Matatar Mai ta Dangote ta rage farashin fetur daga Naira 828 zuwa Naira 699 a lita.
Bayanai sun nuna cewar matatar man ta rage Naira 129.
- Me Ya Sa Ya Kamata Kasashen Afirka Su Bunkasa Tattalin Arziki Tare Da Kare Muhalli?
- Kamfanin CRCC Ya Kammala Shimfida Hanyar Jirgin Kasa A Gadar Layin Dogo Mafi Tsawo A Afrika Dake Algeria
Wani jami’in matatar ya ce sabon farashin ya fara aiki ne daga ranar 11 ga watan Disamba, 2025, wanda hakan ya zama karo na 20 da matatar ta ke rage farashin man fetur a bana.
Ragin na zuws ne bayan kwana kaɗan da shugaban kamfanin, Aliko Dangote, ya yi alƙawarin ci gaba da sanya sayar da fetur a farashi mai rahusa yayin da matatar ke ƙara samar tare da yin gogayya da man da ake shigowa da shi daga waje.
Bayan wannan sauyi, wasu manyan wuraren ajiya masu zaman kansu su ma sun rage farashinsu kaɗan, wanda ya nuna tasirin sabon farashin da Dangote ta fitar.














