Matsalar Arsenal Babba Ce –Aubameyang

Dan wasan gaba na Arsenal kuma kaftin din kungiyar, Pieere Emerick Aubameyang, ya tabbatar da cewa matsalolin kungiyar sun wuce tunanin mutane saboda haka akwai bukatar a zauna a nemo mafita kafin lokaci ya kure.

Dan wasan wanda bai buga wasannin kungiyar ba a baya sakamakon rashin lafiyar mahaifiyarsa ya bayyana cewa abune mai wahala kungiyar ta samu damar zuwa inda take bukata a halin yanzu sai dai ya ce komai zai iya faruwa duk da haka.

Minti biyu kacal da take wasa Aston Billa ta cilla wa Arsenal kwallo a zare a wasan mako na 23 na Premier League kuma tsohon mai tsaron ragar Arsenal din ne, Emiliano Martinez, ya fara bugo awallon wadda Bertrand Traore ya tsinta bayan Soares ya yi kuskure, inda shi kuma Ollie Watkins ya cilla ta zaren Mat Ryan.

“Tabbas abubuwa basa tafiya yadda yakamata kuma akwai bukatar mu tashi tsaye domin nemo bakin zaren kafin lokaci ya kure domin yadda ake tafiya a halin yanzu bana ganin zamu iya cika burinmu na muka sanya a bana” in ji dan wasa Aubameyang, dan asalin kasar Gabon

Wannan ne karon farko da Aston Villa ta yi nasara kan Arsenal a wasa biyu a jere cikin shekara 28 saboda ranar 8 ga watan Nuwamban 2020 Aston Villa ta casa Arsenal da 0-3 har gida a gasar Premier.

Tsohon mai tsaron ragar na Arsenal Martinez, ya hana Granit Xhaka farke kwallon daya tilo a lokacin da ya buga masa wani bugun tazara sannan da wannan sakamako, Aston Billa ta zama ta takwas a teburi, yayin da Arsenal ke mataki na 10.

Exit mobile version