Matatar Dangote ta sanar da dakatar da tsarin ɗaukar mai kai tsaye daga matatar, inda ya ce wannan mataki zai fara aiki daga ranar Alhamis, 18 ga Satumba, 2025. Sanarwar ta bayyana cewa matakin zai hana masu siye marasa rajista shiga wajen saye kai tsaye tare da ƙarfafa amfani da tsarin kai wa kyau bayan saye (Free Delivery Scheme).
A cewar kamfanin, wannan sauyin wani gyaran aiki ne don inganta tsari, tare da tabbatar da cewa manyan cibiyoyin lafiya da muhimman wurare suna ci gaba da samun isasshen mai. Matatar Dangote ta kuma umarci a dakatar da dukkan biyan kuɗi da ya shafi ɗaukar mai kai tsaye, inda ta ce duk wani kuɗi da aka biya bayan wannan rana ba za a karɓa ba.
- Jigilar Mai: Me Ya Haddasa Rikicin Dangote Da Ƙungiyar NUPENG?
- Dangote Zai Gina Kamfanin Taki A Habasha Kan Dala Biliyan $2.5
Sai dai matakin ya zo ne a daidai lokacin da ake samun saɓani tsakanin matatar, da NUPENG da DAPPMAN. Yayin da NUPENG ke zargin kamfanin da ƙin yarda da ƙungiyantar da direbobinta, DAPPMAN na ganin tsarin kai wa kyauta zai tilasta ‘yan kasuwa su dogara da motocin Dangote a farashi mai tsada.
Amma a cewar kamfanin, tsarin ya ƙunshi dabarar kare rabon man fetur daga karkatarwa da kuma tabbatar da wadatar mai a kasuwa. Masana sun yi gargaɗin cewa dakatarwar za ta fi shafar ‘yan kasuwa masu zaman kansu da gidajen mai da ba su shiga tsarin kai wa kyauta ba, waɗanda suka dogara da ɗaukar mai kai tsaye daga matatar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp