Saboda kawo karshen matsalolin tsaro da ke shirin zama gagarabadau ga masu ruwa da wannan batu, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya yi zama na sa’o’i da dama da kungiyoyin addinin musulunci da suka haxa da kungiyar Fitiyanul Islam da kuma kungiyar Izalatul Bidi’a Wa’ikamatul Sunna reshen jihar Kaduna, domin gano bakin wannan matsala ta tsaro.
Tun farko a jawabinsa, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Bamalli, ya bayyana cewar ya kira wannan taro ne da kansa, domin lurar da wannan batu na tsaro da ake jin labara dagga nesa, amma a halin yanzu, a cewar Mai martaba sarki shi ya say a ga mafitar matsalar shi ne zama tare da xaukacin malamai da kuma hakimai ma su gari, domin ganin an sami yi wa wannan matsala ta tsaro rajamu.
Mai Martaba Sarkin Zazzau ya nunar da cewar, a halin da ake ciki a halin yanzu, babbar hanyar da za a runnguma domin kawo karshen wannan matsala ta kamfar tsaro shi ne rungumar addu’o’i dare da kuma rana, domin ta haka ne kawai, kamar yadda ya ce wannan matsala ta tsaro za ta tarihi musamman a jihohin da wannan matsala ta yi kamari.
A dalilin haka ne, a cewar Mai martaba Sarkin Zazzau, ya fahimci rungumar addu’o’i da kuma gyara tafiya, su na kan gaba na matakan da ya ce, idan an bi su wannan matsala da ta addabi al’ummomi daban-daban, za ta iya zama tarihi, amma sai kowa, kamar yadda ya ce ya yadda addu’ar ce mafita, ba wasu hanyoyi na daban ba.
Yayin da kuma Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli ke tsokaci kan kisar gillar da a ka yi wa wasu al’ummomi har su 43 a jihar Barno, ya nuna matukar kaxuwarsa da jin wannan lbari mara daxin ji, a nan sai ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan waxanda suka rasa rayukansu da kuma gwamnatin jihar Barno, na wabbab rashin al’umma da aka yi, ya na addu’ar kare faruwar mai kama da wannan matsala a nan gaba, ba a jihar Barno ba, ya ce a Nijeriya kafatan.
A dai jawabinsa ga malamai da kuma hakimansa day a gayyata, mai martaba Sarkin Zazzau ya yi kira garesu das u kara tashi tsaye na ganin sun bi duk hanyoyin da suka dace domin kawo karshen wannan matsala ta kamfar tsaro da ta addabi duk wani da ke arewacin Nijeriya..
A karshen jawbinsa ya tabbatar da cewar, zai yi koyi da wanda ya gada marigayi Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, na yadda ya rungumi malamai da shugabannin addini da hannu biyu, da kuma karban shawawrwarin da suke bayar wag a majalisar masarautar Zazzau, a kan matsalolin da suka shafi harkar tsaron lafiyar al’umma da kuma dukiyoyinsu dare da kuma rana.
Jawabansu daban – daban a lokacin taron, Shugabannin kungiyar Fitiyanul Islam dad a kuma na Izala dukkansu sun bayyana matukar damuwarsu na yadda matsalolin tsaro suka zama tamkar wasan yara, na yadda ake hallaka al’umma dare da kuma rana da kuma yadda ake farautar al’umma a matsayin garkuwa da su, da suka ce, in an rungumi addu’o’I, wannan matsala ta tsaro za ta kau, da yaddar mai – kowa – mai – komi.
Sai dai kuma wasu daga cikin mahalarta wannan taron, sun nuna matukar damuwarsu na yadda gwamnatoci ba su damu da malaman addini ba, ‘’ba ma sa karban shawarwarinsu, a kan duk wasu al’amurra da suka shafi kasa ko kuma jiha ya zuwa kananan hukumomi, wannan matakai da wasu gwamnatoci suka xauka, na kan gaba na yadda matsalolin tsaro a kullun sai kara kamari ta ke yi, mai mamakon matsalolin su fara raguwa.
Har ila yau, wasu malamaiu da suka halarci wannan muhimmin taro da mai martaba Sarkin Zazzau ya kira sun yi kira ga mai martaba sarki da ya shiga cikin ma su bayyana wa shugabannin da matsalolin tsaro ke hannunsu gaskiyar lamurra, ta haka, a cewarsu, sai ma su ruwa da tsaki a batun tsaron su kara ilmantuwa da laujen da aka cusa lauje a cikin naxi da ake yi da nufin dagula wasu al’umma bisa tsare-tsaren da aka sa wa gaba, domin ci gaba da shuka matsaloli a jihohin arewacin Nijeriya.
Mahalarta taron sun kuma shawarci mai martaba sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli, da ya ci gaba da karfafan hakimamai da su ke garuruwan da aka ce su kula da su da kuma ma su Unguwanni da suke tare da al’umma a kasa, in an yi haka, a cewar mahalarta taron, matsalolin tsaron za iya gano su a cikin gaggawa.