Da yake ga dukkanin alamu har yanzu kalaman da Ministar Mata, Hajiya Jummai Alhassan ta yi a kan goyon bayanta ga ubangidanta na siyasa, Alhaji Atiku Abubakar a zaben 2019 na cigaba da tayar da kura, Ministan Wasanni da Matasa, Barista Solomon Dalong ya bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi garambawul a majalisar ministocinsa.
A cewar Minista Dalong yin garambawul din ya zama wajibi saboda la’akari da wadanda suke neman cinna wa gwamnatin wuta kowa ya kone kurmus a siyasa.
Ya bayyana haka ne a wata zantawa da ya yi da Sashen Hausa na Muryar Amurka a tsakiyar makon nan.
Ya ce, “Ba zai yiwu muna saida man fetur wani ya ce zai toya kosai a waje kusa da mu ba. Maganar da ta yi ta sa kowane Dan Nijeriya zai kalli mu ministocin Buhari a matsayin maciya amana. Da ta ajiye aikin nan sai ta yi abin da take so”.
Ba wannan ne karon farko da wasu ke kiraye-kirayen shugaban kasan ya yi garambawul a majalisar zartaswarsa ba, domin ko a ‘yan makwannin da suka gabata, Kungiyar Kwadago a Kasa (NLC) ta nemi hakan har ma ta ce idan aka wuce wannan lokacin ba a yi ba, lokaci zai kure.