A Matsayinsa Na Ɗan Kasuwa: Ko Sabon Kwamishinan Ciniki Da Masana’antu Na Kano Zai Kai Kano Ga Gaci?

Daga Mustapha Ibrahim, Kano

An ƙarƙiro jihar Kano a shekarar 1967 wanda gwamn na farko shi ne, marigayi kwamishinan ‘yan sanda Alhaji Audu Baƙo, gwamnan Kano na soja na farko kuma wanda ya naɗa kwamishinoni a wannan lokacin inda a cikin su akwai kwamishina wanda a tarihin kasuwancin Afirka sai an sa sunan mahaifinsa, wanda shi ne, ya fara riƙe wannan ofis na kwamishinan ciniki da masana’antu na Jihar kano wajen 1967 watau, ina nufin ɗan gidan Dattijon ɗan kasuwa Alhaji Alhassan Ɗantata kuma kwamishinan da nake magana da ya fara kwamishina a wannan ma’aikata shi ne, Alhaji Aminu Alhassan Ɗantata wannan duniya ta shaida ɗan kasuwa ne a ko’ina kuwa domin ya zama ɗangado a kasuwanci a cibiyar kasuwanci ta Afirka.

To shi dai wannan ofis na kwamishinan ciniki da masana’antu na Kano bai sake samun wani wanda ‘yan kasuwa suka yarda cewa shi ma ɗan kasuwa ne ba sai dai wannan lokaci da gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya zaɓo Alhaji Ahmad Rabi’u, wanda ya kafa tarihi a cibiyara ciniki da masana’antu ma’adanai da aikin gona ta Jihar kano.

Honarabul Ahmad Rabi’u tsohon ma’aikaci  a fitattun kamfanoni da ake alfahari da su a Nijeriya da Afirika koma duniya baki ɗaya.

A ɓangaren kasuwanci na ƙashin kansa kuwa shi ne mamallaki kuma shugaban kamfanin sauke kayayyaki na jiragen sama dana ƙasa da kuma na motoci a doran ƙasa wato gaɓar sauke kaya a doran ƙasa wanda ake kiran kamfanin da suna Dala Dry Inland Port haka kuma yana da kamfanin hada-hadar saye da sayarwa na waya kuma shugaban kamfanin tuntuɓa a kan hakar Haraji da makamantansu da sauransu kuma ya kasance mai yawan tafiye-tafiye a kan harkar kasuwanci a ƙasashen Afirka da Turai da Cana da Asiya da sauransu kuma bincike da bayanai da wakilinmu ya tattara a kan sabon kwamishinan ciniki da masana’antu a tsakanin ‘ya kasuwa ya nuna cewa kashi 99 cikin 100 na’ yan kasuwa sun yarda cewa, nasu ya samu wato ɗan kasuwa ya zama kwamishina,a bayan shekaru sama da 40 ba su samu wannan damar ba sai yanzu.

Zuwan sabon kwamishina Alhaji Ahmad Rabi’u ya zo  daidai lokacin da kasuwanci da ‘yan kasuwa suke fuskantar babban ƙalubale da siyasar ‘yan kasuwa ta tsaya cak, musamman idan aka yi lakari da yadda zaɓen ƙungiyar kasuwar kantin kwari ya ƙi yiwuwa saboda wasu dalilai masu yawa da gwamnati ta bayyana haka kuma ga ƙorafi na tashin Dala da rashin ciniki a kasuwanni ga kuma ƙorafi na cewa gwamnati sama da ta ƙasa wato ta tarayya da ta Jiha ba ta dama wa da su da dai sauran matsaloli wanda wasu ke ganin cewa sum a ‘yan kasuwa da kansu suka jawo wa kansu musamman in aka yi la’akari da yadda wasu suke faɗa na rashin haɗin kai da san kai da hassada da rashin riƙe amana, da taurin bashi da dai sauransu da ke mayar da kasuwanci da ‘yan kasuwa baya, ganin irin waɗannan matsaloli marasa iyaka ya sa jama’a da dama  ke tambaya naɗa Alhaji Ahmad Rabi’u kwamishinan ciniki da masana’antu ko kwalliya za ta biya kuɗin sabulu?

In dai ana zancen inganci na shugabanci da ta fi d al’umma Alhaji Ahmad Rabi’u KACCIMA ya na da shi domin duk wanda yayi mu’amala da shi zai san haka ta hanyar tawaru’un san a ɗaukar abin duniya ba komai ba ne da kuma rashin girman kai da kuma jawo na ƙasa jikin sa ga kuma biyan haƙƙi ga ma’aikansa akan lokaci a duk inda ya samu kansa a lamba ɗaya wani abu da ya isa shaida kuma kowa ya sani akan Honarabil Ahmad Rabi’u shi ne ya na daga cikin mutane kaɗan da na sani ba ka iya gane waye mai gida waye Direba waye maigida in dai za ka la’akari da sa sutura ne to da wahala ka gane Direban Alhaji Ahmad Rabi’u domin kuwa za ka ga Direbansa fes-fes kuma kasan wannan ba ta yiyuwa sai an samu mai gida mai tawaru’u da sanin haƙƙi ɗan Adam da darajar sa. ko wannan ce ta sa ma’aikatan sa ke masa fatan alheri da kiran sa ɗan Aljanna? Kuma su ke musanyen suna, da yan Jarida, inda suke kiransa da Partner on Progress shi ma ya kiran yan jarida da wannan suna na Partner on Progress? Ko ba komai dai mutum ne mai kyakyawan mu’amala da karrama ɗan Adam.

Duk da wannan bayanai da suka gabata wakilin mu ya samu sabon kwamishina ciniki da masana’antu Honarabil Ahmad Rabi’u inda wakilin Jaridar Leadership a yau Lahadi ya nemi ya kafa tarihi na cewa shi ne Ɗan Jarida na farko da ya nemi yin hira da sabon kwamishin cewa ya ba shi damar kafa tarihin cewa Leadership a yau ita ce ta fara hira da shi a Tarihi bayan da shi da aka yi kuma ta same shi ta yi hira da shi a aikinsa na farko a tarihi da ya fara yi bayan rantsar da shi a wannan muƙami a wannan rana da aka gabatar da zaben sabon shugaban KACCIMA da aka yi a wannan rana ta 16/10/2017.

Ga yadda ya bayyana wa wakilin mu matsayin sa a wannan kujera inda ya ce ba shakka kowa ya san kano cibiya ce ta kasuwanci kuma jalla babbar Hausa yaro ko da me ka zo an fi ka kuma Jiha da Allah ya Albarkaceta da hanyoyi waɗanda suka haɗa ƙasashe daban daban da ake harkar kasuwanci kuma Jiha ce da ta ke da tarihin kasuwanci da yan kasuwa haka kuma ya bayyana cewa wannan abu zai yi iya ƙoƙarinsa ya ga kasuwanci, da `yan kasuwa sun cigaba sosai a wannan zamani na sa bisa goyan bayan gwamnan Jihar kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da su yan kasuwan da sauran al’ummar Jihar Kano.

Haka kuma ya bayyana cewa ba shakka yan kasuwa na da matsaloli da ƙalubale mai yawa wanda ba za’a ce ga iya ƙalubalen da suke fuskanta, amma a matsayin sa na ɗan kasuwa zai yi iya ƙoƙarin ya ga yan kasuwa sun haɗa kai domin a ciyar da kasuwanci gaba dai dai da zamani, ya ce kuma wasu matsalolin na yan kasuwa ba aikin gwamnati bane aiki ne da su yan kasuwan za su yi da kansu sai ga an samu nasara amma sai ka ga an tsaya jiran gwamnati wanda kuma ba haka abun yake ba.

Dan gani da maganar kuwa da ake cewa ba a yi da ‘yan kasuwa ya ce wannan akwai gyara cikin wannan maganar domin duk mutumin da yake da muhimmaci dole a yi da shi ko ana so ko ba a so yau matsayin ‘yan kasuwa a duniya ya wuce a ce ba a yi da su domin su ne ƙashin bayan tattalin arziƙin duniya haka kuma abin yake a Nijeriya haka abin yake a Jihar Kano don haka ne ma ya ce zai iya ƙoƙarin sa na ya ga an bunƙasa ƙananan da manyan masana’antu, kuma za a yi iya ƙoƙari na gani cewa an wayar wa da ‘yan kasuwa kai na su fahimci kasuwancin zamani kuma a wannan zamani.

Ko dai mene ne ba shakka ‘yan kasuwa sun yi murna kuma sun gansu da naɗa Honarabil Alhaji Ahma,d Rabi’u kwamishinan ciki da masana’antu na Jihar Kano

cikin kwamishinoni shida da Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa kuma ya rantsar da su a wannan lokaci goge wa da sanin makama ta kwamishina.

Exit mobile version