Masana harkokin kudi da na tattalin arziki sun bayyana wa Shugaban kasa Bola Tinubu cewa karuwar kaso 3.19 na kudin shigar Nijeriya a zango na biyu na 2024 ya gaza fito da hakikanin halin da ‘yan Nijeriya ke ciki.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar kiddiga ta Nijeriya (NBS) ta sanar a ranar Litinin cewa kudin shigan Nijeriya ya karu da kaso 3.19 cikin 100 a zango na biyu na shekarar 2024, wanda ya dara da kaso 2.98 cikin 100 a zangon farko.
- Kamfanin Abinci Na BUA Ya Samu Ribar Naira Biliyan 130 A Wata Shida Na 2024
- Yawan Ribar Da Masana’Antu Masu Matsakaicin Kudin Shiga Suka Samu Ya Karu Da Kashi 3.6% A Farkon Watanni 7 Na Bana
A cewar rahoton NBS, bangaren kamfanoni da ayyuka sun ba da gagarumin gudunmawa wajen ci gaban kudin shigan a zango na biyun.
Bangaren ayyukan yau da kullum ya ba da kaso 58.76 na kudaden shiga, inda bangarorin da ba na mai ba suka kawo kaso 94.30, yayin da kuma bangaren mai ya kawo kaso 5.70 a zango na biyun.
Duk da wannan ci gaban da kudin shigan kasan ya samu, masana tattalin arziki sun yi tambayar mene ne ya sanya har yanzu talakawan Nijeriya ba su ga tasirin karin da aka samu ba.
Bugu da kari, farashin kayayyaki na nan a kan tsadarsu duk da tsare-tsaren da Tinubu ya bijiro da su.
Wani masani kan tattalin arziki, Farfesa Segun Ajibola, tsohon shugaban kungiyar kwararru a bangaren banki, ya ce, ci gaban bai taba rayuwar talakawa ba ko kawo sauyi daga halin da suke ciki.
Ya nemi gwamnati da ta bullo da hanyoyin da suka dace da talaka zai samu sauki da ganin tasirin ci gaban da ake samu na kai tsaye.
A cewarsa, ci gaban ya kamata ne ya shiga cikin abubuwan da suke na bukatun jama’a na farko-farko wato irin kayan abinci kafin a je ga manyan bangarori na ayyukan yau da gobe, wanda in aka samu hakan talaka zai shaida.
Shi ma masanin hada-hadar kudade, Gbolade Idakolo, ya ce, karuwar kudin shigan bai janyo sauyi kan lamarin tattalin arziki daga tushe a wajen talaka ba.
Don haka ne ya ce a yi la’akari da hakikanin halin da ake ciki ta yadda za a nemi tunkarar abubuwan da suke akwai domin samun sauyi mai ma’ana.