Daga Muhammad Maitela
Idan an kalli matasan kasashen Afrika musamman Nijeriya akwai matukar damuwa tare da nuna halayyar ko-in-kula daga bangaren shugabanin da ke rike da madafun ikon kasar nan, wanda tsuffin hannu su ka mamaye; kusan tun bayan samun yancin kasar nan, an hana matasa rawar gaban hantsi. An jefa rayuwar su cikin yanayin ba tsuntsu babu tarko.
Abin bakin ciki ne ga kasa irin Nijeriya wadda ke ikirarin kasancewa giwar Afrika kana ta shida a samar da danyen man fetur da iskar gas a duniya amma ta kasa darajanta kimar matasanta wajen kirkiro ayyukan yi a lokacin da adadin yan kasar ke habaka.
Wanda a halin da ake ciki yanzu, hasashen masana ya nuna yawan yan Nijeriya ya doshi miliyan 200, inda kuma suka nuna adadin matasan kasar ya kai kaso 80 cikin dari, amma har yanzu gwamnati ba ta dena yiwa wannan ayarin matasa alkawuran muzuru ba.
Tun bayan da Nijeriya ta samu yanci s mulkin kai a 1960, bai fi cikin cokali na miskinan matasan da suka samu dama a madafun ikon siyasar tarayya, a jihohi shima ta hanyar mahaifa ko iyayen gida; bayan hakan babu wani abu na daban.
Uhmm, idan ka kalli masu ikirarin wakiltar matasan Nijeriya a gwamnatin tarayyar kasar nan sai ka tarar yan sama da shekaru 50 ne a duniya, al’amarin da zai kara bayar da tabbacin cewa matasan Nijeriya suna ruwa tsamo-tsamo.
Wannan kucuba-kucubar ba ta tsaya nan ba, idan ka binciki ma’aikatar ci gaban matasan da gwamnatin tarayya ta kirkiro abinda za ka rinka cin karo dashi shi ne tsuffin shafafu da mai ne suka mamaye ma’aikatar tare da wakiltar kawukan su da sunanan matasan Nijeriya wadanda aka bari kudan tsando suna kalaci a bakin su.
A hannu guda kuma, sau nawa ne gwamnatin Nijeriya take yi wa matasan kasar nan kwalele da man shanu a baki ta janye a kalaman zolayar cewa matasa sune shugabanin yau, ba na gobe ba?
Wanda mafi yawan matasan da ka ga suna shanawa da fantamawa a madafun ikon kasar nan a yau, idan ka bincika za ka tarar da cewa gado suka yi daga iyayensu da suka dana taragon mulkin kasar nan tun daga 1960 kuma a hakan suke har yau din nan da nake magana da ku.
Ko sun manta ne! A taswirar dokokin kasa wadanda suke kunshe a kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 da aka yi wa gyaran fuska, ya fayyace cewa duk dan Nijeriyar da ya zarta shekara 18 ya na da yancin yin zabe, haka kuma idan ya mallaki takardar shaidar gama makaranta nan ma yana da yancin tsayawa takarar kowane mukamin siyasa a kasa, yayin da wannan doka ta sahale cewa duk dan sama da shekara 18 zai iya rike kowane madafar iko a siyasance.
Wanda hakan ya nuna cewa akalla dan shekara 35 zuwa sama yana rukunin matasa wanda zai iya takarar matsayin kujerar shugaban kasa da sauran su. Sai dai kash, an saba lamba a wannan tafarki a Nijeriya kuma sai illa-nadiran.
Saboda yadda bangarorin gwamnatoci guda uku a kasar nan; tarayya, jiha da karamar hukuma, su ka gwasale gwiwar matasa tare da hana su rawar gaban hantsi hatta har a mukamin kula da ma’aikatar matasa, mai magana da yawun kaso 80 cikin dari na adadin yan Nijeriya wadanda sune matasa.
Kaicho matasa, an yi yaki daku an barku da kuturun bawa- kaso 95 cikin dari na adadin kuri’un da ake zura wa akwatunan kowane zabe a kasar nan matasa ne, gagarumar gudumawar su ce amma kuma suke kutal a kasar su ta haihuwa.
Al’amarin da kowace rana kara ta’azzara yake, sannan kuma alkawuran samar da gurabun aiki sai kara zama ga ta nan ga ta yake zama wanda a karshe samun aiki sai dan wane da wane- amma a wajen dan talaka sai dai ace “kurun-kus”!
Baya ga yadda duk mako sai kungiyar malaman jami’o’in kasar nan ta daka barkono mai yaji tare da bada shi ga hancin daliban kasar nan, ka ga kuwa ido da hawaye ina zancen karatu! Sannan a wannan halin da ake ciki na karbar kidan Janaral a sama, wane uba ne zai iya jure kai dansa makarantar kudi a Nijeriya? Sai ka ga yaronka ya fara jami’a ko kwalejin kimiyya da fasaha yana dan shekara 18 Ko 20 amma ya kammala ya na dan 30!
Wayyo Allah matasa, Aradu matasan Nijeriya cike suke da burin ci gaban kasar su face kawai tsuffin kaya ne suke sace musu taya, ta hanyar dakushe aniyarsu da karsashin da suke mafarkin ganin sun aiwatar dashi a zahiri.
Wannan ita ce Nijeriya kasar da dan sama da shekara 60 ke burin ci gaba da aiki a ma’aikatar gwamnati ko mai zaman kanta tare da yin ikirarin samartaka, ya yi babakere da rabon daruruwan matasa. Ko ka samu dattijo dan 70 yana aiki, ba tare da komawa gida ya kula da iyalan shi ba, ya mallaki gingima-gingiman gidaje a Abuja, Kaduna ko Kano.
Wannan wadane irin hadamammun mutane muke dasu a kasar nan, kun manta a baya bayan nan gwamnatin tarayya take kokarin tsawaita shekarun aikin malaman jami’a zuwa 70 maimakon 60? Alhali ga matasa nan sabbin jini dauke da kwalayen shaidar karatun digirin-digirgir a fanni daban-daban!