Connect with us

TASKIRA

Matakan Kariya Daga Kamuwa Da Cutar Hanta (Hepatitis)

Published

on

Yadda kamuwa da cutar hanta ta zama ruwan dare sakamakon rashin daukar wasu matakai, jama’a ku karanta wannan jawabin sannan ku sanar da iyalai da ‘yan’uwa da masoyanku baki daya.

Ina ma a ce mutane za su yi hakuri su daina amfani da cokali, kofi, lemun kwalba, ruwan leda, kai duk inda dai yawun bakinka zai hadu da na wani inama a ce jama’a sun dauki matakin kiyayewa daga yau. Musamman a wajen mai shayi, idan mutum daya mai cutar hanta (hepatitis) ya sha shayi ya gama, za ku ga nan take mai shayin zai saka kofin a cikin ruwa ya girgije sannan ya yi amfani da kofin ya zuba wa wani, to ya zuba kwayoyin cutar hanta a cikin ruwan da ya girgije kofin wancan mai dauke da cutar hanta, kuma duk kofin da za a kara wankewa da wannan ruwan za a iya daukar wannan cuta ta hepatitis. Cutar hanta gata nan ta yi yawa a asibiti, ana ta mutuwa kuma mutane basu san ta inda suke samun ta ba, haka mai sayar da abinci a restaurant ko otel, haka mai dafa indomi, haka kofi na shan ruwa na kowa da kowa da a kan ajiye a wajen aiki ko masallatai na kasuwa, duk wani abun amfani wanda zai sa yawun bakin mutum zai hadu da na wani wallahi a kiyaye mu’amala dasu jama’a. Akwai sauran guraren kamuwa da cutar hanta kamar yin jima’i da wanda yake dauke da cutar, sannan sumbata (kiss) da saka tufafin da mai dauke da cutar ya saka kuma gumin jikinsa ya taba tufafin, a kiyaye jama’a!

Kuma da yawan mutane suna da cutar hanta amma basu san suna da ita ba, kuma basu san cewa suna yada ta a cikin al’umma ba, cutar hanta ba a saurin gane wanda yake dauke da ita a ido, sai idan ta yi nisa sosai a jikin mutum musamman wanda baya zuwa gwaji asibiti.

Yana da kyau duk bayan watanni 7 mutum ya dinga zuwa asibiti ana masa gwajin cutar hanta, ana iya maganin cutar hanta da zaran an ganota idan ba ta yi tsanani ta kai wani mataki ba, don haka zuwa gwaji a asibiti yana da matukar muhimmanci.

Don haka jama’a a yi hattara a kiyaye (hepatitis) cuta ce mai saurin kisa

Allah ka kare mu daga kamuwa da cututtuka masu saurin kisa, amin.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: