa har sai bayan an dawo daga sallar idi ya ci abinci ko wani abu daga cikin layyarsa, Allah zai bashi lada wacce ta fi dutsen Uhud girma da nauyi. Kuma ana so ya raba namansa kashi uku. Kashi na farko sadaka, kashi na biyu kyauta, kashi na uku kuma domin iyalai.

Allah ya bamu ikon azumtar wannan ranaku, ya kuma bamu ikon samun wannan falala. Al’umma muna fatan za a riƙa amfani da wannan tunatarwa domin an riga an san tunasarwa ce. Allah ubangiji ya bamu wannan lada, Allah ya sada mu da alkhairan dake ciki, Allah ka haɗa kanmu, Allah shugabanni Allah ka shirye su, wanda ba za su shiryu ba Allah ka canza mana su ka bamu waɗanda suka fi alkhairi. Allah shugabanni duk wanda muke so, da wanda ba ma so indai alkhairi ne Allah ka tabbatar mana da shi ka zaɓa mana shi, domin Allah ka fi mu sanin daidai, ka fi mu sanin wanda ya dace da mu.

Ibrahim Bala
+ postsBio
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    A Duba Halin Da Masu Buƙata Ta Musamman Ke Ciki
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    Matsalar Ƙwacen Waya: Ina Mafita?
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    Bukatar Kulawa Da Marayu Da Masu Karamin Karfi

MASU ALAKA

A Duba Halin Da Masu Buƙata Ta Musamman Ke Ciki
Marurun Zuciya

A Duba Halin Da Masu Buƙata Ta Musamman Ke Ciki

June 20, 2026
marayu
Marurun Zuciya

Bukatar Kulawa Da Marayu Da Masu Karamin Karfi

May 17, 2026
Abincin Da Ya Kamata Ku Ci Lokacin Al’ada
Marurun Zuciya

2027: Bukatar Zaben Shugabanni Na Gari

May 10, 2026
Next Post
Alkalin Babbar Kotun Tarayya Ya Rasu Bayan Faɗuwa A Gidansa A Kano

Alkalin Babbar Kotun Tarayya Ya Rasu Bayan Faɗuwa A Gidansa A Kano

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.