Matsalar Tsaro: Zagami Ya Yi Alkawarin Ba Sojoji Karin Goyan Baya

Daga Awwal Jibril Yankara

Magajin garin ‘Yankara, Alhaji Abba Adàmu Zagami na 2 wanda ya samun Wakincin kanin Sa Alhaji Rabe Adàmu Zagami, ya yi alkawarin bayar da cikaken goyan baya ga rundunar Sojojin Nijeriya a yakin da ta ke yi da ‘Yan Ta’adda da kuma masu taimaka wa ‘yan ta’adda da bayanan sirri na garin na ‘Yankara a dukkanin fadin Masarautar ta Zagami.

Zagami ya yi Wannan alkawarin ne yayin gudanar da wani taron masu ruwa da tsaki kan al’marin garin ‘Yankara, tare da hadin guywar shugaban Sojojin da ke kula da shiyar ‘Yankara da ke karamar Hukumar Faskari jihar Katsina, Manjo Janar MM Ibrahim a ranar Asabar 4 Ga Shawwal, 1442 (16 Ga Mayu, 2022)
Da yake Jawabi Manjo Janar MM Ibrahim ya yi kira ga mutanen garin na’Yankara da su kula so sai da mihimmancin haddin kai, taimakon, da kuma hade bangarorin ‘yan bangar garin da suke da gida biyu.
Dole ne a mihimmatar da wannan, ya ce rashin hadin kai ba karamar Illa ba ce.
Sha’anin tsaro na kowa da kowa ne, shima shugaban kwamitin tsaro na garin na ‘Yankara Alh. Gambo Sharu, ya gode ma mahalarta taro, da suka amsa goran gaiyatar kuma ya gode ma Manjo Janar MM Ibrahim bisa irin hangen nesan sa da kuma kishin garin na ‘Yankara ya hada taron, haka zalika DCP Alhaji Ibrahim Husaini, ya yi kira ga mutanen garin na ‘Yankara da gaskiya tsakani da Allah su rungumi shawarwarin da shugaban sojojin Manjo Janar MM Ibrahim ya bayar. Muhimman mutane ne ‘yan garin da wadanda ke wake aka gayyato da halartar taron da Lalubo hanyar magance matsalar tsaro da ta adabi Garin na Yankara tsawan Shekara guda daya cib.

 

Exit mobile version