ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, July 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

A Duba Halin Da Masu Buƙata Ta Musamman Ke Ciki

by Ibrahim Bala and Sulaiman
3 weeks ago
Hali

A wani ƙiyasi na Majalisar Ɗinkin Duniya an bayyana cewa akwai kimanin mutane Biliyan ɗaya a duniya wato kashi 15 cikin ɗari na mutanen duniya na da nakasa a wani sashi na jikinsu, sai dai ba dukkan su ne ke bara ko gararamba a titi ba, akasarinsu na da rayuwar da suka dogara da ita ko ayyukan da suke yi na moriya. Kamar yadda wata ƙididdiga ta nuna cewa a Nijeriya akwai kimanin kashi bakwai cikin ɗari na yara da shekarunsu suka wuce biyar, da kuma kashi tara cikin ɗari na manya da shekarunsu suka wuce 60 waɗanda ke rayuwa cikin ƙunci da tagayyara saboda wata nakasa da suke fama da ita.

Kodayake a shekarar 2018 gwamnatin Nijeriya ta kafa wata doka da ta haramta nuna wa nakasassu, masu buƙata ta musamman, wariya da ƙyama, amma duk da haka ba ta canza zani ba. A mu’amala ta yau da gobe, a makarantu da wuraren ayyuka, wani lokaci har ma a wuraren ibada. Akwai wasu abubuwa da dama da ake ganin bai dace a ga mai nakasa a wajen ba, ko kuma shi matsayinsa bai dace da wajen ba!

Muhammad Hussaini Yakubu, wani matashi ne da ya fuskanci wani ƙalubale na janye sunansa cikin wasu ɗalibai ƴan asalin Jihar Bauchi wanda gwamnatin baya ta yi wa alƙawarin ba su aiki, da zarar sun kammala karatunsu na digiri da suke yi a bangaren kimiyya da fasaha. Amma bayan ya samu wani tsautsayi a ɗakin binciken kimiyya na jami’ar da yake karatu, wanda a dalilin haka idanunsa suka tsiyaye, ya zama makaho, sai ya canza fannin karatun da yake yi zuwa sashin nazarin aikin jarida. Wannan ya jawo aka janye batun aikin da aka yi masa alƙawari, wanda a baya har ana biyansa wani alawus daga tallafin karatun da gwamnati take ba su. Rayuwa ta yi wa Muhammad ƙunci sosai, karatun ma ya nemi ya gagara, saboda ga lalurar makanta kuma ga rashin tallafin da zai biya kuɗin makaranta.

ADVERTISEMENT

Kodayake bayan sanya baki da taimakon wasu ƴan’uwa an samu dai sabuwar gwamnatin Jihar Bauchi ta dawo masa da alƙawarin aikinsa, kuma har ya kammala karatun da yake yi. Amma ba kowa ne yake samun irin wannan gata ba, matasa da dama ba sa samun aikin yi, saboda wata nakasa da suke da ita, ana ganin ba za su iya ba. A dalilin haka da dama ke faɗawa mugun hannu, ko su shiga aikata munanan ayyuka, irinsu barace-barace, shaye-shaye, da wasu ayyukan da basu dace ba.

Ƙoƙarin da Gwamnonin wasu jihohi suka yi na kafa hukumomin kula da haƙƙoƙin nakasassu da sanya wasu masu iliminsu cikin harkokin gwamnati, ya taimaka wajen ɗaga darajar su da ƙara ba su bakin magana, a inda suka ga ana nuna musu wariya da bambanci. Kodayake wasu daga cikin mambobin waɗannan hukumomi na kokawa da rashin ba su muhimmancin da ya kamata daga bangaren gwamnati.

LABARAI MASU NASABA

Falalar Goman Farko Na Zul-hajji 

Bukatar Kulawa Da Marayu Da Masu Karamin Karfi

Na so in ji daga bakin Babban Sakataren Hukumar Kula da Nakasassu ta Ƙasa, James Lalu, dangane da abin da hukumar sa ke yi wajen isar da koke-koken masu buƙata ta musamman da a lokuta da dama suke ƙorafin ana hana musu damar cin wata moriya ta gwamnati a matsayinsu na ƴan ƙasa, duk da ilimi ko cancantar da suke da ita. Amma har kawo lokacin haɗa wannan rubutu bai waiwayi saƙona ba, duk kuwa da amsa min da ya yi na cewa ya ga saƙona.

Muna kira ga hukumomin gwamnati su ƙara sa ido kan yadda ake watsi da buƙatun nakasassu, da tauye musu damar da dokokin ƙasa suka basu a matsayinsu na ƴan ƙasa. A samar musu da tallafin lafiya da na ilimi, a inganta karatun ƴaƴansu, a koyar da su sana’o’in dogaro da kai, don hana su yawon bara, kuma a riƙa shigar da su cikin ayyukan raya ƙasa na gwamnati.

A yayin tattaunawar da aka yi, an tattauna game da buƙatar hukumomi da masu faɗa a ji su tallafawa masu buƙata ta musamman wajen shigar da su cikin ayyukan raya ƙasa, musamman abin da ya shafi samar musu da ayyukan yi da za su dogara da kansu ba tare da sun yi bara ko sun jingina da wani ba. Masu takardun shaidar karatu kuma a sama musu ayyukan yi da suka dace da lalurar da suke fama da ita. Ƙananan yara masu nakasa kuma a samar musu da tallafin karatu, da kayan koyon karatu da koyarwa ga malamai da ɗalibai, da suka dace da zamani. A kuma kula da batun lafiyarsu, musamman sun buƙaci a basu tallafi a bangaren kiwon lafiya ta hanyar inshora, yadda za su riƙa samun magunguna cikin sauƙi da rahusa.

Da wuya ka je wata ƙasa a duniya da ba za ka ga mabarata a titi ko a wasu kebantattun wurare suna bara ba, wasu don neman abin da za su ci a dalilin talauci da rashin gata, ko kuma don neman tallafin rayuwa saboda wata nakasa da ke tare da su. Duk kuwa da cewa a wasu ƙasashen gwamnatocin su na da wasu tsare tsare na tallafawa irin waɗannan mutane marasa gata da masu nakasa, da kuma kafa dokar hana bara a titi.

Hali
Ibrahim Bala
+ posts Bio
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    Matsalar Ƙwacen Waya: Ina Mafita?
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    Falalar Goman Farko Na Zul-hajji 
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    Bukatar Kulawa Da Marayu Da Masu Karamin Karfi
Hali
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Ta Yi Nasarar Dawo Da Rokar Da Ake Sarrafa Dawowarta A Tashin Farko Na Samfurin Long March-10B
  • Sulaiman
    CMG Ya Gabatar Da Shiri Na Musamman Mai Taken “Samun Nasara Dangane Da AI+” A Ketare
  • Sulaiman
    Zargin Da Wasu Sassa Ke Yiwa Kasar Sin Na Takure Sauran Kasashe Masu Tasowa Ba Shi da Tushe Ko Makama
  • Sulaiman
    Taron Kara Wa Juna Sani Na Duniya Ya Yi Nazari Kan Kwarewar Kasar Sin Wajen Rage Talauci

MASU ALAKA

Laifukan Intanet: Kotun Abuja Ta Karɓi Rahoton DSS, Ta Ba Da Belin Wani Ɗan Gwagwarmaya
Marurun Zuciya

Falalar Goman Farko Na Zul-hajji 

May 23, 2026
marayu
Marurun Zuciya

Bukatar Kulawa Da Marayu Da Masu Karamin Karfi

May 17, 2026
Abincin Da Ya Kamata Ku Ci Lokacin Al’ada
Marurun Zuciya

2027: Bukatar Zaben Shugabanni Na Gari

May 10, 2026
Next Post
Sojoji Sun Kashe Mayakan Boko Haram 6, Sun Kama Wasu A Borno

Sojoji Sun Ceto Mutane 22 A Jihar Sakkwato

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Nasarar Dawo Da Rokar Da Ake Sarrafa Dawowarta A Tashin Farko Na Samfurin Long March-10B

Sin Ta Yi Nasarar Dawo Da Rokar Da Ake Sarrafa Dawowarta A Tashin Farko Na Samfurin Long March-10B

July 10, 2026
CMG Ya Gabatar Da Shiri Na Musamman Mai Taken “Samun Nasara Dangane Da AI+” A Ketare

CMG Ya Gabatar Da Shiri Na Musamman Mai Taken “Samun Nasara Dangane Da AI+” A Ketare

July 10, 2026
Zargin Da Wasu Sassa Ke Yiwa Kasar Sin Na Takure Sauran Kasashe Masu Tasowa Ba Shi da Tushe Ko Makama

Zargin Da Wasu Sassa Ke Yiwa Kasar Sin Na Takure Sauran Kasashe Masu Tasowa Ba Shi da Tushe Ko Makama

July 10, 2026
2027: Tinubu Ya Sake Zaɓar Shettima A Matsayin Abokin Takararsa

2027: Tinubu Ya Sake Zaɓar Shettima A Matsayin Abokin Takararsa

July 10, 2026
Taron Kara Wa Juna Sani Na Duniya Ya Yi Nazari Kan Kwarewar Kasar Sin Wajen Rage Talauci

Taron Kara Wa Juna Sani Na Duniya Ya Yi Nazari Kan Kwarewar Kasar Sin Wajen Rage Talauci

July 10, 2026
An Ceto Dukkanin Ɗalibai Da Malaman Da Aka Sace A Jihar Oyo — Fadar Shugaban Ƙasa

An Ceto Dukkanin Ɗalibai Da Malaman Da Aka Sace A Jihar Oyo — Fadar Shugaban Ƙasa

July 10, 2026
Xi Ya Zanta Da Shugabar Namibia

Xi Ya Zanta Da Shugabar Namibia

July 10, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Ko Ka San Dalilin Da Ya Sa Chana Da Indiya Ba Sa Buga Kofin Duniya?

July 10, 2026
“Kashin Baya” Na Sin Ya Zama Abun Dogara Ga Kasashen Afirka

“Kashin Baya” Na Sin Ya Zama Abun Dogara Ga Kasashen Afirka

July 10, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Sana’ar Ɗinki: Yadda Telolin Zariya Suka Yi Fice A Sassan Afirka

July 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.