Mataimakin firaministan kasar Sin, Ding Xuexiang, ya bayyana a jiya Jumma’a cewa, kasar a shirye take ta yi aiki tare da Rasha domin zurfafa hadin gwiwar makamashi a dukkan fannoni, da kuma kiyaye dorewar ci gaban cinikayyar mai da iskar gas cikin dogon lokaci. Ding, wanda har ila yau mamba ne a zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS), ya yi wannan bayani ne a yayin da yake jagorancin taro na 23 na kwamitin hadin gwiwar makamashi na Sin da Rasha tare da mataimakin firaministan Rasha, Alexander Novak, a birnin Vladivostok na gabashin Rasha mai nisa.
Ding ya ce, ya kamata Sin da Rasha su hada hannu wajen inganta tsarin jagorancin makamashi na duniya, da kuma ba da gagarumar gudummawa ga kare samun wadatar makamashi da ci gaba mai dorewa na kasashen biyu da ma duniya baki daya.
A nasa bangaren, Novak ya bayyana cewa, Rasha a shirye take ta yi aiki tare da Sin domin inganta ayyukan hadin gwiwar da ake da su a kasa, da fadadawa da kuma tsara sabbin fagagen hadin gwiwa, kana da ba da sabbin gudummawa wajen zurfafa hadin gwiwa a aikace tsakanin Sin da Rasha. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














