Uwar gidan gwamnan Jihar Bauchi Hajiya Aisha Bala Abdulkadir Muhammad ta bayyana cewa mata su na taka muhimmiyar rawa da ginshikin samar da shugabanci na gari, idan aka yi la’akari da hidimar tarbiyan al’umma.
Ta fadi hakan ne a wajen wata bita na kwana biyu 2 da ofishinta ya shirya wa matan Kwamishinoni da matan shugabbanin kananan hukomomi, tare da hadin gwiwan wata kungiya mai zaman kanta (Synistania Nigeria Limited) wanda ya gudana a dakin taro na gidan gwamnati.
Aisha Bala ta jaddada cewa matan shugabanni a matakai daban-daban su na da jan aiki ta wajen fadakarwa da nusar da al’umma musamman matasa kan shugabancin da ake masu, na gari ko akasin hakan.
Bugu da kari ta kira yi mata da su ci gaba da aiwatar da ayyukansu na jinkai da tausayawa, kana ta ce sun yi amfani da abubuwan da aka gaya masu a yayin bitar, in sun koma cikin al’ummar da suke shugabanta, hakan zai bai wa gwamnati samun nasara a gudanar da shugabancin mutane.
A nashi jawabin maraba, Kwamishinan kananan hukomomi da masarautun gargajiya Alhaji Abdurrazak Nuhu Zaki, ya yaba wa uwar gidan gwamnan kan irin ayyukkan ta na jinkai da kuma shirya irin wannan taro na karin ilimi.
Ya ce “Ki na cire wa mata kitse a wuta ta wajen wayar masu da kai, ina jan hankalin wadanda aka shirya taron domin su, da su yi amfani da damar da suka samu, kar su rika dinki ana warwarewa, ku rika koyi da irin ayyukan da Uwar gidan gwamnan ta ke yi, da kuma dogaro da kai, don tabbatar da shugabanci na gari.”
Har-ila-yau, shugaban hukumar kula da marayu da marasa galihu jihar Bauchi, Misis Hassana Arkila ta ce wannan bitar ya zo a daidai, kuma ta ce sai an hada karfi da karfe kafin a samu nasarar abun da gwamnati ta sa gaba akai, ta kara da cewa dole ne a sake sabon lale ta wajen tarbiyyar yara musamman a arewacin Nijeriya.
“Ba za mu zura ido yaranmu su na lalacewa ba, da shaye shaye da sara suka, da fyade da fashi da makami, dukkan mu muna da aiki tukuru a gabanmu kan tarbiyyar ‘ya’yan mu baki daya,” ta ce.
A wajen taron da ya daga cikin kasidar da Dakta Musa Adamu Wunti, na Jami’ar Jihar Bauchi dake Gadau, ya gabatar da takarda inda ta yi nuni da cewa, “Mata su na da kaso mai tsoka ta wajen gina al’umma, da kuma shugabanci na gari, bin doka da oda da zimman ayyukan da za su kawo ci gaba, da zaman lafiyan jama’a bakidaya.”