Bunkasar tattalin arzikin kasa ya dogara ne kacokan ta hanyar tallafa wa kananan sanao’i da kasuwanci a kasa,ta haka dole ne gwamnati ta taimaka wa kasuwanci musamman ta bangaren samar da bankuna domin samar da jari ga ‘yan kasa don yin kananan sanao’i, don bankunan da muke da su a kasar nan a yanzu ba kananan ‘yan kasuwa suke taimakawa ba, suna taimakawa manyan ‘yan kasuwa ne kawai.
Saboda haka kai dan karamin dan kasuwa wadannan matakai guda bakwai da zan gaya ma indai ka karanta kuma ka yi aiki da su da shawarwari hakika na baka tabbacin samun ci gaba a lokaci kankani.
- …Dalla-dallar Yadda Aka Kashe Kudin Tallafin Mai
- Wani Abun Fashewa Ya Tarwatse A Wani Masallaci Ya Kashe Akalla Mutane 18 A Afganistan
Saboda haka ka ga kenan kai zuwa da ‘yan wasu shekaru masu zuwa ka san inda ka sa gaba.
 Kasashen da ake ganin sun ci gaba ta fannin tattalin arziki sun ci ne saboda yadda gwamnatocinsu suka jajirce wajen taimaka wa ‘yan kasuwa musamman kanana.
Mai karatu wadannan matakai da zan fada maka ba ni ne na kirkiro su ba, a’a! nima na samo su ne daga masana kasuwanci da kuma hulda da na yi da ‘yan kasuwa a kasashen da suka ci gaba a hirarrakin da na yi da su na fahimce su.
Dafatan idan an karanta a yi kokarin yin amfani da abin da aka karanta:
- Matakin Yin Kasuwanci. 2. Matakin Shugabanci. 3. Matakin Samun Kudi. 4. Matakin Saye Da Sayarwa. 5. Matakin Yarjejeniya. 6. Matakin Lokaci.
Matakin Yin Kasuwanci: Menene Makasudinku Na yin Kasuwanci?
Watakil babu wata cikakkaiyar amsa da za’a samu in ka yi wannan tambayar ga dan kasuwa, kamar ka ce da mutum ne don me yake neman kudi, watakil idan ba ka ci sa’a ba wanda ka yi wa wannan tambayar zai iya harararka in ma ya ji haushi da yawa ya kawo maka duka.
To! don Allah kar a ji haushi don na yi wannan tambaya.Tambayar da na yi ita ce ‘menene Makasudinku Na Yin Kasuwanc?I’ Da yawa daga al’umma da na Yi musu tambayar dalilin da ya sa suke kasuwanci sun amsa da cewa dalilin da ya sa suke kasuwanci shi ne don su ci riba kawai. Tabbas! Hakika duk wani abu da dan’Adam zai yi in babu amfani ko riba a cikinsa to wannan abin ya zama aikin banza.
Don ba wanda zai yarda ya yi wani aiki a kamfani ,ko a gwamnati, ko a karkashin wani mutum kyauta ba tare da ya samu wani lada ko amfani ba, ina zato ba zai yiwu ba.
Saboda haka ni a ganina babban dalilin yin duk wani kasuwanci shi ne don Samun Riba.
To! a tuna yanzu muna wani hali na matsin tattalin arziki in ka ci riba me kake yi da ribar? dalilin da ya sa na fara da tambayar dalilinka na yin kasuwanci.
Abin da nake so ka fahimta a nan shi ne ka shiga kasuwanci, bayan ka fara wane tanadi ka yi wa irin wannan lokacin na matsin tattalin arziki.
To dai tun ran gini tun ran zane, dole kafin ka fara kasuwanci ka yi wa kanka tsari.
Tsarin nan kuwa shi ne zai zamar maka wani madubi a koda yaushe. Misali kana samun Naira dubu daya kullum riba, me kake da ita, kashewa ko cefane mai kyau a gida, ko yin dinkuna akai-akai kamar sabon ango? Abin da nake so ka fahimta a nan shi ne ribar da ake samu a kasuwa ita ce take;
- Auna Yadda Kasuwancin Ka Yake Gudana
- Jawo Kasuwancin Ya Dore
- Samun Mai Saye Ako Da Yaushe.
Idan an kula cewa ashe ribar da kasuwanci take kawowa kusan ita take rike maka kasuwancin kacokan. Saboda haka sai ka duba ka gani a a cikin wadancan abubuwa guda uku suna yi maka tasiri a kasuwancinka.