Bayan tsawon watanni biyu, kasashen Nijar da Amurka sun cimma daidaito game da batun janyewar sojojin kasar Amurka daga Nijar din, inda a ranar 19 ga watan nan, ma’aikatun tsaro na kasashen biyu suka fitar da hadaddiyar sanarwar cewa, Amurka za ta janye sojojinta daga Nijar kafin ranar 15 ga watan Satumba mai zuwa.
Idan ba a manta ba, ba da jimawa ba, wato a karshen bara, Faransa ta janye sojojinta daga Nijar bisa bukatar Nijar din.
- Xi Ya Taya Murnar Bude Tattaunawar Manyan Jami’An Sin Da Amurka a Fannin Yawon Shakatawa Karo Na 14
- Ba Wanda Zai Iya Keta Ka’Idar “Kasar Sin Daya Tak a Duniya”
To, ko me ya sa Nijar ke ta korar sojojin kasashen yamma daga kasar? Lallai za mu iya gano amsar tambayar daga tattaunawar da firaministan kasar Ali Mahamane Lamine Zeine ya yi tare da wakilin jaridar Washington Post a kwanan baya.
A watan Maris na bana, wata tawagar wakilan kasar Amurka karkashin jagorancin Molly Phee, mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amurka, ta ziyarci jamhuriyar Nijar, kuma tawagar ba ta jima ba da barin kasar, sai Nijar ta sanar da yin watsi da yarjejeniyar hadin gwiwar ayyukan soja da ta kulla da Amurka. A game da haka, Mr. Lamine Zeine ya ce, a yayin ziyararta, Madam Molly Phee ta yi wa gwamnatin Nijar barazana da cewa, idan Nijar ta daddale yarjejeniyar sayar da Uranium ga Iran, to, za a kakaba mata takunkumi. Mr. Lamine Zeine ya kara da cewa, “kun zo nan kasarmu kun yi mana barazana, abu ne da ba za mu amince da shi ba, kuma kun zo nan kun bayyana mana da wa ya kamata mu yi hulda, shi ma abu ne da ba za mu amince da shi ba……a lokacin da ‘yan ta’adda suka zo suna kashe jama’armu tare da kone garuruwanmu, su Amurkawa suna nan a kasarmu, amma kallo kawai suke yi. Sun zo sun bar ‘yan ta’adda suna kai mana hare-hare yadda suka ga dama, wannan ba abu ne na sada zumunta ba. Mu muka ga yadda Amurka ta yi kokarin kare kawayenta irinsu Ukraine da Isra’ila”.
Alal hakika, akasarin al’ummun kasar Nijar na ganin cewa, neman tabbatar da iko a kan ma’adinan Uranium da Allah ya albarkaci Nijar da shi, na daga cikin dalilan da suka sa kasashen Amurka, da Faransa suka girke sojojinsu a kasar, hakan abun yake ma a sauran wasu kasashen Afirka wadanda suke da arzikin mai da sauran ma’adinai.
A cikin shekaru 10 da suka wuce, Amurka, da Faransa sun fake da sunan yakar ta’addanci, wajen girke sojojinsu a yankin Sahel na nahiyar Afirka, sai dai hakan bai haifar da da mai ido ba, ganin yadda kasashen suka yi ta kara fama da talauci da rikici. Abin da ya sa karin al’ummar kasashen Afirka suka gane cewa, don neman tsoma baki cikin harkokin gidansu, da kwace albarkatunsu ne kasashen yamma suke girke sojojinsu, don haka ma suka yi ta nuna kin jinin sojojin. Ba ma kawai a Nijar ba, Faransa ta janye sojojinta daga kasashen Mali da Burkina Faso a cikin ‘yan shekarun baya bayan nan. A watan Afrilun bana, Chadi ita ma ta bukaci Amurka ta janye sojojinta daga kasar.
A sa’i daya kuma, kasancewar kasashen yamma sun taba yin mulkin mallaka a galibin kasashen Afirka, kasashen Afirka na ganin kasashen yamma na yunkurin ci gaba da samun iko a nahiyar da ke da arzikin albarkatu iri iri, duba da cewa barazana ce a maimakon kwanciyar hankali, sojojin da kasashen yamma suka tura suka haifar ga nahiyar, kuma tarnaki a maimakon ci gaba ne gudummawarsu ta samar. Yadda aka kori sojojin Amurka da na Faransa ma ya bayyana yadda kasashen Afirka suke kyamar “sabon nau’in mulkin mallaka” da kasashen yamma suke neman kafawa, da ma bukatunsu na neman samun ‘yancin kansu, da hadin gwiwar cin moriyar juna.
Ya kamata kasashen yamma su gane cewa, lokacin da suka yi wa kasashen Afirka duk abin da suka ga dama tuni ya wuce. Dole ne a bi ka’idar martaba juna, da zaman daidaito, da cin moriyar juna wajen aiwatar da hadin gwiwa da kasashen Afirka, sabo da ta haka ne za a kai ga tabbatar da ci gaba, da tsaro na bai daya. (Mai Zane:Mustapha Bulama)