An yi kira ga matasa dasu tashi haikan wajen neman na kansu domin maganin zaman kashe wando tare da ganin sun dogara da kawunansu don huce takaici.
Wani matashi Bahaushe dake sana’ar zane ko Adon Riga, wato Design, Mallam Abdullahi Anas( Anas Designer) ne yayi wannan kira a yayin da yake hira da wakilin jaridar LEADERSHIP A YAU a ranan asabar data gabata a shagonsa dake garin Lokoja.
Anas Designer wanda dan asalin jihar Kano ne amma haifaffen Lokoja, har ila yau malamin makaranta ne dake koyarwa a makaranta mai zaman Kansa, wato Sunnah Academy dake Lokoja, yace rashin sana’a a tsakanin matasa yana haifar da mummunar illa ga rayuwarsu dama al’umma bakidaya.
Anas wanda yace Alhamdulillah, yanzu kam ya amfana matuka da sana’arsa na Designing,ya kuma janyo hankalin matasa yan uwansa,musamman yan Boko wadanda basu da sha’awar koyar sana’oin hannu dasu rungumi sana’a ba wai sai sun jira gwamnati ta basu aiki ba wanda bature ke kira (White Cola Job).
“A wannan sana’a ta na Design nayi na dauki dawaniyata ta karatu. Da sana’ar nayi aure da kuma ita nake daukar dawainiyar iyali har ma nake taimakawa iyaye da yan Uwa,” cewar Anas.
Anas ya ce, kama sana’ar hannu tamkar taimakawa gwamnati da kasa ne, inda yace” A yanzu haka ina biyan gwamnati haraji ko wace wata wadda zan bayyana da cewa gudunmawata ce ga ci gaban kasa.
Ya ce, a yanzu yana da yara kusan goma wadanda suke koyon sana’ar Zane da dinki a shagonsa wadanda a yanzu suna samun kwarewa a karkashinsa.
Sai dai kuma ya shawarci iyaye dasu rika tura yayansu don koyon sana’oin hannu. “Bai kamata a ce yara suna tashi ko girma ba tare da suna da sana’oin yi ba. A don haka ina kira ga iyaye dasu rika turo yaransu don koyon sana’a. Ko ba komai zasu taimakawa kansu da kansu ba sai sun dogara da iyayensu ba.
A dan abinda yara suka samu a sana’ar zasu ragewa iyayensu nauyi musamman ma kudin sayen sabulu,man shafawa, omon wanki da dai sauran kananan abubuwan amfani: inji Anas Designer.
Ya kuma yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da kuma masu hannu da shuni dasu taimakawa masu sana’oin hannu da jari ko kayan aiki domin bunkasa sana’oinsu.
Ya ce, babban kalubalen da su masu sana’oin hannu suke fustanta shine rashin samun isasshen hasken wutan lantarki wadda sai da ita zasu inganta sana’arsu.
Daga nan ya zarce jami’ar Bayero dake Kano inda ya samu takardan shaidar digiri a fannin tattalin arziki( Economics).
Anas Designer yayi hidimar bautar kasa( NYSC) a jihar Taraba dake arewa maso gabashin Najeriya.
A yanzu haka ya sake komawa karatun digirinsa ta biyu( Masters) a jami’ar Bayero dake birnin Kano. Mallam Abdullahi Anas Designer nada mata da ya guda.